UBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK 43

Shiru Akira tayi tana sauke Kai Suma tuni kowa ya sauke Kai 

Akira ta Dan dago cikin shakkun tsoma Baki cikin al’amarin sbd babban gargadi daga mr Omar na kada Wanda yafadi Wanda aka kashe din wa NURU Koda Wasa.

Sake maimaita tambayarta tayi wannan karon da ‘dan daga murya 

Akira ta sake sauke Kai ahankali cikin tausasa harshe tace”

Kisa akai a sassan maleek a Daren shekaran jiya, Matar MALEEK ta farko itace ake zargin tayi kisan sai jekadi da aka tafi da ita itama sbd ansameta a gurin 

da abin yafaru…….

Kai tsaye NURU tace”

Waye aka kashen???

Tsit sukayi Akira na sake sauke kanta

Qasa cikin nutsuwa tace”

Babu Wanda yasani tukuna.

Shiru sukayi dukkaninsu daga NURUn har afia sbd tashin hankalin da mamakin al’amarin.

Zamewa afia tayi ta sulale kan kujera ta zauna tana rasa tunanin Yi 

NURU ta zauna kusada ita tareda kallonta cikin tausayawa da sanyin yanayi tace”

Kaddarace wannan ki dauka daga ubangijine Kuma Inshallah zata samu kanta idan har batada hannu aciki

Sbd dad dinku bazai taba barinta cikin wannan halin ba komai zaizo ya warware Inshallah.

Kasa dagowa afia tayi tana sauraren abinda NURU take fada Mata Wanda hankalinta baya Kai tayi zurfi cikin tunani ta dago ahankali ta kalli NURU da jajayen 

idanuwanta tace”

Idan ta tabba cewan itace ta aika wane hukuncine zai hau kanta a shari’ancen Court??

Shiru NURU tayi tana kallonta cikin tsananin tausayawa kafin ta Dan dauke Kai cikin sanyi tace”

A shari’ancen musulunci shine Wanda ya kashe da gangan a kashesa,

A shari’ancen kotu ma idan dukkanin shedu sun bayyanarda yayi kisan da gangan ne ba bisaga qaddara ko dalilin Kare Kai ba ko dalilin ceton Rai to tabbas 

kisa ce ta Kai tsaye zata hau kansa….

Saurin dafa afian tayi ganin tana neman fita hayyacinta cikin sauri tace”

Dukkanin wannan kadaki yanke ko daya sbd bakisan akan me kisar ta afkuba kika tayine Dan kariyar Kai ko bisaga kaddara kadaki cire Rai daga sauqin ubangiji 

kiyi kokari kiriqe jarumtar fuskantar komai Inshallah ba hakan bane Ina Mata fata.

Miqewa NURUn tayi Jin tahowar farhat dake kiranta tun daga cikin bedroom ta juya ta kalli kofar dakin kafin ta dawo da kallonta kan Afia a natse tace”

Ina zuwa Bari nadubo ta.

Wucewa tayi zuwa dakin dake gefen nata Wanda aka tsarashi da komai na yara domin farhat din tana shiga ta qaqalo murmushi tana kallon kallon farhat din data 

shirya cikin riga da wandon asalin yadin qasar na sarauta me kyau ta qaraso gurinta tana cewa”

Heyy sweetie you look more pretty.

Cikin Jin Dadi ta qaraso gurin NURUn tana fadawa jikinta suka juyo zuwa palo tana cewa”

Aunt jiya Ina Kika kwana Kika barni Ni kadai?

Siririn Murmushi NURU tayi tana kawar da zancen tareda Dan dagowa ta kalli inda afia data bari Palon tana fatar Bata jiyo zancen da farhat din tafada ba ta 

kamo hannun farhat din suka nufi gefen da dining yake ta miqawa Akira hannunta tana cewa”

Kije da ita taci abinci Ina zuwa.

Komawa bedroom dinta tayi tayi wanka cikin sauri ta shirya cikin doguwar royal gown ash ta fito Akira dake jiran fitowarta ta gyara tsayuwa suka nufi sashen 

Anneti Dan sai yanzu tunanin zuwa Kai Mata gaisuwa ya shigeta musamman tasan tanacan cikin damuwar al’amarin itama tabar afia zaune agurin tana saqa da 

warwarar yanda zata tarbi al’amarin wa mahaifiyarta sbd ko kowa ya yadda da ita ta aikata hakan bazata taba yadda da mum dinta zata aikata hakan ba.

Koda aka sanarwa Anneti qarasowar NURU gurinta sai farin ciki ya shigeta taji ta Dan samu nutsuwa da saukin abindayake cin ranta ta fito daidai shigowan 

NURUn data qaraso har gabanta ta durqusa har qasa ta gaisheta cikin girmamawa

Da farin ciki Anneti ta dagota tareda nuna Mata gurin zama tana amsawa cikin kulawa tace”

NURU ya kike?

Kina lafiya dai ko?

Alhmdlh”tafada cikin nutsuwa tana Dan dagowa bayan sun gama gausawar tace”

Ashe abin daya faru kenan¿Allah ya kawo mafitar wannan al’amari tareda tsare gaba.

Ajiyar zuciya Anneti tasake tana gyara zama ahankali cikin bayyanarda ‘yar damuwarta tace”

Allah ne kawai masanin wannan al’amarin Amma dai koma Yaya yake

Allah ya fitar da kowa yakawo mafita

Musamman shi maleek da abin yafaru a qarqashinsa Wanda yasa Yan jaridu keta fidda labarai marasa Dadi akai

 bana fatan hakan yazamo matsala agaresa, ki kula dashi sosai kibashi kulawa Dan Yana cikin tsananin damuwa na tabbata.

Shiru NURU tayi dukkanin jikinta nayin sanyi da wannan sabon bayanin data samu.

Boyayyan numfashi ta sauke tanajin tsananin buqatar son ganinsa Dan Bata lurada cewa halinda yake ciki ba kenan tun jiyan da bazata baro gurinsa ba gashi 

yanzu batada ikon maida kanta batareda ya nemi ganintaba.

Miqewa tayi jiki Sanyaye ta fito Takoma tanajin danuwarsa na lullubeta tana shiga Kai tsaye daki ta wuce tafara tubewa ta saka Kaya marasa nauyi tayo alwala 

tazo tayi sallah tana idarwa ta kwanta tareda lafewa kan gadon tanajin kaman zazzabi na neman shigarta.

Baccine yafara fizgarta cikin tunanin datai nisa daga sama sama taji Ana Kiran sunanta ta bude idanuwanta ahankali dasukai nauyi sbd kanta daya fara ciwo 

tuni, ta dishi dishi taga kaman jekadi take gani gabanta ta bude idanuwanta gabaki daya tana waresu akanta.

Jekadi data fahimci NURUn Bata gasgata ita bace saita Dan murmushi ahankali tana cewa”

Allah qarawa MUSHRAn maleek kyau da lafiyar bacci.

Da sauri ta tashi zaune har batasan lokacinda tafada jikin jekadin ba ta rungumeta da qarfi idanuwanta na cikowa da hawayen farin cikin ganinta da 

tausayinta tace”

Alhmdlh Masha Allah jekadi kindawo kindowo.

Farin cikine yakama jekadi ta zame tana kallon NURUn wadda Allah ne ya hada kauna tsakaninsu tun farko ta kalli idanuwanta dasuka ciko da hawaye tace”

Karkiyi kuka Allah zakiyiwa godia Allah yaqaro haske a rayuwarki kinji,share hawayen ki gyara fuskanki maleek ke buqatan ganinki tareda afia.

Sai alokacin ta tunoda lailah ta kalli jekadi cikin sanyi da tausayin afia dayake sake kameta tace”

Mum din afia fa??

Ajiyar zuciya jekadi tayi tareda dagowa a natse tace”

Tana hannun hukuma haryanzu sbd anyi bincike an tabbatar itace saidai haryanxu takasa tsayawa ta nutsu tayi bayaninda zai taimaketa.

Shiru sukayi dukkaninsu NURU na jajanta abin cikin ranta da yanda Afia zata dauki abin.

Ficewa jekadi tayi tana cewa tana jiranta a Palo itakuma ta nufi toilet ta wanko fuskarta ta fito ta Dan gyara ta sauya Kaya zuwa doguwar jallabiya maroon 

ta fito tana qamshin turaren _bosslady_ dayake fita ajikinta ahankali Bata saka sosaiba sbd kada taqarawa afia damuwa akan tata hakama Bata shafawa fuskarta 

komaiba duk sbd afia Dan batason saka Mata damuwar wani tunanin daban.

Data fito kallo daya jekadi Tai Mata tana karanto Mata adduoin tsari daga sharrin ido Dana Baki sbd ko Yaya NURUn tafito ita din kyanta me sanyi ne.

Afia kuwa Batada wani kwanciyar hankalinda zaisa tayiwa NURUn kallon tsaf itama dai tayi kokari ta shirya kanta suka fito jekadi na gaba suna baya sai su 

Akira dake take nasu bayan har zuwa bakin sashenshi kowa ya dakata daganan daga jekadi saisu suka qarasa ciki a palo na biyu suka taddashi zaune Yana 

sauraren bayaninda mr Omar keyi Masa hankali kwance Yana sanye cikin wani coffee brown kaftan dasuka fiddo da qyallin da fatarsa keyi kwarjininsa yana sake 

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button