UBAYD MALEEK 43

bayyana tareda cika idon me kallonsa
Yana Jin shigowarsu Bai waiwayoba saima takardun daya bude Yana karantawa na sakin jekadi da akai a yau din
Mr Omar kuwa sauya bayanin dayakeyi yayi da kallon gefensu NURU da cewa”
Barka da shigowa.
Da Kai NURU ta amsa Masa ahankali tana satar kallon gefen maleek din kadan Wanda Bai nuna ya San da shigowar tasu ba
Afia kuwa Batada karfin amsa Masa
Zama sukayi kafin ya dago ahankali ya zubawa NURU idanuwansa dasuka sata saurin cafko numfashinta daya tashi barin jikinta sbd kallon tajisa ajikinta sosai,
ta dago fuska ahankali ta kallesa ya juyarda kallonsa kan Afia tausayin ‘yar tasa na kaunarta na sake shigarsa sbd yanason ‘yayansa fiyeda yanda ake gani
Ya bude Baki Kai tsaye cikin kulawa da kamewa yace”
Afia maleek yaya?kina lafiya dai ko?
Shiru tayi Idanuwanta nason cikowa da hawaye ta dago ta kallesa tana hango kulawa da kaunarta gurin dad din nata sai hawayenta suka gangaro ta girgiza Masa
Kai ahankali tana cewa”
Bana cikin nutsuwa dad.
Dan gyara zama yayi Yana ajiye takardun hannunsa ya sake kame muryarsa yace”
Mum dinki itace damuwarki right?
Gyada Kai tayi tana sauke Kai kalar tausayi.
Afia idan kinmin alqawarin Zaki kwantarda hankalinki ki nutsu kodan karatunki da bawa Taki rayuwar mahimmanci ki daina biyewa tunani irin na mum dinki then
namiki alqawarin Babu abinda zai samu mum dinki zata fita cikin case dinnan lafiya Amma Zaki Bata shawaran ta tafi ta inganta rayuwarta ta wani hanyar kin
saurari abinda nake fada right??
Dagowa tayi ta kallesa da hawayen dake gudu akan fuskarta ta gyada Kai tana cewa”
Yes Dad namaka alqawari Inshallah dagani har ita zamu cika wannan alqawarin.
Daukan takardun gabansa yayi ya bude tareda karban biro a hannun Mr Omar yasaka hannu cikin takardun tareda rufewa ya miqawa Mr Omar yace”
Ka sameta tabaka sunan lawyernta shine zai qarasa aikin yakai takardun can zasu saketa kada abari ‘yan media su sani ko kadan infact dagacan a haura da ita
tabar qasar gabaki daya.
Da sauri afia ta qaraso gabansa tana Masa godiya cikin tsananin farin ciki tace”
Imran ne lawyern mum zankirasa zaizo ayau Inshallah dad.
Sunan Imran data ambata yasa NURU kallon afian ta sauke kanta.
Fita afia NURUn ma ta miqe zatabi bayanta jekadi zata dakatar da ita maleek yayi Mata kallon ta barta ta wuce.
Bayan fitarsu ya kalli Mr Omar yace”
Ayi Mata takardun ganin likitan tabin hankali kada a taba barin afia tasan mum din Tata tasamu tabin hankali sbd shock din wannan al’amarin
a fitar da ita abar Mata gidan Vegas tazauna can taringa ganin likita akai akai har Allah ya yaye Mata
Afia Kuma iyakacinta da ita airport.
Allah yaqarawa maleek tausayi da adalci.
Sai maganar Dan jaridar daya fara wallafa cewan ‘yar uwar…..’dan shiru yayi Wanda yasa Mr Omar da jekadi kallon juna suna Dan murmushin dasu kadai sukasan
ma’anarsa
Mr Omar ya karbi zancen da cewa’
Za’a shigarda bayyananniyar qarar shariar sama akan Wanda yafara wallafa labarin ankashe ‘yar uwar mushrah sbd haryanxu bayan mu da hukumar dake hannunka
babu Wanda yaga asalin gawar ta Yaya yasan wacece aka kashe hadda alaqarta da mushrah,
Dan Haka inda bayanin yafara fitowa zai fada.
Ahankali maleek ya gyada Masa Kai Yana cewa”
Daga gobe kada abarsu fitowa kowa ta zauna a sashenta a tsananta tsaro a hanyoyin bangaroransu sbd komai zai iya faruwa idan aka fallasa zancen qarar Dan
jaridar sbd kada asan inda yasamu zancen.
Juyawa sukai suka fice suka bar sashen nasa sbd wayar dazai fara da kaleeb.
Sbd tsaro Koda afia Takoma sashenta doka aka bayar kadata sake fitowa sai gobe Dan Haka ita Bata damuba take tasaka aka kawo Mata sabuwar waya dayake tana
tareda layinta na qasar saita Sanya ta nemi numbern Imran.
Cikin tsananin damuwar halinda suka samu labarin abindaya faru cikin tsananin damuwa yake tambayar afian Yaya case din ke tafiya sbd case ne na masarauta
babu me halin Shiga danma sunyi mamakin da hukuma tashiga zancen Dan masarauta irin delah gizah sune suke hukuncin komai daya shafesu da kansu Amma Kuma ace
MALEEK dakansa ya bawa hukuma damar shigowa ciki duk da hukumarma tasace sai abinda yace suke amfani dashi.
Cikin nutsuwa afia tace”
Ni yanxu duk wannan bana tunaninsa yanxu sbd ya amince zai sa asaki mum a sirrance tabar qasar Dan Haka kana buqatan isowa cikin gaggawa gobe ka isarda
takardun abaka ita ku tafi
Dan Allah kamun alqawarin zaka kularmin da ita sbd nasan yanzu tana cikin tsananin hali na tashin hankali.
Dan shiru yayi Yana cewa”
Bazai yiyi nazo gobe ba sbd Kar takardun nikadai lawyer bazan iya zuwaba Dole sai munje tareda wani lawyern Wanda zai duba takardun dazanje dasu agurin dama
wannan Dole 2 lawyers ne suke zuwa Dan Haka Ina buqatan time Zan nemo wani lawyer din Wanda zai bamu time dinsa yazo taredani.
Shiru afia tayi cikin tsoro da tashin hankali tace”
Baza’a iya jiraba damace dad yabawa mum Dan Allah kazo kawai an zamu samu wani lawyer din…..