UBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK 44

Katseta afia tayi da cewa”

Dad dakansa jiya gabanki yabada damar komai gameda case din mum din wannan maganar ta sirrice yanzu idan nace zamu dauko lawyer daga waje then komai zai iya 

sauyawa 

So please NURU ki amince dan Allah dad Bai taba dakatar damuba ko hanamu harkan data shafi karatu bare yanzu aiki Dan Allah ki yarda Ina roqonki.

Dagowa NURU tayi takalli afian tareda Dan sauke ajiyar zuciya tace”

Na amince Amma sai dad dinki ya amince Zan nema izininsa.

Shiru afia tayi tana kallon NURUn tana nazarin abin data fada din saidai tunda ta amince batada zabin daya wuce itama amincewa da bayanin tace”

Thank you.

Miqewa tayi zata fice ta dakata da cewa”

 Anjima Imran zai iso inshallah saikuyi mgna.

Ficewa tayi tabar NURUn zaune mamaki na kasheta Jin da Imran zasu tafi kenan.

Faduwa gabanta yayi sbd tunani biyu dasuka shigeta take,

Na farko ta Yaya zata fadawa MALEEK maganar zuwan harda qarin Imran ne abokin aikin,

Ma biyu tayaya zata iya fita daga ita sai Imran bazata iyaba sbd tasan Imran din sai yayi kokarin tado Mata da maganarsu data wuce wadda hakan baya cikin 

abindata shirya dawowa dashi.

Bangare daya afia nason daureta da jijiyoyin jikinta.

Daqyar ta iya tashi daga Inda afian ta barta ta nufi bedroom tafada toilet jekadi dake jinsu batace komaiba ta juya ta fice daga sashen Kai tsaye ta nemi 

numbern Mr Omar ta fada Masa komai yace idan yadawo zai sanarda maleek.

Qarfe goma Sha biyu na ranar Mr Omar ya sauka a airport na gizah na dawowarsa Dan yagamo abinda yaje Yi Kuma adaidai lokacin Imran jalal ya sauka a airport 

din cikin sa’a suka hadu dukkaninsu motar masarauta tazo daukansu shi Mr Omar drivern maleek yazo daukansu shikuma Imran drivern Anneti afia tasaka yazo 

daukansa.

Kallon kallone yashiga tsakaninsu Mr Omar ya saki wani murmushi Yana miqawa Imran din hannu yana kallonsa yace”

Barka da zuwa Barr Imran jalal and all the best.

Miqa Masa hannu Imran yayi Yana cewa”

Thank you Mr Omar.

Murmushi Mr Omar yasake sakewa Yana Dan kallon gefen Imran din yace”

Kai kadai kazo??

I mean nasan kasan kana buqatan wani lawyern ga aikin.¿

Sai alokacin Imran yasaki murmushi Yana kallon Mr Omar din yace”

Aikina ne Kuma nasan da hakan shiyasa lawyern da nake buqatan muyi aikin tare tana Nan Dama 

Fata dai kawai idan zaka iya jimirin ganin hakan.

Wani irin Murmushi me Fadi Mr Omar yasake Yana sake cewa”

Good luck with that too.”ya juya ya wuce Yana sake sakin murmushi yashige mota aka jashi sukabar Imran din a tsaye Yana bin motar da kallo kafin ya sauke 

numfashi me zafi yashiga tasa motar da akazo daukansa  suka wuce Suma Yana Jin tamkar zuciyarsa nason karbuwa da qiyayyar Mr Omar sbd koyaushe shine yake 

shiga hancinsa da kudundune Amma sbd qiyayya bata cikin abindayake Bari Yana shigarsa yasa yake yaqar hakan Yana dannewa sbd ya dauki qiyayya wani aikin 

wahala da kake dorawa kanka yazo Kuma ya ringa wahalar dakai ka rasa focus da sukunin rayuwa karshe ka wargaza kanka agurin qiyayyar wani.

Kai tsaye dukkaninsu masarauta suka nufo cikin sa’a kusan atare motocinsu suka iso Mr Omar ya wuce Kai tsaye sashen maleek daukeda sketch din dayazo dashi 

daga delah shikuma Imran afia ce da kanta ta bada umarnin kaisa sashen baqi na musamman kafin ya huta suyi mgn.

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button