UBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK 45

Sai yamma lis ta fito suka hadu da Imran din suka nufi sassan Anneti sbd sosai yake girmamata itama duk cikin familyn lailah shine yaron datafi ganin

hankalinsa fiyeda kowa har iyayensa shiyasa akwai mutuntawa a tsakaninsu ba laifi tana yaba Masa.

A palon Anneti din na farko suke zaune suna gaisawa tana sake tambayarsa family tareda jajanta Masa abin daya farun na lailah Yana jajanta Mata itama.

Duk maraice NURU na zuwa gurin Anneti din hakama yau Kai tsaye ta nufo sassan cikin sanyi da nutsuwa tareda jekadi tana sanye da doguwa riga dark purple

suka qaraso sashen da sallama dauke abakinta tashigo
Dukkaninsu suka dago kowa na zuba Mata ido da nasa tunanin.

Ganin Imran datai shine abu na qarshe da Bata tsammanaba ta sunkuyar dakai tana kokarin juyar da hankalinta daga kansa ta nufi Anneti ta zauna kusada ita

tana gaisheta cikin biyayya Kamar ko yaushe
Cikeda kulawa Anneti ta amsa tana miqewa Dan amsa wayar da ake Mata ta shige ciki tana cewa”

Ina zuwa.

Murmushin qarfin hali NURU tasaki tareda Dan waiwayowa ta kalli su afia din a natse tacewa imran”

barka da zuwa.

Boyayyar ajiyar zuciya ya sauke tareda dagowa ya ‘dan kalleta ya dauke Kai Yana cewa”

Thank you.

Yi afia tayi Kamar batasan meya taba faruwa tsakaninsuba ta gyara zama tana fuskantar kowannensu tayi musu godiya tana cewa”

Anjima zata karbo takardun daga hannun Mr Omar yabawa imran.

Qala NURU Bata samu cewaba sai Dan yaqen murmushi datayi ta miqe tana cewa”

Zan koma.

Tashi sukayi dukkaninsu suka fito tare afia na kokarin Jan kowannensu da zance sbd su samu sakewa kada itadai asamu matsala agurin fitar mum dinta.

Suna fitowa kofar sashen gabaki daya daidai isowar MALEEK Mr Omar na gefensa Yana Masa wani zancen Wanda kullum baya rasa zance tsakaninsa da MALEEK.

Kwarjininsa da cika musu idon yayi yasa dukkaninsu sauke Kai Banda NURU data dago ta kallesa zuciyarta na narkewa saidai dukkaninsu Babu Wanda yasamu ko

kallo daga garesa ya wucesu ya shige saidai abin mamaki Yana shiga din saiga dukkaninsu sun dawo Banda NURU wadda ta nufi sashenta zuciyarta ba dadi.

Ba wani fargaba ko tunanin komai afia ta sanarda dad dinta gameda zuwan Imran da aikin dasuyi din shida NURU tareda amincewar NURUn sai daidai lokacin ya

dago ya kalleta da idanuwansa dasuka sata Jin tana neman fara rawar murya.

Ya maida kallonsa kan Imran ahankali kafin ya juyarda kallonsa kan Mr Omar ba wani zance Mr Omar ya kalli Imran yana cewa”

Bismillah muje abaka takardun.

Dan kallon maleek Imran yayi Dan Dole cikin girmamawa yace”

Ka huta lafiya” ya juya yabi kofa da Mr Omar yake nuna Masa suka fice.

Kasa sukuni afia tayi ta juya ta fice da sauri itama tana cewa”

Kafito lafiya dad.

Tana fitowa ta wuce sashen NURU Kai tsaye saidai Koda ta isa NURUn Bata wani cikin walwala sbd cewa tayi kanta na ciwo sai tabarta Dan tasamu ta huta sbd

goben.

Juyar da Kai NURU tayi tana Dan rufe idanuwanta kallo daya maleek ya Aiko Mata Yana dawo Mata sbd itakai ta lurada kallon Wanda yasa duk taji Kamar zazzabi

na neman kamata ta sauke qaramin numfashi ahankali tareda tashi zaune sbd sallar magriba datayi ta nufi toilet tashiga tayo alwala tana fitowa farhat na

shigowa a Sanyaye tace”
Jeki kiyo alwala sweetie muyi sallah ko.

Zaune yake cikin palonsa bayan sallar magriba Yana kallon sketches din guda biyu dasuka nuna mutum dayane da Wanda yakaiwa Yan jaridar da Wanda yabada meriz

ya sake kallon idanuwansa
Cikin nutsuwa Mr Omar yace”

Yakoob ne.

Dan waiwayosa maleek yayi cikin kamewa yace”

Ya aika sketches din gurin hukuma tareda bayanin komai da aka hada akan case din gobe ko jibi Inshallah za’a Kai karshen matsalar Ina buqatan komawa Paris.

Dan shiru Mr Omar yayi Yana Dan Sosa tsakiyar kansa kadan cikin Dan tausasa harshe yace”

Maganar shigar mushrah cikin maganar MSS LAILAH akwai hadari sbd abune na sirri dakuma hadari sbd neges nada mutane ko Ina
Akwai hadari zuwanta is too risky Kuma tareda umnn ummn Imran din ma is….

Wani Abu maleek din ya Dan hadiye batareda ya kalli mr Omar din ba yace”

Yaushe ne tafiyar daukan lailan??

Gobe ne Inshallah da karfe Tara na safe yace sbd jirginsu zai tashi karfe goma na safe.

Shiru yayi na wani lokaci kafin ya miqe tsaye ya fuskanci kofar shigewa palonsa na kurya cikin kamewarsa da muryar asalin MALEEK dinsa yace”

Kaji da aikin fitarsu lailan daga qasar ita wannan ko haske waje gobe bazata gani ba zanji wannan.

Dan sunkuyar da Kai mr Omar yayi Yace”

Maleek tariga ta amince da cewar zataje ko Zan sanarda jekadi dokar kada abarta fitowa din sbd kada taje din batareda ankarewar muba….

Kallo daya maleek yayi masa yayi saurin Dan soke Kai Yana cewa”

Nagane zanji da fitarsu lailan gobe
Saida safe ahuta lafiya.

Sidadewa yayi ya fice daga sashen gabaki daya Yana murmushin dayasan na menene shikadai sbd duk duniya ko motsi maleek yayi yasan me yake nufi bare kallonsa

wannan wata baiwace da Allah ya hadasu akanta shiyasa Babu me iya sanin sirrin tsakaninsu cikin ransu Allah yasaka musu qaunar junansu Dan dai shi Yana

qarqashin maleek din ne yasa maleek nasa kulawan yake a boye shikuwa dama ko ransa zai iya badawa akan maleek.

Yana fitowa gabaki daya daga sashen na maleek ya ciro wayarsa ya Nemo numbern jekadi ya Danna Mata Kira Yana kokarin daidaita kansa Dan cika aikin

ubangidansa tana dauka Kai tsaye yace”

Zuwa anjima maleek na buqatan ganinta a rakata sbd tsaro.

Yanayin yanda yayi maganar yasa jekadin amsawa tana satar kallon NURU wadda ke zaune Palo farhat na jikinta suna kallon cartoon din da hankalinta baya wani

kai duk da dai tana Dan murmusawa kadan idan akai abin dariya.

Sai da akayi sallar ishai suka tashi sukai sallah suna idarwa tasa aka jera abinci sbd farhat Dan ita Bata wani Jin yunwa tadaisha sabuwar madarar raqumi me

dumi wadda kullum ake kawowa safe da dare daga sashen Anneti.

Suna gamawa suka nufi daki farhat ma dakinta ta nufa tayi wanka Da kanta ta shirya cikin kayan bacci tazo dakin NURUn ta haye gado ta kwanta.

Wanka NURUn tayo itama ta fito ta shafa Dan neu oil kadan ajikinta tareda shafa body mist da sprays masu sanyin qamshi ta daure gashinta da band qarami ta

dauko rigar bacci me tsantsi tasaka ta nufi gadon zata hau taji knocking din kofar dakin ta juya ahankali tana kallon agogo kafin ta qarasa jikin kofar Dan

tasan jekadice ta bude Kai tsaye.

Ajiyar zuciya jekadi ta sauke tareda kallon NURUn tace”

Maleek na buqatan ganinki yanzu.

Shiru tayi tareda kallon jekadin cikin mamaki a natse zatai magana saita fasa ta juya Takoma ta dauko sabuwar  free jallabiya ta saka akan rigar baccinta

dako bra batada ajiki ta zari qaramin gyalen rigar ta rufe kanta ta kalli farhat tana Dan shafa kanta yace”

Ina zuwa sweetie kinji.

zuro slippers tayi ta fito jekadi na gefenta suka nufi sashen nasa.

Suna Isa har kofar palon kuya jekadi ta rakata ta dakata daganan tareda kallonta cikin nutsuwa tace”

Afito lafiya” ta juya ta fice daga sashen gabaki daya masu tsaron gurin suka sake rufe sashen duka.

Bude kofar tayi a natse tashiga da siririyar sallama bakinta.

Sanyi da qamshin turarensa ne suka cika palon ba motsin komai sai tv dake aiki itama murya can qasa kaman Koda yaushe.

Baya palon Dan Haka ta daga Kai ta kalli kofar shiga bedroom dinsa sai taji shakkar qarasawa ciki Kai tsaye
Ta dauke Kai tana Dan sauke numfashi bugun zuciyarta na sauyawa ta daure ta taka ahankali ta Isa kofar dakin ta Dora hannu ahankali kan handle din kofar

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button