UBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK 48

 

Mamuhgee 48_*Kallon yakoob Mr Omar yayi Yana gyara tsayuwa yace”

Allah ya yafe Masa kurakurensa tareda Kai mahaifinsa daka dorasa akan irin wannan rayuwar da batada hanyar bullewa ko a duniya ko agurin ubanginka,

Son Rai da bin zuciya qarshensa baida Dadi yakoob Amma tunda kune kuka zabi hakan hakan shine daidanku,

Babban kuskuren daka aikata yakoob shine sako ‘danka da baida kwarewa acikin wannan harkar dakai ka Jima da dadewa acikinta Dan kuwa gashi kuskurensa 

yakaisa ga Haka kaima yakaika ga hakan.

Allurar meriz ce ta kashesa kaman yanda kukai amfani da ita Dan kashe tsohon NEGES mahaifin maleek Kuma kukaso kashesa da ita,

Kun aikashi kashe padima saidai kun manta cewan a sashen maleek ne take 

Kuma a sashen Babu wani lungu da Babu camera a maqale Wanda idonku da zuciyarku sun rufe da aikata hakan kuka saka Amed disconnecting dinsu Wanda ko karatun 

addini bayadashi bare na zamani Dan Haka ta Yaya kuke tunanin zainiya ciresu.

Ranarda muka samu labarin zuwan lailah gizah muka tabbatarda akwai dalilin zuwan nata Wanda anyi kirantane Dan ayi amfani da ita hakan yasa muka sauya 

tunani ta hanyar Dena shayarda padima meriz sbd ga hanyar sauki tazo Mana,

Tunda neges yayi magana da lailah tafara bibiyar jekadi Wanda jekadi tagane hakan ta sanar Mana daga lokacin mukasan meyake faruwa har lokacinda muka 

tabbatarda amed na bibiyar lailah itama bamui wani motsiba muka barku Dan ku aiwatar da naku Shirin dazai bamu tamu damar.

Kaf gizah Babu Wanda yasan da padima na cikin masarautar shiyasa muka kyaleku Dan munsan Dole bazaku barta ba duk da batasan ainihin waye yasakata aikin 

daya sakata ba ahaka rashin nasararku yakaiku aika amed kashe padima wadda taji sauki da kanta zata iya Kare komai kuma a Daren ranar jekadi ta miqa Mata 

allurar meriz a hannunta ta sanarda ita duk Wanda ya shigo kawo Mata farmaki ta tabbatarda ta kwaci kanta da allurar Wanda hakan zai fidda ita daga wannan 

rigimar gabaki daya har abada.

Padima na son ranta fiyeda masoyinta amed Wanda shima yakeson dukiya fiyeda rayuwarta Dan Haka a Daren ranar abindaya faru shine bayan yaja lailah da dubara 

zuwa gurin Dan kisan ya hau kanta mun gani Kuma mun sanarda jekadi komai kafin isowarsu gurin Dan Haka jekadi tasake nanatawa padima tana sane ya fito 

lailah ta doketa saidai bamuyi tsammanin amed yaqara doke jekadin ba yasamu ya qarasa dakin ya bige lailah ta hanyar kwada Mata katako akai Wanda ganinsa 

yasa padima shiga tashin hankali saidai Bata Bari tsoronta yabarta barin amed yasamu sa’ar kashetaba tayi amfani da matsayinta na mace ta nuna Masa kanta 

amatsayin su Raya darensu na qarshe kwadayin Zina yajasa ga rasa ransa batareda yasamu abinda yake kwadayinba.

Babu Wanda yasan padima na kasar tayaya Yan jaridar suka San waye aka kashe bayan Babu Wanda yaga gawar da idanuwansa wannan shine babban kuskurenku na biyu 

daya kawo karshenki batareda ansha wuyar hakan ba,

Padima ta kashe amed sbd Kare Kai itama Allah yabata nata sakamakon ta hanyar rasa cikakken hankalinta kamar lailah Da Haka kowa zai girbi nasa aikin.

Allah ya tsare Mana imaninmu yabamu kariya daga mutane kamarku Wanda suka Tara arziki ta hanyar kisa da miyagun ayyuka gashinan dukiyar Zaki tafi ku barta 

abawa mutane suna Kuma tsine muku.

Juyawa yayi ya fice yabar yakoob din tsaye cikin rashin sanin makamar tunanin Yi sbd dukkanin gangar jikinsa da jininsa sun tsaya cak Babu abinda yake motsi 

ajikinsa bayan zuciyarsa dake bugawa ahaka aka jasa Yana tangadi aka fice dashi

Take ‘yan jarida aka sakar musu labarin suka fara yadawa cewan 

Yakoob amintaccen bawan neges ne ya kashe tsohon NEGES na gizah 

Take aka bayyanarda shedu dasuka hada da garin meriz dake ciki sarkar da padima ta taba boyewa da aka samu a sashensa gurin bincike.

Hankalin jama’ar gizah ya tashi tareda girgiza matuqa sbd kishin kishin fara zargin NEGES da akai Wanda yasa akai gaggawar yankewa yakoob hukuncin kisa ta 

hanyar cire kansa sbd kada ragewa fitinar tsayi 

Amma duk da hakan ba a daina bayyanarda zargin NEGES ba Wanda yasashi kasa fitowa sbd tsananin kunyar kansa da baqin ciki me nauyi daya lullubesa sbd Kai 

tsaye ko an boye laifinsa saidai yasa jama’a yin shiru Amma wannan zargin da laifinma gabaki daya bazai rufu ba musamman da kaleeb da maleek sukai shiru 

sunki saka Baki a maganar sai hakan yasake bawa jama’a kwarin gwiwa aka fara kishin kishin sauke neges jama’a da jinin sarautar gizah da ‘yan delah gabaki 

daya kowa yafito ya nuna sha’awarsa ta sauyin neges sbd kobabu saka hannunsa zamtowar bawansane ya aikata hakan to tabbas hakan ya shafesa Dan Haka gabaki 

daya kusan ya rasa girmansa da mutuncinsa a idon jama’a

Musamman Anneti da yakejin Kamar bazai iya hada idanuwa da itaba sbd girman kunyar abindaya aikata Wanda yasan itama yagama fahimtar komai saidai kawai tayi 

shiru sbd wani abin basai kafadaba Allah ya kyauta kawai yafi maka saukin fada

Da wannan ya kebe kansa da kansa a sashe dabam bayan ya fitar da wasiqar sauka mulki da kansa ya aika har delah gurin kaleeb Wanda har lokacin yaqi cewa 

komai bare maleek daya fara Shirin barin qasar bayan ya bayarda sunan Mohan YONAS (autan kaleeb) amatsayin Wanda za’a nada sabon NEGES na riqon kwarya kafin 

lokacinda zai karba Dan haryanzu Yana buqatan wani Dan lokaci kadan kafin yadawo gabaki daya ya karba gizah din.

******

Zazzabinta yayi sauki sosai ba laifi Dan kuwa Daren tasamu tayi bacci sosai sbd wani magani da jekadi ta kawo Mata Dan Haka gari na wayewa tun karfe shida 

da mintuna ta fito cikin doguwar jallabiya data rufeta koina ta nufi sashenta tana Isa ta wuce bedroom dinta tashige tana sauke numfashi ahankali kafin ta 

dago ta kalli farhat dake kwance kan gadonta tana bacci cikin nutsuwa 

Ta qarasa gadon ta zauna tana kallonta tasaki murmushi ahankali tace”

Sweetie nayi missing naki da surutunki sosai.

Miqewa tayi ta zare rigar jikinta ta jefa cikin wardrobe ta nufi toilet ta shige.

Kodata fito komawa gadon tayi ta haye ta kwanta gefen farhat ta gyara musu rufa Takoma bacci sbd baigama isartaba.

Qarfe tara ta farka lokacin har farhat ta Jima da farkawa ta bude idanuwanta ahankali tana kallon farhat dake Kiran sunanta cikin murna da farin ciki tace”

Aunt NURU yaushe kika dawo?

Tashi zaune tayi tana gyara gashinta da murmushi akan fuskarta tace”

Sweetie na barci nadawo

Ya kike?

Fadawa jikinta tayi ta rungumeta tana cewa”

Next time idan zakije tare Dani Zaki Zan biki kinji Aunt NURU.

Wani irin Murmushi ne ya saukowa NURUn ta kalli hancin farhat din zuwa bakinta dasuke Zak Zak Dana dadynta saita sake sakin murmushi tana saukowa gadon 

tace”

Kinyi brush?

Biyota tayi tana cewa”

Eh nayi nace next time zakije Dani??

Tsayawa tayi tareda juyowa ta kalli farhat din ta kamo fuskarta taja hancinta ahankali tana murmushi tace”

Wannan hancin Ina sonsa sosai kaman yanda nake son sweetie dan haka kidainama tambayan idan zanje wani guri ba dakeba ok¿.

Cikin murna tace”

I love you too lewa.

Knocking kofa akai ahankali tareda bude kofar aka shigo 

NURU ta dago tana waiwayowa kofar sukai ido biyu da afia dake kallonta da dukkanin hankalinta tana nazarin NURUn da akace batada lafiya saidai bataga alamar 

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button