UBAYD MALEEK 48

ciwo atareda NURUn ba jikinta ba inda ya nuna alamar akwai ciwo tareda ita ta karaso ahankali cikin ‘yar kulawa da alamar tambayarta tace”
Jekadi tace bakida lafiya da fatan dai ba wani serious ciwo bane ko??
Murmushi NURU tasake tana matsowa gaban afia din tace”
Naji sauki kawai gajiya ce da rashin isashen bacci Amma yanzu lafiyana kalau.
Kallon cikin idanuwanta afia tayi tana kokarin karanto idan da akwai ciwon atareda NURUn tace”
Mezaisa ki kasa samun isashen bacci bayan kina samin hutu sosai bakida aikin komai a gabanki….
Aiki dad dinku yabani Wanda duk ya kawo hakan yanzu dai inason Baki hakuri akan rashin samun damar zuwana gurin mum dinki I am really really sorry for that
Kuma Ina fatan komai yatafi yanda ake fata?
Ajiyar zuciya afia ta sauke tana qarasawa bakin gadon dakin ta zauna tana cewa”
Komai yatafi yanda akeso mum Dina tana Las Vegas tareda Imran Wanda yakoma can yanzu da zama da aiki sbd su manta rayuwarsu ta baya su fara sabuwar rayuwa
Mara damuwa da Danasani.
Numfashi NURU ta sauke cikin ahankali tareda ajiyar zuciya tana kallon Afia da taushin murya tace”
Ina musu fatan kyakkyawar rayuwa me Dadi da amfani.
Thank you afia tace tana kallon fuskar NURUn data sauya Mata gabaki daya.
Wanka NURU tashiga ta fito cikin nutsuwa ta shirya cikin doguwar riga golden me sequence ajiki suka zauna dukkaninsu su ukun anan sashenta sukai breakfast
tare suna gamawa suka dawo Palo suka zauna NURU na Shirin zuwa gurin Anneti afia ta kalleta tareda dawowa gefenta ta zauna cikin nutsuwa ta kalleta tana
tattaro abinda zata fada Mata tace”
Shin kinsan case din kisan da mum take ciki padima ce wadda ake cewa ta kashe……
Wani irin kallo NURUn juyo tanayiwa afia din da dukkanin fararen idanuwanta.
Wata ajiyar zuciyar afia takuma saki tana dafa hannun NURUn tace”
Padima ce wadda dukkanin labarai da duniya ta shedarda an kashe….
Hawayen dasuka ciko fararen idanuwanta dasuka koma ja Nan take suka gangaro kan fuskarta ta sake kallon afian da kyau tana kasa gasgata zancen sbd bazai
yiyuba babban zance irin wannan a boye Mata
‘yar uwarta jininta aka kashe ace Bata saniba sai yanzu bayan wadda tayi kisan har ansaketa ta tafi Kuma maleek na sane da hakan,wane hali iyayenta suke
ciki gameda wannan mummunan al’amarin na rasa padima itakuma Bata tareda dasu a lokaci irin wannan miqewa tayi zuciyarta da idanuwanta na rufewa da wani
irin yanayi Mara Dadi da damuwa
Afia tayi saurin riqota tana Miqewa tsaye cikin nutsuwa da kulawa tace”
NURU ki kwantar da hankalinki anyi bincike angano komai da cewan ba padima bace kawai yan media ne suka juya zancen sbd basusan ainihin wayeba aka kashe
angano komai yanxu tareda gano Wanda sukeda hannu a komai har kisan tsohon NEGES wato mahaifin dad dinmu komai ya wuce yanzu Inshallah…
Girgiza Kai tafarayi ahankali hawayenta na tsananta gudu cikin wani irin yanayi na toshewar Kai tace”
Bani wayanki inason Kiran abal Dina Ina buqatan Jin halinda suke ciki,
Ina buqatan magana da padima
Mezaisa padima ta zauna Nan har irin wannan Abu yasameta,
Ni gabaki daya ban fahimta ba,abal nakeson magana dashi yanzun Nan……
Cikin sanyi da son kwantar Mata da hankali afia ta miqa Mata wayarta tana cewa”
Dan Allah ki nutsu kada ki dagawa su abal din naki hankali idan har Basu saniba, ki tambayeshi ta yanda bazaki daga hankalinsu ba muji idan padiman na
taredasu.
Bata tsaya sauraren sauran bayanin afia ba ta hau saka numbobin abal dinta ta Danna Masa Kira zuciyarta na rawa.
Kamar zata tsinke saigashi ya daga cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yayi sallamar data Sanya NURU saurin riqe numfashinta tana seta muryarta tace”
Abal.
Jin muryar NURU yasa abal din tashi zaune daga kishin giden dayake Yana kallo a tv cikeda kewarta da kaunar ‘yarsa yace”
NURU kece?
Kina lafiya?
Ya kike?
Yaya maleek da yaransa?
Shiru tayi zuciyarta na sake bugawa ahankali muryarta na rawa tace”
Abal Ina padima?
[ad_2]



