UBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK 49

Kayan marmari aka kakkawo aka jere musu Anneti tasa aka kawowa NURU nata hadin wani sirrin daban suna ‘yar Hira sama sama jekadi na miqo Mata tana Sha a Dan kunyace harsuka Gama sukai sallar magriba Basu barota ba sai bayan ishai 

Suna fitowa afia ta kalli NURU cikin sakewa tace”

Meye sirrin wanna maganin da Anneti ke Baki?

Kodai na……

Kallonta da NURU tayi yasata dakatawa da zancen tana ‘yar dariya.

Murmushi NURU tayi tana tafiya a natse tana cewa”

Idan nafada Miki sirrin bazaki iya bacci ba nikuma inason ki ringa samun bacci yanzu sbd ki koma AFIA UBAYD MALEEK dinki ta asali duk wannan ‘yar ramar ta fice.

Murmushi afia tayi tana cewa”

Thank you Ms NURU YONAS.

Suna Isa ko zama basuyiba saqon mr Omar ya samesu na cewa gobe zasu koma Inshallah Dan Haka su shirya.

Wanka kawai tayi tayi Shirin bacci ta haye gado ta kwanta da wuri sbd ciwo ciwon Kai datake ji.

Washe gari da safen kayanta ta hada acikin qaramar akwati saina farhat data saka Akira ta hada Mata ta shirya tsaf ta nufi sashen Anneti tareda jekadi dake gefenta tana sake nanata Mata wasu maganganun akan zama na aure.

Koda suka Isa ga mamakinta kusan kayayyaki ta tarar jere a tray Ana jiranta Kai tsaye Anneti ta nuna Mata kujera tana cewa”

Zauna jekadi ki nuna Mata komai yanda yake ta shanye shekara daya zasuyi ajikinta suna aikinsu.

Miqewa tayi ta shige sbd ganin yanda NURUn kejin kunyar Sha din

Tana shigewa jekadi ta zage tana zuzzuba matasu tana Bata tana shanyewa a wahalce sbd sunyi Mata qarfi sosai a Baki daqyar ta shanye kusan duka sauran daya rage ganin tana neman yin amai yasa Dole jekadi ta qyaleta.

Koda Anneti ta fito daukeda kyautar Dan qaramin akwatin turarukansu na asalin hadin Ethiopia masu wani irin kamshi kamar na turarukan oud ko itacen turaren wuta qamshinsu dai me sanyi da Sanya nutsuwa ta miqawa NURUn tana cewa”

NURU Allah yayiwa aure albarka.

Amin jekadi tace tana karbanwa NURUn wadda take godiya cikin girmamawa da ladabi kafin sukai bankwana suka fito.

Qarfe goma Sha daya suka fito zuwa airport har lokacin Babu Wanda yaga MALEEK acikinsu har suka Isa airport suka shiga jirgi jirginsu ya daga Saida suka Isa Paris suka sauka tukuna suka San bataredashi suka dawo ba shi sai bayan nadin sarauta zai dawo.

Ajiyar zuciya dukkaninsu suka sauke lokacinda suka fito daga cikin motar data ajesu daidai kofar shiga palon gidan 

NURU ta lumshe ido tareda karanto adduar samun zaman lafiya da ingantacciyar rayuwa a gidan auren nata tayi bismallah ta jefa kafarta ciki da sallama tana kallonsu mum Sarah dasuka jera suna Mata sannu da zuwa cikin farin ciki da murnar dawowarsu.

Afia ma kusan adduar samun nasarar rayuwa da qarfin gwiwan cigaba da rayuwa kaman da tashigo tana murmushi wa su mum Sarah dasune kusan suke taredasu tun suna yaransu haryanzu Dan Haka yanzu ta yarda da cewa basai Wanda ya haifeka yake iya zama uwa agarekaba hakama basai jininka ne kawai zai amsa sunan ‘dan uwa agareka.

Da wannan kowaccensu ta nufi dakinta sukai wanka da salloli suka fito cin abinci,

Sanyeda wasu riga da wando marasa nauyi ta fito gashinta a daure kyakkyawar fuskarta tayi fayau ta nufo dining din afia tabita da kallon burgewa sbd ita akoda yaushe tana yiwa NURU kallon kyakkyawar halitta me sanyin kyau da shiga zuciya saidai takasa ganewa ko ta yadda dad dinta da NURUn zasu iya rayuwar aure a tsakaninsu.

Ganin kallon da afia ke Mata yasata sakin murmushi Tana zama kan dining tace”

Thank you.

‘yar dariya afia tayi tana cewa”

Kinma riga kinsan Ina yabawane kenan.

Wani murmushin takuma saki tana cewa”

Nariga nasan ko kallonki me yake nufi ai.

Suna Gama cin abincin kowaccensu ta nufi daki sbd gajiya da baccin dasuke buqata musamman gobe kowaccensu tayi niyar fara fita makaranta sbd satin zasu fara exams dinsu na karshe Inshallah kafin sukama ayyukansu na Gina career dinsu.

Rashin waya a hannunta yasa washe gari kafin su Isa makaranta tasa aka tsaya wani qaton shagon waya ta siya waya tasaka layinta suka wuce tana gani sakon baquwar number na shigowa wayarta batareda ta duba ba ta saka wayar jaka ta shige class.

Sai yamma suka dawo wanka tafara yi kafin ta Dan kwanta tayi hutun AWA daya da rabi kafin lokacin sallar magriba yayi ta tashi tayo alwala tazo tayi sallar ta Dan dauko takardunta zatai karatu sai alokacin ta duba wayarta ta bude sakon daya shigo dazun taga ansaka”

_Inidemìní āderíki kwēn of GIZAH_

(Gud morning Queen of gizah)

Wani irin Murmushi ne ya sauka kan kyakkyawar fuskarta har tana Dan dafe goshinta sbd wani yanayi data tsinci kanta bayan karanta sakon tasake kallon numbern ta Dan sunkuyar dakai tana murmushin sbd sanin tabbas MALEEK ne yayo sakon ta daga wayar ahankali tanason yimasa reply Amma takasa sanin me zata rubuta saita ajiye wayar tareda daukan takardunta tana karatu Wanda fiyeda Rabin hankalinta baya Kai Yana kan tunaninsa.

Kwana shida sukai da dawowa suna zuwa school aka fara exams Dan Haka kansu yadauki zafi Sosai musamman afia dasuke likitoci gabaki daya basuda lokacin kansu bare na gida shiyasa farhat ta daga musu kafa Dan itama nata karatun Yana daukan zafi yanzu sbd tashiga secondary yanzu.

Daga NURUn har afia gabaki daya kashe wayoyinsu sukai suka ajiye Saida suka kammala Kuma har lokacin maleek be dawoba sbd abubuwan dayakeson saisun daidaita a gizah kafin yabarota shiyasa shima ayyaukansa na Nan Paris suka taru ga hutu dayake buqata na duk wainnan gwagwarmayar da akai Yana buqatan samun nutsuwa.

NURU ce tafara gamawa da kwana biyu kafin afia Nan hankalinsu ya kwanta suka hau Taya juna murna tareda farin ciki har wani Dan party suka hada acikin gida na tsananisu su uku da farhat saisu mum Sarah da ‘yan aikin gidan NURU da kanta tayi musu katoton cake suka yayyaknka abinsu aka bawa kowa sunata farin ciki dayake ciki Palo ne sukai abinsu Babu me wasu kayan nauyi ajikinsu 

Ita afia jeans ne three quarter da blue da purple riga Mara dogon hannu 

Itama NURUn pencil jeans ne dogo dayafi na afia tsayi ajikinta Ash daya kwanta jikin dogayen sirarun cinyoyinta da fadin hips dinta sai farar riga me hannun shimi ta nufi kitchen ta wanko hannunta daya Dan baci da cake ta fito duba massages dinta saiga Kiran abal dinta ta daga cikin farin ciki suna tayata murna da Dan mamaki tace”

Abal waye yafada muku?

Murmushi abal dinta yayi kawai ya bawa amminta ta tayata murna itama tareda Sanya Mata albarka aka bawa meryam Nan tahau ihun tayata murna tabawa afia itama sukai Mata adduoi da Taya murna ta karba wayan kenan ta Dora a kunnenta taji qamshinsa daf da ita sosai Yana Shiga hancinta tayi saurin juyowa ahankali tana sauke wayar daga kunnenta 

Sukai ido biyu dashi Yana tsaye daf da ita a bayanta fararen idanuwansa nakanta Yana Mata kallon daya sata juyawa ta kalli gefen Afia ahankali wadda itama gabaki daya Bata lura da shigowar dad din nata ba 

Ahankali ya bude bakinsa daya motsa kadan ba sauti yace”

Congrats lewa.

Wani irin Murmushin farin cikine me tsanani ya lullubeta ta matso ahankali ta matsu dashi sosai ta lakaci tsakiyan cake din dake gefenta kadan da babban yatsanta takai bakinsa ya bude bakin ahankali ta zura Masa yatsan ya kame ya kasa hannun da harshensa ta lumshe ido ta bude tana zare yatsan sbd Jin yanda yake tsotsa ya Kai hannu ahankali zai kamota 

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button