UBAYD MALEEK 50

Wata irin sabuwar rayuwa suke a qasar ta zararrin masoyan da basa ganin kowa sai junansu
Dan kuwa yanzu ko irin kayan datake saka Masa cikin daki sun gama makantar da idanuwansa da ganin kowa bayan ita musamman da yanzu ya koya Mata batada gurin zama sai kan cinyoyinsa da jikinsa.
Tana waya dasu afia sosai saidai har lokacin takasa fada mata inda take tadai sanar da ita Bata tafi delah ba tana gida sbd cewa abata su abal su gaisa afian datai.
Su abal ma dadin duniya da farin ciki ya ishesu duk lokacinda sukai waya da ‘yarsu
Itakuma padima kullum akai waya da NURU sai kaman ciwon ya tashi sbd ta ringa Kiran sunan NURU kenan yinin tana cewa ta yafe Mata.
Satinsu uku cif suka dawo gida har lokacin su afia Basu dawoba sbd afia data gane mahaifiyarta tana samun ‘yar matsalar juyewar Kai wani lokaci shiyasa takira dad din tasake rokon yaqara Mata sati daya yakuma qara musu din.
Koda suka dawo kallo daya mum Sarah tayiwa NURUn ta dauke Kai tana yaba zallar kyau da cikar data Karo shi kansa oga kwata kwatan Mr Omar dinga satar kallonsa yayi Yana Masa barka barka akai akai har Saida maleek din ya kallesa yace”
Yaushe ka zama me saka ido Mr Omar?
Murmushi yayi Yana shafa Kai yace”
Allah dai yaqara maleek lafiya da kwanciyar hankali.
Dan guntun murmushi shima yasaki Yana share Mr Omar din sbd dama yasanshi da ‘yar Karan saka Masa ido musamman daga baya bayan Nan.
Kwanansu biyu da dawowa yayi tafiya tareda Mr Omar bayan yagama aikin bada Baki sbd kedaicin dazata shiga basu afia babushi
A ranar kafin ya wuce yakira afia yace su biyo jirgin washe gari su dawo gida
Afia tace to.
Washe gari da yamma saigasu sun dawo cikin tsananin farin ciki da murna tarbesu ta rungume farhat kafin ta rungume afia din tana cewa”
Oh my God I missed you guys so much
Musamman wannan beautiful sabuwan likitan tamu” taqarasa fada tana kallon farhat data tsuke fuska zatai mgn ta tareda da Bata kiss a goshi tana cewa”
My sweetie kinsan kece farko a zuciyana basai kince komaiba kinji.
Har dakin afia din suke duk su dukansu suka zauna afia na sauke ajiyar zuciya tana lumshe ido tace”
Alhmdlh Ya Allah
Gida me Dadi.
Murmushi NURU tayi tana tayata janye akwatin ta gefe tace”
Keda Zakiyi aure wata Ran kitafi
Amma nidai har banason tuna ranar
I don’t wnt you to leave us” taqarasa fada tana kallon afian cikin kwabe fuska.
Dariya Afia tayi tana miqewa ta dauko wayarta cikin Jakarta tadawo kusada NURUn ta zauna tana cewa”
Hmmm ki shirya to babe sbd nakusa tafiya idan kina maganar aure ne sbd….
Wani tsananin farin ciki NURU tace”
Yaushe kika fara soyayya Banda labari¿
Wane me sa’ar ne wannan?
Dan wani blushing afia tayi tana kallon NURUn kafin ta miqe ta nufi toilet tana cewa”
Zanfada Miki komai kinsani Amma saina hutu yau da daddare akwai fira.
Murmushi kawai tayi tana cewa”
To ahuta lafiya Bari naje na saka hannu a abincin yau abincin dakukafi so za’ayi.
[ad_2]