UBAYD MALEEK 51

51_*Sai dare suka samu kansu a dakin afia din ma suka kwana bayan sun kwanta
Afia ta fuskanci NURUn ta sauke ajiyar zuciya da numfashi ahankali tafara cewa”
NURU mum Dina tasamu matsalar juyewar Rabin Kai dayake Dan tashi wasu lokutan idan tana tuno abinda daya faru na wannan al’amarin.
‘dan shiru tayi tana sake juya al’amarin cikin ranta ta bude Baki tacigaba da cewa”
NURU mum ta rokeni alfarmar na amince na auri Imran sbd nuna sha’awarsa da yayi ga aure Dan samun cikakkiyar nutsuwar Bata kulawa shine ta nuna sha’awarta
nason auren Hadi a tsakaninmu idan har dad Dina ya amince,
Na zauna nayi nazarin maganarta NURU Nima inason kasancewa tareda ita Dan samun lafiyarta Dan Haka na amince da maganar auren saidai bansaniba ko hakan
danayi nayi daidai kokuwa?….
Ajiyar zuciya ahankali NURU tasaki tana kallon afian cikin tsananin tausayinta da qaunarta sbd a rayuwa tasamu gata da dukiya da kyakkyawan asali da ilimi
da komaima na rayuwa Allah yabata Amma ta bangaren mahaifiyarta ta hadu da jarabawa me qarfi wadda gashi dai daga karshe tayi sacrificing rayuwarta kacokan
akan auren Hadi sbd neman lafiya da kawo sauyi a rayuwar uwarta Wanda hakan yaqarawa NURUn ganin girman afian fiyeda koyaushe sbd tabbas tsakaninta da Allah
takeso da kaunar mahaifiyarta komai halayenta kuwa.
Cikowa idanuwansu duk su biyun sukai da hawaye NURU tace”
Ina Miki fatan kyakkyawar nasara arayuwa fiyeda kowa afia,
Allah ya dasa Jin Dadi da kwanciyar hankali tareda soyayya me girma acikin wannan auren Kuma Inshallah dad dinku ma bazaiqi hakan ba sbd burinsa dama akanki
karatunki ne Kuma kin kammala Dan Haka burinsa na gaba akanki bazai wuce aurenki ba.
Ahankali ta furta”
Thank you NURU.
Murmushi tasaki tana dafa hannunta ta girgiza Mata Kai.
Washe gari a washe suka tashi kowa da nasa farin cikin sbd takardunsu dasuka fito Kai tsaye tare data aikinsu
Murna da farin ciki a ranar ma Saida sukai partynsu cikin Palo wannan karon afia harda rawa Tasha
Farhat da itama farin cikin ganinsu cikin farin ciki duk ya lullubeta itama tasha rawarta duk da Bata iyaba
Saiga Imran yakira afia din vcall ta zauna sunayi tana gyara gashinta data sauyawa kala daga baqi zuwa dark brown suka fara fira sama sama wadda yawanci
idone yake kafe dasu sbd wasu halayenta da kyakkyawar kamilalliyar fuskarta dasuka fara saka Masa Sonta.
Mum dinta yafita yakaiwa wayar suka hau murna mum dinta na cewa”
My baby I love Allah ya albarkaci rayuwarku duka.
Amin ta amsa tareda janyo NURU dake can gefe tana waya da Alama duk wanda take wayar dashi yanada mahimmanci a rayuwarta ta kara Mata wayar tana cewa”
Mum ki gaisa da NURU ki tayata murna itama.
Kallon kallo sukayiwa junansu tareda yin tsit na wasu sakanni kafin NURU ta Dan ago tana kakalo murmushi cikin nutsuwa tace”
Ina wuni?
Ya gida?
Ajiyar zuciya tareda numfashi lailah tasaki kafin ta kalli NURUn cikin nutsuwa tace”
Congrats to you.
Thank you.
Sake kallonta lailah tayi tace”
Kiyi hkr da duk abinda yafaru abaya Ina fatan Zaki yafemun komai ya wuce?
Murmushi NURU tasaki tana girgiza Kai a natse tace”
Yariga yawuce na Dade da yafe Miki sbd girma da darajarda afia take dashi a zuciyata.
Nagode sosai” lailan tafada tana sake murmushin daya qarawa kyakkyawar fuskarta kyau ta Dora da cewa”
Ina gaida farhat.
Jawo farhat NURUn tayi tana cewa”
Sweetie zo ga mum dinki ki gaisheta.
Zama farhat tayi tana karban wayan fuskarta daukeda farin ciki sbd yanzu tafara sakewa da mum din tasu sbd ta sauya sosai yanzu har cikin ranta takeson
yayan nata ita Kuma farhat dama tsorone yasata take shakkar kusantar lailan.
Har Imran suka gaisa dashi kafin NURU ta miqe Takoma ga tata wayar datakeyi da Bata oga kwata kwatan Wanda duk wayar datayi da lailah da gaisawa datai da
Imran duk yanaji Kuma shima hakan yasashi farin ciki ganin atlast dai afia tasamu soyayyar mahaifiyarta dataketa kwadayi tun tasowarta.
Da daddare sbd gajiya tunda suka kwanta Basu farka ba sai qarfe takwas na safe suka miqe cikin sauri sukai sallah kowa yafara Shirin fita aiki musamman afia
datafi NURU buqatan fita da wuri sbd yanayin aikin nasu ba daya ba.
Cikin ikon Allah kowaccensu tafara aikinta cikin aminci da kwanciyar hankali har sun Dan fara sabawa cikin kwanaki kadan.
Yau NURU ce tajasu suka fita tare suka biya ta ajiye afia asibiti kafin ta wuce gurin aikinta tana sake trying numbern MALEEK dabata shiga tun safe rabonta
dashi tun jiya cikin Daren dasukai vcall.
Tunanin rashin samunsa yasakar Mata ciwon Kai da damuwa qarshe Bata Bari yamma tayi sosaiba ta tattara ta baro office din harta Kama hanyar zuwa gida ta
fasa ta nufi asibiti gurin afia sbd tayita kiranta tafada Mata zata wuce gida idan tagama takira zata Aiko Edward yazo ya dauketa Amma afian Kuma Bata dauki
wayarba shiyasa Mata biyawa asibitin Dole tana sakin Dan qaramin tsaki sbd kanta dake tsananin sarawa
Tana yin parking cikin asibitin saidata dakata cikin motar ta sauke ajiyar zuciya da numfashi sbd yanzu Kam kaman hadda jiri tana gani Haka ta daure ta fito
sanyeda shades sbd Rana ta nufi ciki.
Direct hanyar office din dazata samu afia wato office din Dr Damien ta nufa saidai kafin ta qarasa tana daf da Isa ta dakata sbd wani jiri daya dibeta tayi
gefe zata Fadi afia data hangota zuwa ta taso tana kawowa ta tareta cikeda mamaki da ‘yar damuwa tana kallonta tace”
Lafiyanki kuwa???
Gyara tsayuwa NURUn ke kokarin Yi tana Dan dafe goshinta ahankali tace”
Bansaniba kawai ciwon Kaine yake damuna yanzu Kuma Kamar karna baro office jiri yafara kamani Ina ganin stress ne da rashin bacci.
Kallonta afia keyi da kyau kafin ta gangaro da idanuwanta zuwa kirjin NURUn ta kalla tasake maida idanuwanta kan fatar hannuwan NURUn saitaga kaman Bata
gani sosai ta kalli NURUn tana cewa”
Bana tunanin stress ne kadai muje nadubaki mugani sbd jiri matsala ne zai iya jefar dakai inda zaka halaka kanka.
Suna Shiga office din Dr Damien ta zaunar da NURUn tana juyawa ta dauko ruwa takawo Mata ta Bata Tasha ta durqusa gabanta tana cewa”
Muji pulse dinki.
Bata hannunta tayi ta riqe tana Jin pulse din NURUn tayi shiru zuciyarta na bugawa
Duk Bata yarda ba ta juya da ita kan gadon scanning din dake office din Dr Damien din NURU ta kwanta tana gyara Mata kafafunta.
Tana Dora Mata abin scanning din take cikin jikin NURUn ya bayyana baro baro ta ajiye abin tana kallon NURU da cikakken mamaki da tsoro harma da shakku da
firgici duka
Bakinta na rawa Kai tsaye ta fuxgo kalmar cikin tsananin mamaki tace”
NURU you are 7weeks pregnant.
Da sauri NURU ta kalleta tana saukowa daga gadon tana goge jikinta da tissue ta Dora hannunta kan cikinta cikin son tabbatarwa tace”
Pregnant???
Ni¿
Wani irin Murmushin farin cikin da Bata taba tsammanin yiba ta sake dafe cikin tana dagowa ta kalli afia datai mutuwar tsaye tana kallonta cikin mugun
mamakin da batasan lokacinda bakinta ya furta”
Dad ne???
Sai alokacin kunyar afia din takama NURU ta Dan takaita farin cikinta tana kallonta ta daga Mata Kai ahankali tana cewa”
Yes wannan qaninki ne afia.
Wani yawun sabon mamaki afia ta hadiye tana sake dulmiya cikin tunani da tsananin mamaki alokaci daya Kuma hadda kunya tana kamata
Daga ita har NURUn sai suka samu kansu da kunyar juna afian tayi saurin juyawa tana zaro takardar scanning din da batama Gama dubawa ta miqawa NURUn ba