UBAYD MALEEK Page 61 to 70

Bata Jima da kwanciyarba bacci ya dauketa Bata farka ba sai bayan asuba har gari yafara haske ta tashi tana miqa ahankali ta wuce toilet tayo brush da alwala tafito ta tada sallah.
Bayan tagama ta miqe ta nufa dakin farhat ta tada ita tayi sallah kafin tafara Mata Shirin makaranta suka Gama ta fito ta nufa kicin ta hada Mata breakfast dinta sukaci tare kafin aka tafi Kai farhat din school itakuma takomawarta daki ta kwanta ta shige bargo ta Dora sabon bacci cikin kwanciyar hankali.
Har Rana tayi Fana na aikin abincin safen aikin yaki karewa sbd kalolin abincin da lailah tasaka a daddafa din Wanda tasaba idan zataci abinci tafison ayisu kalolo daban daban sbd taci Wanda taga tanada raayinshi sukuma yanzu sun Saba aikin abincin gidan akan kaida akeyinsa tunda NURU tafara Aiko a kicin din gashi tun bayan tafiyar maleek NURU ta cire hannunta a aikin abincin iyakacinta ci idan anyi kamar kowa.
Koda ta farka ta bude idanuwanta taga afia zaune a dakin tanashan Cocoa Krispies da Madara ta mamaki take kallonta tana tashi zaune tace”
Afia yanzu da Rana kike Shan Krispies nagama bakyashansa be damekiba.
Kallon NURU afian tayi tana Kai spoon bakinta tace”
Yunwa nakeji ne sosai kodana tashi kaman naci Rami acikina sbd jiya da daddare banwani ci abinci ba juice kawai nasha bayan hakama ace haryanzu a gidan Nan ba’a Gama breakfast ba sai kace wasu celebrities dakecin abinci akan lokacinda suke zabarwa kansu bazan iya jiraba.
Murmushi NURU tayi tana cewa”
To kodai fana batada lafiya ne da aikin yakaita haryanzu?
Pass 11 fa.
Sanin dalilin hakan yasa afia batace komaiba taci gaba dashan abindake gabanta tana cewa idan nagama asibiti zanje Nanda 4 days zamu fara zuwa session training dinmu yaushe ne naku?
Tana saukowa gado ta nufi mirror tana cewa”
Namu sai next week Nanda kusan 10 days ma Amma Nima may b kwanakin Nan nafara lekawa court din.
Toilet ta nufa tashige tana cewa idan kinfita zanmiki texting din sunan wani littafi kizomin dashi idan Zaki dawo.
Wanka tayi tana fitowa daureda towel tana goge kanta da ruwa yadan jiqa ta alamar afia din ta fita ta nufi mirror kenan zata zauna aka shigo dakin ta Bata waiwayoba ta cikin madubin taga lailah wadda takusa hadiyar zuciya ganin NURUn a Haka sbd fatarta dake wani irin daukan ido sbd zamanta fresh ta kanne tareda dan yamutsa fuska ta kalli cikin dakin taga afia Bata Nan ta maido ta kallonta kan NURU dake abinda ke gabanta tace”
Karkicemin anan dakin kuke zama tareda afia?
Waiwayowa NURU tayi ta kalleta sai tace mata”
Barka da shigowa”tayi skipping wancan tambayar tana kokarin dauko Kaya tasaka ajikinta.
Sake kallonta lailah tayi tana cewa”
Wane irin toshewar Kai ne zaisa ki zauna a dakin AFIA bayan dakunan dake gidan Nan gasucan kusa Dana Sarah Amma kinzo nan kin gwamutsa ta Yaya mutum biyu zasu zauna daki daya a matse wani na shaqan numfashin wani wannan masifa ne cuta na shigowa ciki.
Wannan karon tsayawa NURU tayi kallonta sbd tasamu fahimtar me mum dinsu afian ke nufi Dan dai ita abin yafara gundurarta Matar tacika tsirfa.
Fara hasala da kallon da NURU ke Mata Kamar wawuya lailah tayi tace”
Ba’a kallo Haka idan Ina magana ba sa’arki ke magana ba Matar uban gidankice ke mgn.
Hakan data fada yasa NURU kallonta gabaki daya saidai har lokacin Bata ce komaiba kafin ta juya ta dauki kayanta tafara sanyawa lailah taqara harzuka sbd ganin Kamar NURUn ta maidata hauka kawai takeyi saita dauki towel din afia ta riqo hannun NURUn dashi tajawota ta fito da ita dakin tasawa dakin key ta zare ta kalli NURUn tana Dan yamutsa fuska tace”
Next time idan Ina mgn saiki saurareni da kyau,
Kije dakunan dake kusadana Sarah ki dauki daya wannan banason tarkace ko gwamutsetse atareda yarana ciwo zai iya shiga.
Wucewa tayi tabar NURU a tsaye daga ita sai towel tayi shiru batareda tace komaiba har lokacin sai kawai ta juya ta nufi dakin farhat tashige Allah yasa tanada wasu Kaya adakin na farhat saita Sanya duk Dana shan iska ne saita fito taje kicin ta dauko drink da biscuits tadawo daki taci tayi sallah ta haye gadon dakin tana juya wayarta tanason kiran jekadi Amma saita fasa ta ajiye wayar.
Sai yamma afia tadawo ta tararda dokar mum dinta ta girgiza matuqar gaske ta kalli mum din zatayi magana mum din tayi Mata wani kallo tana numa Mata kofa sbd batason dogon zance bare hayaniya.
Koda afia ta fito dakin farhat ta nufa Kai tsaye sbd tasan NURUn na can tana shiga ta taddasu zaune kan kujera suna game da farhat hankalinsu kwance suna dariyarsu.
Wani iri taji na rashin Jin Dadin abinda mum dinta tayi Amma bazata iya take maganartaba sbd duk yanda take kaunar NURU mum dinta mum dintace saita kasa shigowa ta juya zata wuce NURU data lura da ita kalleta tace”
Charger na kawai nake buqata a dakin sai laptop Dina.
Tsayawa afia tayi tareda juyowa ta kalli NURUn taga ba damuwar komai akan fuskarta ta dake itama tace”
Ok zan Aiko mum Sarah takawo miki.”tajuya ta tafi tabar gurin suka cigaba da abinda sukeyi zuciyar NURUn a dake Taki Bari abinda takeji ya rusata.
Koda dare yayi daqyar NURU ta iya rintsawa sbd dokokin lailan sunfara tsauri sbd ko dining din suna Gama cin abinci aka rufesa
Mum Sarah duk hankalinta ya tashi NURUn ta nuna Mata bakomai kadata damu Takoma daki ta kwanta.
Washe gari bayan tafiyar farhat school ma haka tashiga wani sabon cin zarafin ta daure dai Bata cewa komai bare ta tanka qarshe dai futa tayi taje restaurant taci abinci dagacan tace driver ya wuce da ita wani guri acan ta wuni sai qarfe bakwai tadawo gidan tana dawowa ta shige sbd komai na gidan da doka da iko sundawo qarqashin Lailah tadawo da duk qaidojinta da kaf masu aikin suka Santa dasu cikin kwana biyu ta dawo LAILAH MALEEK dinta Dan kuwa tani kowa yasake shiga taitayinsa.
NURU kuwa tsananin yafara Mata yawa Dan kuwa ko ruwan gidan Idan bana toilet ba batada ikon ganinsu bare tabawa Kullum tana daki idan taji yunwa ta fita taje taci abincinta qarshe dai abin duniya ya isheta sbd cin zarafi da ikon lailah yayi yawa Dan yanzu drivernma ta hanashi sake daukan NURU Dan Haka kwana biyu tana daki ga ciwon Mara tun jiya daya sakota gaba sai kawai ta sayi ticket din komawa gizah ta waya.
Tana kwance ciwon mararta yafara tsananta Mata ta tashi zaune riga da wandon baccin safene a jikinta qananu tun na safe Bata tashi tacireba tana dungule cikin gashi yau weekend ne farhat na gida duk taqara hanata sakat da hayaniyarta shiyasa duk Bata cikin nutsuwarta.
Tashi zaune tayi ta kalli farhat tace”
Farhat kije kifadawa mum Sarah takawomin tea me lemon.
Tashi farhat din tayi ta fita da gudu taje tafadawa mum Sarah ta jira Dan agama su taho dashi tana Taya mum Sarah fira.
Mum Sarah duk hankalinta ba kwanceba ta hadawa NURUn tea din tareda sabon cupcakes datayi yau da safen ta hado Mata a qaramin tray ta miqawa farhat din tana cewa”
Farhat ki riqe da kyau kije ki kaiwa aunt dinki kafin mum dinki tafito ko.
Karna farhat tayi ta fito tana tafiya ahankali sbd kada ya zube ta nufi hanyar Palo zuwa dakinta
tana kaiwa tsakiyar Palo sukai kicibis da mum dinta tafito cikin shigar Kuwait gown tana kamshi fuskarta taji kwalliyarta kamar ko yaushe sirrin kyau sai fita yake a fuskar.