UKUBAR KISHIYATA Page 41 to 50 (The End)

Karb’a yayi tare da d’aure ta a jikin kujeran.
Hannu yasa a aljihun wandon shi ya fito da gum ya manne mata baki dashi.
Durkusawa yayi daidai fuskarta yana murmushi yace…”ni bawan ki ne da zaki ce kin bani ajiyar irin wannan kud’in kuma kice in dawo miki dasu?harda wai sai kin dawo zaki bani rabona?hmmmm gaskiya kin raina min wayo ke da baki kare amanan mijinki ba har kike zaton wani zai kare miki amana?kinyi kuskure babba Lateefa cos tunda muke dake ban taba sonki ba koda na second 1 ba.look at this”yace yana nuna mata kud’in da ido.
Ya cigaba…”sune dalilin da yasa muke tare,na da kuma sabida Kore sha’awata nake tare dake.but I regret every second I spent with u”ya k’arasa yana huci.
Dariya Aina’u ta sheke dashi harda rike ciki tace…”kasan me?wai ni ta bawa blank check akan in cire kud’i,dakikiya kawai saboda duk zaman da mukayi dake Lateefa ban tab’a sonki da alkhairi ba ,wajan boka da shawarwari da nake taimaka mini dasu Salees ne yake tilasta min inyi dan Mu cimma burin mu,but Lateefa i terribly hate u”.
Tayi kaki ta tofa mata a fuska.
Rintse idonta tayi da karfi saboda wani rad’adi da take ji a k’asan zuciyarta da take ji kaman ya fashe.
Meye zata iya yi musu balle taji sauki a ranta?
Babu shine amsar da ta bawa kan ta sabida tasan sun gama cutarta a rayuwa kuma gata a d’aure.
Saukar lafiyayyar mari taji shiya dawo da ita hayyacinta.
Salees tagani yana nunata da yatsa yace…ni zaki rainawa hankali INA magana kina jina?”
K’aramar jakan ya jawo gabanta yace…”ga rabonki sweetheart sai dai nake ganin kaman d’aukan zaizo miki da matsala,let me call wanda zai taya ki d’auka kin san bana son inga kina wahala”.
Wayar ta ya dauka ya fara scrolling yana neman Wanda zai kira.
Yana zuwa kan sunan da yake nema ya kece da dariyar mugunta tare da nuna mata screen d’in wayar.
Sunan da ta gani ne ya k’ara jefata cikin tashin hankali da ya d’ara na yanzu.
Kai ta fara girgiza mishi hawayenta na k’ara k’aruwa.
Shafa gefen fuskanta yayi yana murmushi yace…” Haba Babyna kar ki d’aga hankalinki just dakon kud’inki zai mini kin gane?”
Tana gani ya danna k’iran number.
Fizge-fizge ta fara ko zata iya kunce d’aurin da yayi mata amma ko motsin kirki ta kasa yi.
????????????????????????
*UKUBAR KISHIYATA*
????????????????????????
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*_~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~_*
*part forty nine*
Al’ameen yana rik’e da Ameera da take ta k’wara amai kaman ranta ya fita.
Sannu yake ta jero mata kuma at d same time yana ta masifan shi…” Dama saida na hana ki zuwa d’akin nan amma kika nace ke sai kin kai mata breakfast, ita yarinya ce da sai an kai mata?gashi kin jawowa kanki aman dole.wannan warin jikinta dana d’akin nata zai iya kisa,kinyi sa’a da kika tsaya a amai”.
Ameera dai tana jinshi ba tace komai ba saboda aman yaci karfinta .
Da k’yar ta samu ya tsaya ta kuskure bakinta tare da wanke fuskarta ta dawo kan kujera ta zauna tana maida numfashi.
Shima zama yayi a kusa da ita yana yi mata sannu.
Ringing d’in wayar shi da yaji yasa ya tashi zuwa kan center table inda ya ajiye wayoyin shi.
Sunan Lateefa da ya gani yana yawo akan screen d’in wayan yasa yaji kamar kar yayi receiving saboda yanzu babu wanda ya tsana kaman ita ga sabon al’ada da ta samu na fita da shiga a duk lokacin da taga dama ba tare da izinin shi ba.
Saida k’iran ya kusan tsinkewa sannan ya daure ya d’aga.
Maimakon yaji muryarta sai yaji murya wani namiji yace…. “Alhaji Al’ameen mudassir mijin Lateefa ko?”
Da k’yar ya bud’i baki ya amsa da…”eh nine meye ya kawo wayar mata ta hannunka?”
Dariya ya kece dashi sai da yayi mai isar sa sannan yace….matarka ko matar mu?”
Tsawa Al’ameen ya daka mishi wanda yaja hankalin Ameera gare shi yace…”bana son zancen banza waye ne kai?”
Salees yace…” Easy man stop shouting yanzu zaka ce baka sanni ba?sau nawa kake zuwa ka same ni a gidanka koda yake raina maka hankali take tace maka no d’an uwanta ne,ga files da kake saka hannu ana kawo min.no need of explanation tunda kasan wannan wayar matar kace yanzu haka tana (prince hotel)room number 35 wannan d’akin matarka tana rik’e da shi fiye da 15years.u can come and see for urself saboda ka tabbatar da abinda na fad’a maka in kaki kuma kayi zamanka,maybe zakayi mamakin dalilin da yasa nake fad’a maka haka ko?ta gama yi min amfani shiyasa”.yana gama fad’an abinda yayi niyya ya katse wayan yana kallon Lateefa fuskar shi d’auke da murmushi yace….
” mijinki yana nan zuwa ya d’auke ki,mu zamu tafi sai wata rana.
Juyowa yayi wajan Aina’u yace mik’o min abin muyi mata suprice na 3.
Wata sharb’eb’iyar wuk’a Aina’u ta ciro a cikin hand bag d’inta ta mik’awa salees.
Karb’a yayi yana jujjuyawa daidai fuskan Lateefa wacce tuni tayi suman zaune dan hawayen ma bata san lokacin da suka kafe ba.
Kan wuyanta ya d’ora yana dariya yace…”am sorry Babyna”.
Rude idonta tayi tana jiran mutuwarta .
Hannunta na dama ya kama daidai wajan yatsunta 5 yace…”bazan kashe ki ba amma zan miki abinda zaki rinka tunawa dani always “.
Sare hannun yaji wanda nan da nan hannun ya guntule ya fara tsalle a cikin parlour ga jini yana ta tarwatsuwa a parlour.
Kafa yasa ya danne gutun hannun daya guntule har ran ya fita.
Ya juya yana kallon Aina’u yace…” muje sweetheart”.
K’wasan duka tarkacen su sukayi gaba suka bar mata k’aramar jakan kud’in.
Ita kuwa Lateefa tun daga nan bata san inda take ba sakaman yawan jini dake ta zuba a jikinta.
Ameera ce durkushe a gaban mijinta tana kallon da ya rine yayi ja kamar gauta..
Hankalinta ne ya tashi saboda bata tab’a ganin shi cikin irin wannan yanayin ba.
Cikin Sanyin murya ta fara tambayan shi meya faru?
Ya dafe goshin shi da hannayen shi duka 2 yana kallon kasa.
Ya d’ago yana kallonta,itama idonta taf da hawaye yace…”wani ne ya k’irani yake min maganan banza akan Lateefa har yake cewa in ban yarda ba inje in gani da idona”.
“Maganan banza?wani irin maganan ne haka?” Ameera ta tambaya da alamun tsoro akan fuskarta.
Mik’ewa yayi zumbur ba tare da ya bata amsan tambayarta ba yasa kai ya fita da saurinsa.
Da kallo ta bishi tana addu’an Allah yasa lafiya.
Yana fitowa compound gidan Bala driver ya taso yana mishi magana ko kallan shi baiyi ba balle ya tanka.
Mota ya shiga ya fige ta da karfin tsiya ya fita a gidan.
Driving yake kaman zai tashi sama zuciyar shi kuwa a cunkushe take duk da yana shakkar abinda yaji a Waya amma wani bangare na zuciyar shi kuma ta yarda bisa la’akari da rashin kulawa da yake samu daga gare ta.
Cikin lokaci k’ankani ya iso hotel d’in ya fito a motan bayan yayi parking a parking space na hotel d’in.
Bugun zuciyar shi sai k’aruwa take a lokacin da yake duba numbers na d’akunan har ya kawo room number 35.
Cak ya tsaya yana fargaban bud’ewa dan bai San abinda idon shi zai gane mishi ba.
Haka ya daure ya kai hannu kan murfin k’ofan ya murd’a ya jiya a bud’e.