MAKAUNIYAR KADDARA 49

*Page 49*
………..Koda suka wayi gari lafiya ma da ƴan zuwa tabbatar da dawowar Zinneerah suka tashi, dan babu kunya mata keta shigowa da ƴammata da yara. Duk da abinda ya faru a baya yana a zukatansu kwarjini da cikar kamalar Zinneerah a yanzu ya hana bakinsu aibantata, dan dama wasu suna zuwane dalilin wancan abun daya faru bawai dan Zinneerah ta kasance zinari ba.
Itako duk da kasancewar ta miskila haka taita dauriyar musu murmushi da nuna kulawarta garesu babu wani wulaƙanci ko yarfi. A ranarma dai duk yanda taso samun kanta bai yuwuba, haka suka yini amsar baƙi da ƴan tsirku har yamma.
A ɓangaren Inna kuwa a ranar taso bazama wajen malamanta baba daya gama karantarta tsaf ya hanata fita, yama kafa mata sharaɗin har Zinneerah tabar Danya idan ta leƙa waje a bakin aurenta. Wannan al’amari ya mata ciwo, ta dinga zazzaga masifa da jidali masu shigowa na mata dariya. Yaran nata da su Gwaggo Maryama kuwa babu wanda yabi takanta. Garama Zinneerah takance “Kiyi haƙuri Inna”. Aiko wannan kalmar haƙuri na mata zafi a rai fiye da masu mata shiru. Itako Zinneerah har cikin ranta batajin daɗin ganin yanda Innar ta koma kamar wata zararriya.
Da daddare aka buɗe mata kayan lefenta ta gani ita dasu Gwaggo Maryama, abin ya bata mamaki sosai, ta kuma jinjina ƙoƙarin su hajiya iya. Suna gama ganin kaya Hajiya Falmata ta jata ɗakin da tasa aka ware musu ta ɗora aikinta daga inda ta tsaya gudun karsu cigaba da cinye lokacin a banza.
Washe gari tun kusan gabannin azhar aka fara karɓar baƙuncin dangin Mmn Sadiq na ɗan-musa a danya. Hakan ya ƙara tabbatarma Inna lallai bikin na gaskene ba wasa ba. Sai kawai ta zauna ta fara kuka rirus ƴaƴanta na lallashinta. Tinene kuwa dariya taita kwasa dan itako ko’a jikinta. Tama nanema Zinneerah ne kamar basuke zuba faɗaba a baya.
Bayan la’asar itama mmn sadiq ɗin sai gata da tawagar ƴan kano. Gida ko ya sake haukacewa da murna. Ita da Inna suka shiga kallon kallo. Mmn sadiq na ganin tsufan inna da komawarta kamar wata zararriya. Inna na kallon komawar mmn sadiq ɗanya shataf ga ƙyau dajin daɗi da kwanciyar hankali tattare da ita.
Cikin rashin damuwa da yanda Innar ta tarbesu Mmn sadiq tashiga gaisheta. Banza Inna tai mata dan idan tai magana to lallai bazata zama mai daɗiba. Fitar mara daɗin kuma shine zai zama tabbatar sharaɗin baba a gareta. Haka kawai yasata zaɓar yin shiru, amma tana ƙullama zuciyarta abinda zata aikata musu wanda sai sunyi nadamar dawowa cikin rayuwarta su dukansu.
Duk wani abinda mmn sadiq zata iya buƙata na abincin da ƴan uwanta zasuci da abinta tazo, hakan yasa suna isowa babu jimawa ta bada aka saya mata icce mai yawa, ta kuma ware kuɗin ruwa. Duk da abin yama baba ciwo baice mata komaiba, dan ganinta kawai sai da ya sakashi share ƙwalla, yanason Hauwa’u matuƙa, ƙaddarar iyakar zamace kawai ta shiga tsakanin su da sharrin Inna.
Tuni Zinneerah ta shige cikin dangin mahaifiyarta da suka nuna damuwarsu akanyi watsi da lamarinta sunata neman afuwarta. Ita dai nata murmushi ne da tabbatar musu babu damuwa. Daga haka aka shiga shagalin biki.
Batare da Zinneerah tasan da zuwan su Bahijja ba sai gasu suma kusan biyar na yamma driver ya kawosu, taji daɗi matuƙa dan sune dai ƙawayen dama. Garama isowar ƴan ɗan musa da sakina yasa taɗan samu ƙawaye, Tinene nata ɗari-ɗarin shiga cikinsu Zinneerah ta jawota tare da gabatar musu da ita.
Sukam babu ruwansu basusan wulakanta mutaneba, hankali kwance suka amsheta babu wani nuna ƙyama gareta ko makamancin hakan.
*KANO*
A kano ma dai gidan hajiya iya ya ɗauki haramar dangi da abokan arziƙi, dan dole AK yabar gidanma gaba ɗaya ya koma nashi dayasha gyara inda za’a saka amarya dama Uwargidan kanta. Dan ya ƙullama Farah batare data san dawan garinba tanacan katsina suna jiran tsammani ita dasu Mammah.
Ƙiri-ƙiri AK yace bai yarda da wata dinner da shirme ba. Hajiya iya tasan kishinsa na tsiya, amma batai zaton zai nuna akan Zinneerah da aka aura masa babu neman shawara ba, dan duk da bikin Farah Mammah ta nuna musu iko akansa haka ya hana yin kowacce bidi’a. Ba kuma komai yasa hakaba sai kishi, dan AK nada matuƙar kishi gaskiya abin a jininsu yake kam da gaske.
Amma duk da haka dai an shirya walima da liyafar cin abincin rana, dan Baffah yace bazasuyi biki lami ba, Khalipha kuma da su Huzaifa suka shirya fati iyakar su mazan kawai dan gayyato abokan AK na kasuwa dana makaranta sukai sosai batare daya sani ba.
Abin mamaki kuma sai ga Uncle Ahmad da iyalansa babu zato babu tsammani, sai baffah da AK ne kawai suka san da zuwansu. A take gidan ya ƙara harmutsewa da farin ciki, babu wanda yabi takan matarsa daketa faman yatsine-yatsine, ƴaƴanshi kuwa dake a ɗarare saboda rashin sanin dangi AK ya musu jan ido tunda shi ba baƙonsu bane. Aiko sai gasu sun saki jiki a cikin su Saifudden.
Hajiya iya kuwa duk da haushin uncle Ahmad ɗin da takeji saita daure ta danne komai dake ranta ta tarbesu da farin ciki da ƙewa. Uncle Ahmad ya rungumeta yana hawaye itama tanayin nata. Daga ƙarshe dai su Mommy suka lallashesu akan suyi haƙuri.
*KATSINA*
Ta wajen su Mammah kuwa yau Farah ta haɗa kayanta tunda safe tace zata wuce kano sabida cimata ƙaniya da Mahma tayi a ɓoye a daren jiya, ta kuma nusar da ita inhar bata daina biyema Mammah da aunty Zakiyya ba to wlhy ƙwaɓarta na gab dayin ruwa. Dan AK zai iya ɗagama mahaifiyarsa ƙafa kodan kasancewarta uwa a garesa amma ita wahala zatasha, ƙarshema ta ƙare da saki idan bata maida hankalinta jikintaba.
Kalmar sakin nan itace ta rikitata tun a daren ta shiga kiran AK amma yaƙi yin picking call ɗinta, daga ƙarshema ya kashe wayan duka. Wannan ruɗanin ya sata shiryawa da farar safiya tace itafa sai kano.
Masifa Mammah da Aunty Zakiyya suka shiga mata akan hakan amma taƙi saurarensu tace suyi haƙuri itadai zataje ƙilama ta samo amsoshin da suke zaman jiran nema ga wanda ke musu bincike. Ba ƙaramin haushi abin ya basuba, musamman ma aunty Zakiyya data nuna har a fuskarta, sai dai tai shiru bata faɗi abinda ke bakintaba saboda wani dalilinta.
Lallaɓa Farah Mammah tasoyi. Ta kamota jikinta cikin lallashi take faɗin, “Haba Farah, kinsan dai komi muke akanki mukeyinsa, bakuma zamuyi abinda zai cuta miki ba. Indai Abdul-Mutallab ne zaiyi fushinsane ya gama ma ya dawo lallaɓaki da kansa. Ni banason ne dangin ubansa su maidaki kamar wata mara gata shiyyasa kikega ina haƙilon nan. Dagani harke taimakon juna mukeyi, banason rasa Abdul-Mutallab a rayuwata, kema kuma nasan bazakiso ki rasashi ba ai. Kuma wannan sakacin namu shi zaisa ya suɓuce mana ɗin dan wannan kakar tasu da Kabeer kansu kawai suka sani, sosuke su rabani da shi”.