NOVELSUncategorized
QANIN MIJI 3

3
Cak kamar ɗaukewar wutar nepa haka fareedah ta dakatar da kukan da take yi ta ɗago tana binsa da wani irin kallo hawaye na cigaba da bin kumatunta, shima itan ya tsare da idanu cikin tsumaye da sauraron abinda za ta ce, domin fareedar tasa ba ta taɓa masa irin wannan kaifaffan kallon haka ba
Murmushin takaici da ya fi kuka ɗaci da ciwo ta masa ta miqe tsaye ta riqe qudunta da yake ɗaya daga cikin makaman yaqinta da hanu ɗaya, abin dariya da haushi sai da fa’eez ya bi qugun da ta riqe da idanunsa sannan ya sake ɗaga idanunsa ya zuba a kan fuskarta, jin ta fara cewa
“fa’eez, ban san me yasa tunaninka ya baka cewa buqatarka a shimfiɗatace kawai haqqin da zan iya yin baqin cikin rasa shi a gurinka ba, duk da cewa shiɗin ginshiqine cikin rayuwar ma’aurata, saidai ni a gurina ba haka abin yake ba, domin lokutanka sun fiye min komai cikin rayuwar aurena, amma ba laifinka bane, laifinane, kuma nayi alqawarin gyara kuskurena da kaina”
Sai da ta sake masa murmushin mugunta da na takaici sannan ta cigaba da cewa
“fa’eez, in har ni ‘yar halak ce, na haramta wa kaina shimfiɗarka tsawon shekaru biyu, bana buqatar sausauci daga gareka, domin ina son in gwada iya qarfin amfani da alfanun da shimfiɗar taka take min, ka sha aiki lafiya”
Ta qarashe da wani murmushin da ya soki zuciyar fa’eez matuqar suka, domin yana matuqar qaunar fareedah a rayuwarshi, babu abin da yake so a duniya bayan iyayensa sama da fareedarsa, shi kanshi ya san son da yake mata ya ninninka nata a baɗininsa, ko a ina yake in ya tuna fareedah tashice mallakinsa sai ya ji wani irin daɗi ya mamaye zuciyarsa, amma yau itace tsaye a gabansa take caccaɓa masa maganganun da suke nuna cewa ba ta damu da shi ba, wacce irin ranace yau da ta zo masa da baqin ciki mai ɗaci a zuciya
Juyawar da yaga tayine ya dawo da shi daga magagin takaicin da ya shiga, musamman tafiyar da take yi tana jujjuya masa qugu kamar da gayya????
Daga waya har laptop ɗin bai san lokacin da ya turesu daga jikinsa ba ya diro daga gadon cikin mahaukacin sauri ya je ya tari gabanta ya tsaya ransa a matuqar ɓace, kallon sama da qasa ta masa ta ɗauke kai ta sake ɗora hanunta a qugu tace cikin muryar da ba wargi “fa’eez ka kauce min a hanya”
A harzuqe yace cikin ɗaga murya
“fareedah ni ne fa’eez?, ni kike kira da fa’eez”?
Bai taɓa ganin bala’in fareedah irin na wannan lokacin ba, dan sai alokacin ya gano ainahin ɓacin ran da ta ɓoye a lokacin da take masa maganganun da ta masa, domin cikin masifa da waina hannu tace
“na ce fa’eez, fa’eez, fa’eez!!!, ba sunanka bane?, kai fa’eezu idan Allah ne yace kar in dinga kiranka da fa’eez sai ka kaini kotun shariar muslunci ta hukuntani, na faɗa na sake faɗa fa’eez”!!!..
Ta qarashe tana wani jijjiga
Baki fa’eez ya buɗe galala yana kallonta, ita ko ta banko masa wata uwar harara ta ɗauke kai
Rufe bakin yayi ya haɗiye wani irin yawu na takaici tare da rintse idanunsa ya buɗesu a kanta still tana tsaye tana jijjiga, daga sama har qasa ya bi jikinta da kallo, sake rintse idanun yayi na wasu seconds sannan ya buɗe ya sake kallonta
Kusa da ita ya matsa ya sanya hanunshi zai riqota ta kauce ta ja da baya, sake yunqurin riqota yayi ta kauce, ganin zata wahalar da shi kawai sai ya mata da gaske ya nufeta ya janyota da qarfi jikinsa ya rungumeta da qarfin gaske yayin da ta fara qoqarin qwacewa amma ina, qarfin ba ɗaya ba, amma duk da haka ba ta daina mutsu mutsun qwacewa ba
Ganin za ta wahalar da su ya sanyashi mata magana a kunne whisperly yace
“pls fareedata ki tsaya ki saurari mijinki, dan Allah, dan son da kike wa annabi muhammad s.a.w…”
Yana faɗin hakan ta daina mutsutsun ta sake fashewa da kuka, janyota yayi suka koma bakin gadon suka zauna ya sake rungumeta tsam a jikinsa yana shafa mata baya da nufin rarrashi
“fareedah me yasa zaki kawo mana matsala muna zamanmu cikin kwanciyar hankali, wallahi na manta ranar da magana ta min zafi a qirjina kamar yadda maganganunki suka min zafi tare da sukan zuciyata”
Cewar fa’eez cikin muryar laluma da neman sulhu tare da share mata hawayen fuskarta
“kai kake cikin kwanciyar hankali, ni hankalina ba a kwance yake ba..”
“saboda me”?
Ya tari numfashinta
“saboda na rasa lokaci da kulawar mijina, tsawon shekaru kuma mijin nawa ya gagara fahimtata”
Ta qarashe da gangarar da wani siririn hawaye a kan kumatunta
Harshenshi ya sanya ya lashe hawaye ya ɗago ya hasketa da rantsattsen murmushi ya sake kwantar da ita a jikinsa yana shafata ya fara magana
“fareedah kece kika gagara fahimtata, kema kin sani bani da wani farinciki sama da ke, kece rayuwar fa’eez gaba ɗaya, ke da K boy, shiyasa na sadaukar da lokacina da rayuwata gurin nemar muku abin da zan inganta muku rayuwarku da shi, duk wata dukiya da na tara mallakarkuce kuma ita nake tattala muku ke da ɗanki, kina tunanin idan baku da muhimmanci a gurina zan iya wannan sadaukarwar?, lokaci fa?, lokacin ma ciki har da na kusantar abinda na fi buqata da so a rayuwata, maman khaleel ɗina?, kin san wace ce ke kuwa?, ni fa ban taɓa ganin macen da ba ta canzawa kullum kamar amarya ba sai fareedata, wallahi babu lafiyayyen namijin da zai iya juriyar da nake yi akan kaiwa da kawowar da kike yi a gabana kuma in danne abinda yake taso min sai waliyin mijinki fa’eez, saboda wani sihirtaccen al’amari da yake tattare da ke wanda ke baki sanshi ba, kuma a hakan nake yaqarsa fata-fata dan nemo muku jin daɗin rayuwa, ashe ba zaki gode min ba”?
Ko ba komai ta ji sanyi a ranta ta dalilin maganganun da ya faɗa mata, dan haka cikin salon kirsar da ta saba masa magana a lokacin soyewa tace
“um..um.., ni dai gaskiya na gode wa Allah kam amma bana ra’ayin wannan sadaukarwar da kayi, ka bamu time ɗinka kawai sauran kuma Allah ya iyar mana”
Qureta yayi da idanu yana murmushi sannan ya lumshe idanu ya buɗe yace
“fareedar fa’eez kenan, ikon Allah, yau kuma da rigima da tawaye aka zo min, toh kin ga mu bar wannan maganar, cinye mana lokaci take yi, bari in ga….”
Ya ɗaga kansa tare da murza sabbabarsa a jikin kan nasa yana tunani, can ya sauke yatsar ya ɗauko wayarsa ya fara dialing wata number
Hello yace bayan an ɗaga kiran, bayan wanda ya kira ɗin ya amsa masa sai ya ɗora da cewa
“maxwell a rushe duk wasu schedules ɗina na gobe, a kai su jibi in Allah ya kaimu, ba zan samu gudanar da komai ba a goben”
“ok sir, an gama, amma akwai……”
“No, nace ba zan samu damar yin komai ba, koma mene ne a sokeshi”
“ok sir, as you wished”
Yawwa yace tare da katse kiran ya kalli fareedah
“An gama madam, gobe ina nan tare da ke a cikin gidan nan, ko falo sai kin min izinin fita, shikenan”?
“ni dai…nidai…., ni fa ba akan gobe kawai nake magana ba, daga goben kenan a sake komawa ‘yar gidan jiya”
Haɗa hannayensa yayi yace
“Dan Allah dan Allah fareedah ki rabu dani a haka, goben ma ba qaramin asara za ku yi a companyn naku ba, ni dai gaskiya nayi iya qoqarina”
Turo baki tayi tai shiru ba tare da tace komai ba
Wani kallo ya mata tare da murmushi sannan cikin tsokana da neman zance yace “da dan mugunta da lafiyata ana kira min shekaru biyu”
Hararan wasa suka yi wa juna yace “toh na qi muguntar, yanzu ma na fasa aikin”
Tashi tayi da sauri tayi hanyar barin ɗakin, da dariya ya rakata yana cewa “za ma ki dawo, in baki dawo ba ma kin san megida da gidansa, zan zo har inda kike”
Ba ta juyo ba tayi ficewarta abinta
***
Daga dukkan alamu dai mutanen naku an ɗan samu daidaito, saboda yanayin da suka kasance a safiyar yau ɗin mai cike da farincikine da annashuwa
Hafeez ya daɗe da tafiya school, su biyu suke cin abincin nasu yayin da tsabar tattalin da fa’eez yake yi wa fareedar tasa a yau abincin ma a baki yake bata, ita kuma ta samu abinda take so sai wani narkewa take yi kamar autar qauye????
Shiko gogan naku mamaki fal ranshi amma haka yake biye mata, dan shi bai ga abin ɗaga hankali a nan ba balle a damu da rashinsa, kasa hakuri yayi yace
“kai… Mummyn khaleel, yanzu ke waɗan nan wasannin sun fiye miki komai?, gaskiya ke yarinyace, ni dai gaskiya…..”
Ta narke fuska za ta bashi amsa kenan suka juyo muryar khaleel da Fa’eez ya tura a ɗaukoshi daga gidan su fareedah yana cewa
“Abby…..!!”
Dukkansu suka juya ga yaron da yake dumfaro gurin da suke kowanne ɗauke da zallar farinciki a fuskarsa
Janye fareedar yayi daga jikinsa ya tashi ya ɗauko khaleel yayi ta juyi da shi sannan ya saukar da shi ya zauna ya ɗorashi a kan cinyarsa ya sumbaceshi cike da qauna yace “gatan Abbynsa me hajiya take baka kayi qato haka”?
Kusa da kunnen Abbyn nasa ya masa raɗa suka kwashe da dariya dukansu, ita ko fareedah kallonsu take cike da sha’awa, dan za ta saka yau cikin kundin tarihinta
“ai kuwa hajiya tayi qoqari, madara zallah, toh mummy kema sai ki shirya, domin ina son K boy ɗina ya kamoni nan da sati” dariya suka qyalqyale da shi yayin da khaleel shima yake tayasu, sai ɓangale baki yake yi abinsa irin na yara, a taqaice dai wannan wuni wunine mai cike da ɗumbin farinciki wa ahalin faeez, domin da yamma tayi ma da kanshi ya fitar da su yawon shaqatawa sai dare suka dawo gidan, shi ko duk yana yin hakan ne a takure dan ya faranta mata, ya kuma ɗauke mata wani kaso cikin nauyin da za ta ji a zuciyarta idan ya sanar da ita tafiyar da zai yi, hmmm toh mu je dai zuwa
**
Kuka take yi sosai yayin da fa’eez yake tsaye kusa da ita cikin shirin barin qasar, hafeez da yake tsaye kusa da su riqe da mr boss ɗin fa’eez, glass ɗinsa ya maqala a idanunsa ya toshesu, kasancewar baqi wuluk ne glass ɗin, ba a iya hango qwayar idanunsa
“haba fareedah, wai me kike son in faɗa mikine, kin kasa fahimtata, tafiyar nan fa iyakarta wata uku, da qyar za ta jani wata huɗu ko biyar, kuma ga waya zamu dinga communicating, ummm.., bayan haka ga hafeez nan zai dinga ɗebe miki kewa, duk abinda kike so ki tambayeshi, baki da buqatar komai, saboda na bar muku kuɗi ko shekara zanyi zan dawo in same saura, toh mene ne kuma bayan hakan, me kike so in miki”?
ISLAM IS MY IDENTITY