FITAR RANA 8

No.8
ACikin sauri tabar wankin ta miƙe tsaye tare da ja da baya tana mai tsura masa fararen idanuwanta tanata kallonshi shima kallonta yakeyi tun daga can nesa yana tahowa cikin takunshi mai sanyi daya gama burgeta.
kyakkwar fuskarshi dauke take da wata iriyar murmushi mai matukar daukar rai,hadadde dan gaye,sumewan tsaye wasime tayi..shikuwa aransa cewa yake..wow ive seen an African queen.”dan kuwa babu abunda yay mugun tafiya da imanin sa sama da shiny luminious dark skin dinta,wanda baiya bukatar ado ko wani kwalliya..he has neva seen a black beauty like this one.
har ya iso gabanta kwakwlnsa bata samu cikakkiyar nitsuwa,kallon junansu kawai suke basu kifta idanunsu.kunya da fargaba duk ya kama zcyar wasime,kyaunsa da gayunsa sosai ya tafi da ita, gashi duk tajiƙe jikinta da ruwa kamar wata yar bola,gayen ya kalleta snn ya kalle cikin bucket dinta,wani murmushi ne ya kufce mishi,miƙa mata hannunshi dayasha ado da diamond wristwach da saphire ring dark red in colour yay..yana murmushi mai taushi cikin murya mai sanyi yace “hey,hello beautiful Angel..,shiru tay tanamai sunkuyar dakanta ƙasa. ganin bata motsa ba ya dauki bukitin kayantan Ya fara jera matasu akan clothline..”..Kyakkyawa baki maganane?kanta ya shafa kadan…ure so damn beautiful. ina mum dinki kika fito cikin sanyin safiyar nan kina wanki?u shud be on ur bed by now!!ina mama?kanta ta sunkuyar kasa sosai muryanta kasa kasa tana jin kunya kunya ahankli tace “tana cikin gida”..yace shine ke kika fito waje?tace ehm “dama wanki nakeyi”
Dan dariya yy yace “I seee”…what a beautiful voice u got,yana furta hakan ta sauƙe broad smiles a bazata..setin zcyrshi ya capke irin”ohh my gosh wat a smile, u will definately kill me kina kasheni fa…kanta ta sauƙe kasa dan kwata kwata ita bata fahimtar meyake cewa sosai da sosai,tsinta kawai takeyi dan ita bawani iya turanci tayi sosai ba dan zamansu a jos ne ma yasatake dan iya gamutsawa kadan kadan but not all the time takeji,saheeb yana murmushi ya aje empty bucket din a ƙasa snn ya dan nuna chest dinshi da yatsa yace”Ahhm! sunana Doc saheeb..ni likita ne..”Kefa beauty?.meye sunanki mai shegen dadin nan?i know ur name most be special.Mayun idanunshi ya zuba akanta yana sauraron ta,dan kadan ta dago kanta tanajin nauyi nauyin shi a kunyace sosai tace “Emm Ni sunana “wasimé…
Murmushi yy yace “wow”yana mai jinjina dadin sunan har cikin zcyarshi yana wani lumshe idanunsa yace “uhm dats so unique!..ke yar uwan Tej ne ko?ive been coming here amma bantaɓa ganinki ba ya akayi hakan to..budan baki tay kamar zata bashi amsa kirjinta ya buga da wani irin ƙarfi a tsorace ta juya ta kalli bayanta taga ashema biltice ke tahowa.
amma abayanta kuma sai taga wani abu kamar inuwar mutum wanda tabbas tasan babu makawa shine.Wani hadiyar yawu tayi abazata dan ta dade kuwa bataganshi ba, atake ta zamto tamkar wata kurma tayi shiru bata ƙara kuma dago idanuwanta sama ba, bilti tana isowa daf suka hau gaisawa da saheeb din dake shi yana da son wasa da raha take ya shiga gaya ma bilti dk yadda sukayi da wasime.
Yace”Bilti dama wannan yarki ce?she is so damn cute…murmushi kawai bilti tay batace mai komi ba tajanye hannun wasime suka tsaya tare da ita agefe itakam tasan gogan na lura dasu kuma zai iyayin ƙorafi akan yanayin da wasimé ta fito, lura da iyayensa sun riga sun dora masa nauyin jagorantar gidan kafin su dawo daga tafyarsu”
..Daga can baya baya taher din ya tsaya,bai ɓata lokcinshi ya iso garesu ba dan baison ma ransa ya ɓaci,kallonsu kawai yake daga can nesa da idanunshi da suka riga suka kankance da masifa, duk abunda suke fada yanaji daga inda yake amma yanayinsa kwata kwata bai nuna hakan ba.
wayarsa yasaka agaba yana latsawa sosai.da kyar ma yake daga idanuwansa sama barema ace ya musu wani kyakkwan kallo.muryan sa ciki ciki kuma a matse yace “guy cmon lets go in,saheeb yace toh am coming”..ya kalli bilti “bari naje ciki pls a cup of coffee.
Cikin sauri bilti ta riko hannun wasime tana kkrin janta ciki,ta amsa masa da cewa ‘toh za’a kawo insha Allahu..gefen fuskan wasimén yadan shafa daxai wuce snn ya wuce din yy ciki,lkcin tej har ya isa bakin kofa da naturenshi na fushi fushi ya bude ya shiga saheeb na biye dashi abaya.
Kallonta bilti tayi snn ta karkada kai “toh Zo mu wuce ciki,kefa bakijin magana wasime ai saida nace miki kidena fitowa wanki anan amma kikayi banza”toh wuce muje ciki. tsadaf tsadaf ta bar jikin tap din bayan ta kulle ,bilti ta cigaba da mata fada sabida sanyi sam Batason ciwonta ya tashi ko wani abu yazo ya sameta,Harta gama surutun Wasimé bata ce mata uffan ba tana famar juya hoton wancan kyakywan mutumin acikin kwayar idanunta,aranta tace dagaji yana da hankli.
Nannauyar ajiyar zcya ne ya kufce mata snn ta wuce bayi tay wanka ta doro alwala tazo ta sauya kaya,riga da zaninta tasaka na abc koriya da fari fari sosai ya mata kyau,kitchen ta nifa ta samu bilti ta kammala musu abun kari.da kallo daya bilti ta bita snn ta mika mata wani abu acikin kofi tace..”zauna acan kisha ruwan zafi ne…inkin gama zaki tayani kai abinci,babu gardama tace toh.akan plastic chair dake kitchen din taxauna takai cup din bakinta slowly,ahnkli tafara shan ruwan zafin har sanda wani zufa ya karyo mata a goshi,kafin nan bilti ta shirya tray na breakfast dauke da tea flask da sauran tarkace
Ta kalli wasime tace,riƙe min jug din toh,karba tay tana cewa toh snn suka fita suka doshi hanyar dakinsan a tare.
A fannin su tej kuwa tun suna hanyar isa room dinshi saheeb yaketa wondering aransa kome aka masa yake wani fushi fushi,suna isa dakin ma ya nemi waje yay kak ya hade rai yaki ya kulasa,”hannu saheeb ya harde yana kallonsa
..”man wats wrong?meye haka kaifa wallhy bakada mutunci Ba azo wajenka bane kacika ma mutum ciki da attitudes”
..to ynzu meye kake wani shasshamin kamshi?
“hannu ya daga masa alaman ya isa. ahankli cikin sassanyar izza ya mike tsaye is enough…
bacin raina ba abunda ya shafeka bane…lets just get down to business menene matsalarka?
Yafadi hakan yana shasshafa wajen gemunsa fuskarsa babu alaman wasa
waje saheeb ya samar makansa ya zauna yana satan kallonsa acikin yanayin son yay dariya,shidai wannan hali na taheer na daure masa kai..mutum sai shegen iyeyi,.ga zurfin cikin tsiya,juyowa yy ya kallesa still yaga bai sake fuskan sa ba.”Man whats wrong, kafadamin mana… wai yanaga ranka a bace ne yau?
Kowani abu ya farune a schl.
Rau Rau da idanunshi yyi
“Saheeb nace babu ruwanka kanaji ko?kaifa gulman ka yake hadani dakai.
“Toh shikenan Its okay na dena.saheeb ya fada yanamai daga hannayensa sama alaman shikenan din ya hakura..ajiyar zucya ya sauƙe snn ya dubesa
“Guy to yane, maganar mu zatayu kuwa?tej im desperate..lallai inason na gano gayen nan da yayima ƙanwata ciki
I want to find him kafin mahaifinmu yaji zancen nan,she is too young to be married,shekarun anisa fa baifi sha shida ba mezataje tayi agidan miji yanzu?,pls pls tej help me find him let me silence this case once nd for all…
…shrugging sholder taheer yay…”ai nafada maka i wll see wat i can do abt it!..kabarmin komi a hannu na amma banga dalilin dazaisa ka zubda ma yarinya cikinta bafa
Kaban haushi wallhi….