WATA TAFIYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA TAFIYAR 12

 ????WATA TAFIYAR????       Story & Written

                By

         Jiddarh Umar

????????????????????????????????

*????✨MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????✨*

https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

 *“`We are the moonlight writers we shine all over the world.“????`* ✍️✍️

بِسم الله الرحمن الرحيم

~~~~~~~????????~~~~~~~

PAID BOOK

                      

               12

Ga mai buƙata zai turo 200 ɗari biyu ta wannan Asusun 2284905309,Hauwa Umar Zenith Bank, 

Sai ki turo shaidar biya ta 08141644865.

Ko Katin Waya.

WANNA LITTAFIN NA KUƊI NE,IN KINSAN BAKI BIYA BA DAN ALLAH KAR KI KARANTA, KUMA KAR KI YI SHARIN PLEASE.

 kan gado ta kwanta dan gaba ɗaya ji take zuciyar ta na mata zafi,lumshe ido ta yi tana ƙara lafewa a cikin katifa,a hankali maganganun matar nan yake dawo mata wacce ko sunan ta bata sani ba,a hankali ta ji gudun zuciyar ta na ƙaruwa yayin da tsoro ke samun gurbin zama a zuciyar ta,tana matukar tsoron ya kasance maganar matar gaskiya ne, amma kuma ai tana da tunani,kuma ya kamata ta yi tunani akan wani abu game da wannan lamarin,ita na farko bata san ƴan uwan shi ba,bare iyayen shi,ko wasu na shi,kai ita ko sunan shi bata sani ba,ko kafin a juya lamarin Aure lokacin yana kan ƙanin shi,wato Haris,yauwa ta tuno, ta tuna Haris ya taɓa bata waya,da sauri ta sauko daga kan gado,Akwatin da aka kawo mata daga gida ta buɗe,cikin sa’a kuwa sai gashi taga waya har da abin caji a ciki,murmushi ta ɗan yi dan ta tabbatar da wannan aikin Nanne ne,kuna wayar ta yi,tana gama kawo wa ta kira number Baba Mudansir,dan ta san in yana gida zan ba Nanne dan ita bata da waya,jin ana sallama yasa da sauri ta amsa”Baba na ina wani”

Wani irin tsanyi ne ya ziyarci zuciyar shi,domin tun randa suka kawo ta gidan hankalin shi ya kasa kwaciya,dan baya samun number ta sai yanzun da ta kira”Fettel Nanne sai yanzun aka tuna da mu”

Dariya ne ya kucce mata mai haɗa da wani tsiririn hawayen farin ciki “Baba na na yi kewar ka”

“Muma munji kewar Asma’u,to ya kike ƴar Baba? 

” Lafiya klau,ya su Nanne,da kowa da kowa? 

“Duk suna lafiya, ya mai gidan ki? 

Ɗan shiru ta yi,dan ji ta yi kamar ta faɗa mai halin da take ciki,sai kuma wani tunani ya faɗo mata,ta tabbatar da idan har Baba Mudansir yasan bata ga mijinta ba har yanzun to za a iya samun matsala da shi,” Yana nan lafiya Baba,ɗan bai ma daɗe da fita ba”tana iya jiyo lokacin da ya sauke ajiyar zuciya”to Allah ya kara muku haƙuri da juna,ai ta haƙuri kin ji Asma’u ”

Hawayen ta share”to Baba”

“Kar ki damu yanzun ina kasuwa da zaran na koma gida zan haɗa ki da Nanne”

“To Baba” daga nan suka ajiye wayar.

Juyowar da zata yi ne kawai taga Mama tsaye a kanta,ihu ta yi tana sake wayar a ƙasa dan ba ƙaramin tsoro ta ji ba”Mama!!! 

“Yi hakuri na yi sallama baki ji ba”

Ajiyar zuciya ta sauke tana cire hannun ta daga saman kirjin ta “kin ban tsoro ai”

“Yi haƙuri ranki ya daɗe”

“ba komai”

“Ya naga idon ki kamar yi kuka”

Murmushi tayi “da Baba na nake waya”

Gyaɗa kai ta yi “amma dai baki ce mai komai ba ko? 

” Kamar me? 

Ganin irin kallon da Asma’u ke mata ne yasa da sauri ta kyara kalamanta”Umm yauwa na kammala abinci”

“Ok  zan ci amma sai zuwa anjima,yanzun zan dan kwanta ne”

“To ranki ya daɗe a tashi lafiya”

Baci ta sha sosai dan sai wuraren La’asar ta tashi,wanka ta yi sannan ta gabatar da sallar La’asar,falo ta fito, kai tsaye dinning table ta nufa in da aka jera kulolin abinci,wanda zata iya ci ta zuba,ko loma uku ba ta yi ba sai ga Mama ta shigo,wacce ke ɗayan dakin zaune ta jiran tashi Asma’u. 

“Ranki ya daɗe har an fito? 

” Eh Mama sannu da ƙoƙari”

Murmushi ƙissa ta yi “ba komai ai kina ne,yauwa tun da kin tashi bari in je in kyara dakin”

“Kar ki damu na gyara”

Dan shiru ta yi tana tunanin hanyar da zata bi domin ganin ta shiga dakin Asma’u,dan tana buƙatar haka,amma ta lora kamar yarinyar tana da sauran hankali,Allah yasa dai kar ya zamana suna mata kallon rogo ne, rasa abin da za ta yi ne yasa cikin sanyin guiwa ta juya. 

Har ta yi taku biyu sai kuma ta ji ta kira sunan ta”Mama”

Da sauri ta juyo”na’am ”

“Sai dai ko zaki canza min zanin gado”

Wani irin daɗi ne ya kamata,dan bakin ta har rawa yake wurin amsa”to ranki ya daɗe”da sauri ta juya ta yi sama,tana shiga ɗakin ta hau buncike,ta na yi tana kallon ƙofa,har karkashin filo duk ta duba ba ta gani ba,daga gadon tayi baya wurin “to ina kuma ta ajiye” ci gaba da nima ta yi,dan ta tabbatar da in bata gani ba lallai ba karamin matsala za  a samu wurin Oga ba,kuma ta san halin shi sarai akan ta zai daura laifin,ganin yanda ta burkuta ɗakin amma bata gani ba yasa kawai ta shiga gyaran dakin, dan ta san ako wani lokaci ana iya samun matsala yarinyar ta shigo,

Ai kuwa hakan ne,dan ko kammala gyara gadon ba ta yi ba sai ga Asma’u ta shigo,kai tsaye gaban ma dube ta je ta ɗauki waya”sannu da aiki ”

Kai yarinya kamar Aljana,tun dazu fa nake nima amma ban gani ba,amma kuma ita tana zuwa ta ɗauka mtss,taja tsaki,jin ta kara ce ma ta sannu ne yasa ta amsa”Yauwa harkin kammala ”

“Umm”

Tana gama canza zanin gadon ta fita,waya ta ciro ta yi kira”Yallabai  ban samu damar ɗaukowa ba”dan shiru ta yi alamun ta na sauraron mai yake faɗa. 

“Ka yi haƙuri yallabai zan san yanda na yi na ɗauko”

“To” Sai kuma ta kashe.

   Da misalin karfe sha biyun dare. 

Zaune take idon ta biyu tana fuskantar ƙofa,kamar ko yaushe ji ta yi ana tafiya sadaf-sadaf mai makon ta ji an yi ta ƙofar can,sai ji ta yi an dafa kofar dakin ta za a shigo, ai da sauri ta mike kan katifa kamar mai bacci harda jan bargo ta kulle ido,tana ji sanda aka zo kusa da fuskan ta aka leka,fanin kamar tana barci yasa aka juya aka shiga caje mata daki, a hankali ta leko da kai tana kallon yan da ake niman wani abu,kasance dakin yanada ƙarancin haske yasa sai da ta zuba ido sosai sannan ta fahimci ko waye,ganin tana dawowa ta wurin kanta ne yasa da sauri ta kara mai da kai,

Dan daga kanta ta ji ta yi ta haska,sai kuma ta ciro wayan Asma’u da ce wurin,a hankali ta furta”ƴar banza sai iya boyo,yan zun bari na kai mashi tunda na samu da kyar”juyawa ta yi ta fita. 

Ganin ta fita ne yasa da sauri ta tashi zaune tana dafe kirjin ta “na shiga uku me kenan? 

Kafin taba kanta amsa har ta fara jin dan maganganu ƙasa ƙasa, gaban ta ne ya ƙara faɗuwa,”sunzo ke nan,waiyo Allah na shi ge su,Nanne, Baba tsoro nake ji,”

Komawa ta yi ta kwanta,yayin da ta dunƙule wuri guda,ƙarfi da yaji,take ƙoƙari  yin barci, yayin da shima baccin ya ki zuwa,sai tunanin da ta kasa bari,dan zuciyar ta sai kwadaita mata yake ta tashi taje ta gani me suke yi.

Ganin ta kasa natsuwa ne yasa kawai ta yi ƙarfin halin sakowa daga gado,a hankali ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito,tsayawa ta yi tana tunani to ta ina zata bi,takai kusan minti huɗu a tsaye kafin ta fara jin takun takalmi alamun wani  na zuwa ta wurin,makalewa ta yi jikin bango har suka zo suka wuce ta,Mama ce da wasu maza waɗanda ba ta gane ko su waye ba, dan haka bin bayan su ta yi. 

Hmmm,wani iko sai Ubangiji,wani abu mai kama ɗan ƙaramin botur dake manne jikin bango suka danna,wanda ita da ke cikin gidan ko da alama hankalin ta bai taɓa zuwa wurin ba,

Ƙofa ne ya buɗe da ƙanshi ta jikin bangon suka shige,tsoro ne ya kamata,ta shin ta shiga ta bi su ko kuma ta rufa ma kanta Asiri ta koma ɗaki.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button