WATA TAFIYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA TAFIYAR 13

“Wawuya, ke a  tunanin ki kin zo gidan hutu ko! har da sani dafa abinci,,da gyaran dakin! in banda ke da Kike mahaukaciya yaushe na miki kama da me aiki,dan tsabar gulma da munafurci har da kirana Mama! A’a ba Mama ba Mamu”ta kara sa faɗa tana dungure mata kai. 

“Yanzun Yaya yaza mu yi da wannan Mahaukaciyar?

Murmushi ya yi” tun da ta shigo tun yanzun ai shi kenan”

“Kamar ya “cewar uncle Nasir,dan uncle Tahir bai samu zuwa ba. 

” Yanzun dai a barta a nan har zuwa gobe idan mun dawo,kaga sai mu taho da takardun tasa mana hannu gaba ɗaya, ka ga kenan komai yazo mana cikin sauki”

Dariyan farin ciki suka yi,Talatu ce ta fito “yallabai na kammala”

“To yayi kyau,nasan dai kinsan abin da ya kamata,dan haka sai ki ci gaba da kula da komai,zuwa gobe wara haka zamu dawo”cewar uncle Ahmad. 

” To ranka ya daɗe”

“Kumu je” Ya ce ma su,nan kuwa suka kama hanyar fita wurin,har sun ɗanyi nisa sai gashi ta biyo su da sauri”yallabai,yallabai ”

Juyowa suka yi. 

“Ga wayan ta dana dauko dazu”ta faɗa tana mika mashi wayar Asma’u da  ta dauko dazu a dakin ta. 

Amsa yayi kawai ya jefa Aljihu suka wuce,ita ma bata koma kan Asma’u ba ta juya ta fita a wurin,yayin da ta bar ta a wannan underground din, wanda yake ihunka banza. 

Sosai take kuka saboda azabar ɗaurin da ta mata kaɗai ya ishe ta,wannan wani irin ƙaddara ce ta jihota nan,bayan tana murnar ta rabu da kaidin Matar Malam wacce ko zaman kishi basu ba,amma ita da uwarta suka nima rayuwar ta,bancin ko a wannan lokacin matar da Auren wani a kanta amma  sai da ta gille masu nasu auren,kuma har yanzun bawai sun kyale ta bane, gashi tana murnar ta rabu a Bukar sai gashi ta haifi Habu,yanzun ya zata yi da zayuwar ta. 

Me yasa tun farko da wannan matar ta faɗamata ta yi taka tsantsan ba ta kira Baba Mudansir ta faɗa mashi ba,ta tabbatar da duk hakan bata faru ba, da ace dazu da suka yi waya ta faɗa mashi cewa ba taga mijinta ba,da yanzun ƙila tana gida tare da Nanne,

Ji ta yi kamar ana kallon ta,hakan ne yasa ta juyo da sauri,ai kuwa wani irin razanannen ihu ta sake mai matukar karfi wanda nan take ta nima sauran numfashi da ya rage mata wanda dama manejin shi take yi ta rasa,dan take kanta ya koma gefe, alamun dai ta shede……..

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button