WATA TAFIYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA TAFIYAR 14

Ido ya zuba masu,dariya ta yi “yauwa dan gari,kalle ta da kyau yanda zaka gane ta koda kunje can,”

Ƙara dago kan Asma’u ta yi”oya ke ma kalle shi, kin ga wannan to shine mijinki ZABIHULLAH ZAMIR,dan haka ki rike sunan a kan ki, 

 Kai kuma wannan ce matar ka ASMA’U EL HABIB,kai ma ka rike sunan ta” ai kuwa kamar yasan mai ta faɗa sai kuwa gashi ya tsurawa Asma’u rikitattun idanun shi, 

Ita ma dan juyowa ta yi dan san ganin ko ya daina kallon su,ai kuwa cikin rashin sa’a in ji ta fa,sai gashi idan ta ya fada cikin na shi,wanda sabar rikicewa yasa sai da ta ji sau kan mari a fuskar ta wanda sai da ta yi ihu sannan ta dawo haiyacinta ta fahimci ashe fitsari tama Talatu a ƙafa,ai kuwa babu imani ta shiga kirban ta tana fika mata mari,shi kuwa mai da idanun shi yayi ya rufe.

Sai da ta gama jibganta sannan ta fita a dakin ta barta kwance a wurin ko motsin kirki bata iyawa. 

 Da daddare misalin sha biyun dare.

Wannan karan dukkan su suka zo harda uncle Tahir,anan suka samu Talatu,yayin da Asma’u ke saman kujera amma ba a daure ba,dan gaba ɗaya a galabaice take,

Gaisuwa suka yi,sannan kai tsaye suka tsaya a bakin gadon da yake kwace,cikin dariyar mugunta Haris ya ce”hello little brother,dama ina son in faɗa maka yau ne fa,ko in ce yanzun ne fa,kaga da zaran ta saka mana hannun ai shikenan,ni dai sakon da zan baka shine idan kaje can in ka haɗu da su ABU kace su yafe min kaji dan uwan na,dan haka juyo ka kalle yanda zan fara sheke matar ka “juyo da fuskan shi yayi setin Asma’u,uncle Tahir ne yace” Ina fatan kazo da takardar Nasir ”

“Eh nazo da shi,yana hannun yaya Ahmad”

“To ya isa haka Haris,kuzo muyi abinda ya kamata mu wuce,ku kyale wannnan dan kunsan shi ai bamu  gama da shi ba,dan shi kaɗai yasan in da ya ɓoye asalin dokiyar,dan wannan da muke hauka a kanshi, kashi ishirin ne bisa dari,,dan haka da sauran aikin shi,ita dai wannan mu fara gamawa da nata aikin tukunna” Cewar uncle Ahmad. 

In da Asma’u take zaune suka nufa da takarda a hannun Uncle Ahmad din,yayin da su kuma fuskokin su ke ɗauke da murmushin farin ciki.

A gaban ta suka tsaya yayin da uncle Ahmad ya Daura mata takardan saman Cinyanta har da bairo”saka hannu ”

Dago galabaitattun idanunta ta yi tana kare masu kallo,sannan ta mai da kallon ta izuwa ga Zabihullah wanda fuskan shi dai na fuskantar inda suke amma idanun shi a lunshe suke,lallai in da ranka kasha kallo,Yaya da kuma kawunne duk suna so su ga bayan shi,to me ya ji wanda be kama ya ji ba,me kuma ya gani wanda ya caccanci barin duniyar gaba ɗaya. 

Haris ne ya daka mata uban tsawa, wanda ba shiri ya dawo da ita hankalin ta”dalla Malama ki sama mutane hannu kin tsaya ki ba ta mana lokaci”

“Ba zan sa hannun ba” kalmar da ta girgiza kowa a wurin kenan. 

Mutuwar tsaye suka yi suna mata kallon mamaki, dan abun da basu zata bane,Mama Talatu ne cikin zafin rai zata kai mata duka uncle Ahmad ya dakatar da ita,”me yasa ba za kisa hannu ba”

Kai tsaye tana kallon idanun su tace”saboda nasan ina saka hannu zaku kashe ni,amma idan ban saka ba dole ku barni a raye saboda kuna  bukatar saka hannu na”

Wani irin mari Haris ya koda mata wanda sai da ta yi ihu,dan ji ta yi gaba ɗaya idonta ya rufe,”ke har kin isa ki kiyin abin da muka saki yi? 

Kara dago runannun idanunta tayi wanda  nan take jini ya kwanta a cikin daya, 

“Ko da zaku kashe ni,ku yi gunduwa-gunduwa da namana ba zan taba saka hannu a wannan takardar ba,balle kuci dukiyar da ba ku kuka tara shi ba, ba kuma hakkin ku ba ne”

Dariya uncle Tahir yayi,yana taɓa hannu “da kyau yarinya,amma ina so ki sani,in ba zamu iya kashe ki ba,amma dai ai zamu iya kashe wannan tsohuwar ta gida ko,wacce yanzun haka take kwance tana bacci,kin ga abu yazo gidan sauki,sai  mu sata a baccin da babu tashi gaba ɗaya,ta yanda data falka sai dai ta ganta  a lahira,dan haka zabi ya rage naki,ko saka hannu, ko kuma tsohuwa!!! ya karasa fada da ƙarfi. 

“Nanne!! Ta ambata sunan da matukar rawar baki…

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button