WATA TAFIYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA TAFIYAR 15

Su na shiga da sauri ya karasa wurin ta,nan take ya shiga duba ta cikin kwarewa,sai da ya ɗauki wasu yan mintuna kafin ya dago ya kalle uncle “wahala ne ya jawo mata dogon suna,wanda idan ta ci gaba da shiga irin wannan yanayin zuciyar ta tana iya bugawa,kasancewar  tana harbawa fiye da kima duk bayan wasu dakiku,haka kuma duk bayan dakikun takan rage harbawa shi ma fiye da kima,wato ta kanyi sanyi,hakan kuma na iya haifar da bugawar ta ako wani lokaci kenan,saboda idan ta tashi bugawa to zata halba ne da karfin gaske,wanda hakan ne ba a so”

“To yanzun ya za ayi? 

“Eh to akwai wasu alluran da nake buƙata in mata, kuma ban da su sai dai in je in siyo in dawo”

“To ba damuwa” Nan ya ciro kudi masu yawa ya bashi,amsa yayi ya fita da sauri.

“Yallabai kayi haƙuri,wallahi kuskure aka kasu,nima shigowa ta kenan na ganta haka”

Cikin tsawa da matsifa ya katse ta”imin shiru shashasha! Bancin irin uban kudin da muke biyan ki shine baki kula! To in ba zaki iya ba sai mu samu wata,kuma mu munce ki dake ta ne?to daga yau sai yau karma ki sake daure ta in ta farfaɗo aka komar da ita dakin,kar ki sake daure ta ko dukan ta,illa iyaka ki  saka mata ido sosai mu kuma za muji da sauran,dan sai ta gommace kiɗa da karatu tunda haka ta zaɓa!! 

“Dan Allah yallabai ka rufamin Asiri,wallahi da aikin nan na dogara, kuma na yi alkawarin duk zan kiyaye abin da ka ce”

“Da yafi miki, sannan in wannan likitan yazo ki tsaka mashi ido dan bana son asamu kuskure, dan kinsan ba shi ke mana aiki ba,shi Dr Bala baya gari, dan haka ki kiyaye”

“To ranka ya daɗe” Juyawa yayi ya fita zuwa falo,, T.V ya kunna yana kallo. 

Bai jima ba sai gashi ya dawo da Leda a hannun shi ya shigo, 

“yauwa Sultan shiga kawai suna ciki, in ka gama sai kazo mu wuce”

“To uncle” Hau rawa yayi har dakin,bai kula Talatu dake zaune ba,tana jimamin yau saura kaɗan ta rasa rayuwar ta,dan ta tabbatar da in dai har ta yarda ya kore ta ya canza wata,to bawai yana nufin kora ba ne,A’a yana nufin kashewa ne,dan ta tabbatar da kashe ta za suyi saboda taga sirrin su,kai ita kan ɗan ba ƙara. 

Cikin ƙwarewar shi yake kula da ita,Allurai ya mata,sai da ya tabbatar da ta farfado tana gane abu,sannan ya juyo wurin Talatu”ko zaki iya kawo mata abu mai dan ruwa-ruwa, saboda akwai Alluran da zan mata kuma yanzun,dan Allah ki yi sauri dan ana jira nane”

Kamar zata ce wani abu,amma ganin yanda ya bata rai ne yasa kawai ta tashi ta fita,yana ganin fitarta da sauri ya ciro wani dan gundun fefa daga Aljihun shi ya ce “gashi imaza ki ɓoye,in kin samu dama ki karanta”

Kamar ba zata amsa ba,amma ganin yanda hannun shi ke rawa,da kuma yanda yake kallon kofa ne yasa ta amsa,ta tura cikin riga,tana fito da hannu uncle Tahir na shigowa,

ɗan kare masu kallo yaye kamar mai nazari,dan a falo ya haɗu da Talatu shine yake tambayar kome ya sauko da ita,, tana faɗa mashi shine ya shigo da sauri dan shi mutum ne mara yarda. 

Ganin hakan ne yasa Sultan din ƙara haɗa fuska ya shiga kara mata ruwa,koda aka kawo   shayin,da kyar ta iya sha, sannan ya mata ɗayan Alluran ya kuma ba Talatu magunguna,sannan suka fita gidan da uncle. 

Sai ƙarfe uku ruwan ya ƙare wanda cikin waɗannan awoyin maimakon ace ta samu isasshen barci sai ta kasa,da ta fara bai wuce mintina biyar zuwa goma zata farka a firgice,hakan ne ma yasa kawai ta hakura da baccin,ruwan na ƙarewa ta dauke ta ta mai da ita wannan Underground din,sai dai wannan karon sai da ta rufe mata fuska da bakin kyalle dan karta gane hanya,kuma a yana yin tafiya kaɗai ta fahimce ba hanyar da ta bi ba ne wancan ranar, har cikin wani daki ta kaita sannan ta buɗe mata ido,sai dai fa abin mamaki wannan dakin ba irin wancan ba ne,kuma tare aka ƙara haɗa su,wato ita da shi, sai dai shi har yanzun a kwance yake saman irin wannan gadon dare da belet,tana tura ta dakin ta fita ta kullo masu ƙofar, wanda ya kasance da Na’urori yake amfani,dan gaba ɗaya ƙofofin wurin da Na’ura da kuma number suke buɗewa da kullewa,shi yasa in baka sani ba ba daman fita kuma ba daman shiga. 

Ajiyar zuciya ta sauke ganin idon shi a kulle kamar yawancin lokaci,

daya daga cikin kujerun ta jawo ta zauna,a hankali ta warware takardar da wannan likitan ya bata,wanda ta ciro daga cikin rigar ta,abin da takardar ta ƙunsa kuwa shine,(ko ta halilin yaya ki ɗaure duk wani kalan azabar da zasu miki, kar ki kuskura ki saka hannu,sannan daga ƙarshe ki bi duk ta kowani hanyan da zaki bi domin ganin kun bar wannan gidan ke da Zabihullah  nan da ƙwanaki huɗu,in ba haka ba a kwana na huɗu zasu kashe ki su aura mashi wata,wacce za ta saka masu hannun,yanzun haka harsun fara niman auren yarinyar,wannan ne tsarin su, dan haka  ki gaggauta).

“Innalillahi wa’inna’ilaihi rajiun!! Nan da kwana huɗu,to ta yaya zan yi in fita daga wannan ramin,ga waɗannan mahaukatan kofofin,sannan ya zan yi da wannan mutumin,ya Allah ka samar min mafita”

Tashi ta yi daga zaune, kai tsaye wurin gadon da yake kwance ta nufa,tsayawa ta yi a kan shi tana ƙare mai kallo,can kuma a hankali ta buɗe baki ta kira sunan shi”ZAMIR ka tashi mu yi magana “tamkar ya ji mai ta ce, sai kuwa gashi ya buɗe idanun shi tar a kanta,wanda hakan ne yasa da sauri ta matsa baya..

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button