WATA TAFIYAR 6

????WATA TAFIYAR???? Story & Written
By
Jiddarh Umar
????????????????????????????????
*????✨MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*“`We are the moonlight writers we shine all over the world.“????`* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~????????~~~~~~~
PAID BOOK
Free Page
06
Ga mai buƙata zai turo 200 ɗari biyu ta wannan Asusun 2284905309,Hauwa Umar Zenith Bank,
Sai ki turo shaidar biya ta 08141644865.
Ko Katin Waya.
Washegari da rana, tsaye suke a ƙofar gida,”Malam kasa an kirani kuma ba kace komai ba ka tsare ni da ido”ta faɗa tana turo mai baki,wanda ba ta san hakan da take yi ba karamin rura mashi wani irin wuta yake a zuciyar shi ba,a gaskiya wannan abin da ta ma Asma’u ba ita taima ba,wallahi shi ta cuta kuma ba zai taɓa yafe hakan ba duniya da lahira,domin ta cutar da su ta raba tsakanin masoya,wanda yake ganin har abada ba zai taba mai da kamar ta ba,domin Asma’u macce ce wacce ko wani ɗa namiji zai yi fatan samu a matsayin matar sa,ga dai ta yar ƙarama a ido amma fa ta san takan tsiya,domin duk girman fushin ka ko ji da kanka ta san ta salon da za ta bi da kai cikin sauki kuma ka fado hannu ta,tuna hakan ba karamin ta da mai da hankali yake ba,yanxun haka yana kallo wani namiji zai dauki wannan sarauniyar,gaskiya yana cikin wani hala,tsakanin shi da wannan saidaniyar sai Allah domin ta cutar da rayuwar shi.
Cikin mutuwar jiki ya kira sunan ta”Asma’u,yanzun kina gani za a raba ni dake, bancin kinsan irin son da nake maki”
“Amma kasan ni ma ina son ka Malam,sai dai rayuwa itace gaba da komai,ka duba yanda aka mai da ni kamar wata mahaukaciya,kullum dare sai na ɗauki alhakin mutane, wasu su tsine min yayin da masu tausayin cikin su ke min Addu’a,gaba daya rayuwata a yanzun ba ni da natsuwa na zuciya da ruhi,wannan duk saboda menene! Wani laifi na aikata Malam! Koɗan na aure ka shi ne laifi na Malam!”
Ajiyar zuciya ta sauke tana share hawayen ta”dole mu rabu ko muna so ko bamu su,,idan ba kada magana zan koma cikin gida”
“Dan Allah ki yafe min,in na cutar da ke a zaman mu”
“Baka min komai ba Malam,,kuma ina maka fatan alheri”
“Wata soyayyar ta kan koya mana cin amanar na kusa da mu,yayin da wata soyayyar ta kan koya mana yanda zamu rayu cikin gaskiya,,
Wata abota ta kan koma soyayya,amma ni tawa soyayyar ina fata ta koma abota,,ina son ki ɗauke ni a matsayin yayan ki kuma abokin ki,idan har kina da buƙatar taimako a kowani lokaci kina iya ni ma na” ya ƙarasa fada yana murmushin dole wanda yafi kuka ciyo.
Ƙasa magana ta yi,sai gyaɗa mai kai da ta yi kawai,sannan ta shige gida.
Zaune suke a harabar gidan su uku suna tattaunawa akan niman auren Haris da zasu je”ya kamata ku biyu ku fara zuwa, duk yanda kuka yi da su sai mu ji”cewar uncle Ahmad.
“Amma kuna ganin ba matsala,dan na riga na gama bincike akan yarinyar,sai dai abin da ban gane ba game da yarinyar shine a kan iyayenta,na kasa samun komai game da su,duk irin binciken da nayi,”
“Dama ba a hannun iyayenta ta ke ba? Uncle Nasir ya faɗa yana kallon Uncle Tahir dan son jin karin bayani..
” Tana tare ne da family Maman ta tun tana jaririya,a yanda na samu labari iyayen yarinyar sun gudu ne akan wani gagarunin abun daya faru a wanna lokacin”
“Me ya faru?cewar uncle Ahmad.
” Shine har yanzu ban samu amsar ba, abin da na sani shine kawai yarinyar ta samu lalura ta sanadin auren wani Malami da tayi,yanzun haka kakarta da yayan Maman ta ke kula da ita,kuma bana tunanin zasu bada auren ta a yanda take dinnan ”
Uncle Tahir ne yace”to ba sai muce masu za mu nima mata magani ba, idan ya so kaga kafin auren sai mu sama mata wanda zata daina ihun nan kawai,dan kar ta zo ta cika mana gida da ihu,amma batun ta bar hauka bai ma taso ba,dan munfi buƙatar ta a haka, ko ya kuka gani?
A tare suka saki dariyar farin ciki”gaskiya shawarar ka mai kyau ne”
To yanzun ku tashi ku tafi kar yamma ta yi “da uncle Tahir da Nasir za su.
Misalin karfe biyar na yamma suka shigo cikin unguwar Daji dai-dai kofar gidan Ɗan Nanne suka tsaya,kasancewar Haris ya faɗa ma Habu ya sanar ma Baban shi zai yi baƙi da ƙarfe biyar,shi dai baisan wasu irin baƙi ba ne,sai dai ya sanar ma Baba Mudansir,wanda shima jin nace suna da baƙi kuma Habu ya sanar da shi Ogan shi ne, yasa shima ya faɗa ma su Ɗan Nanne.
A falon gidan wanda suke aje baƙin su, nan aka sauke su uncle Tahir sannan aka kawo masu ruwa da cups,Baba Ɗan Nanne jikin shi har wani rawa yake ganin manyan mutane sai wani washe baki suke,bayan gaishe-gaishe ne aka shi ga gabatar da kai in da Baba Dan Nanne ya fara bayani “Ni suna na Salmanu,amma anfi kirana da Ɗan Nanne,ni ne Babba sai ƙanne na guda uku gasu nan,mai bi min shi ne Mudansir, sai Auwal,sai Sani,to ku kuma bamu waye ku ba”
“Ni suna na Tahir,wannan kuma ƙanina ne Nasir,sai babban yayan mu Ahmad wanda muka wakel ce shi a yanzun,kuma ba komai ya kawo mu ba face ni ma wa ɗan mu auren yar ku”
Wani irin farin ciki ne ya kamasu gaba ɗaya, Baba Sani ne yace”to ya’yan mu yawa ne dasu, wacce daga ciki?
Gaba ɗayansu a ba zata suka ji saukar sunan ta”Asma’u “cawar uncle Tahir.
Tsabar mamaki da rudewa har suna haɗa baki wurin maimaita sunan” Asma’u kuma”
“Eh ita,domin ɗan mu ya gani kuma yana so”
Baba Auwalu ne ya tare zancen da cewa”mu dai gidan nan Asma’u daya gare mu,kuma tanada matsalar tabin hankali,sai dai ko daya daga cikin yaran mu ”
“A’a gaskiya ita ya ce, kuma a shirye muke da mu nemo mata magani,in har zaku bamu da zuciya daya”
Nan take falon yadau shiru, wani rin hassada da kyashi ne ke taso masu,ya za ayi su tsallake yayan su masu hankali su zaɓa mara hankali,bancin ga yan mata nan a gidan wadanda suka fi Asma’u komai,
Baba Ɗan Nanne ne yace”Alhaji mai zai hana kace ma ɗan ku yazo ya zaɓa cikin yaran gidan, ni ma da kaina ina iya bashi auren ƴa ta Maimuna,ba abin da Asma’u zata nuna mata,ban cin haka ita lafiyar kalau Amma ita wancan fa shafar Aljannu gare ta”
Kiri-kiri suke hango hassada a idanun waɗannan mutanen,ban da mutum ɗaya, wanda tunda aka fara magana kanshi na duke,sai yanzun da ya dago kai.
“Kun ce za ku nimar mata magani ta warke?
” Kwarai kuwa”
“Kuma kuma ganin ɗan ku zai iya zama da ita a haka?
” Sosai ma kuwa, dan ba kasan yanda ya damu da ita bane ”
“To shi kenan ni na bashi aurenta,idan ya shirya kuma sai ayi komai” gaba ɗaya juyowa suka yi suna ma Baba Mudansir kallon mamaki,sai dai ba damar magana tunda a gaban baki ne, kuma ba zasu so suyi wani abin da za a tafi da su ba.
murmushi samun nasara suka yi “mu a shiyar muke, dan yanzun haka da kudin auren mu muke tafe,in kun shirya sai mu bada, sai a saka lokaci,amma ba mai tsayi ba,dan mu ƴar mu kawai muke buƙata ba wani abu ba”cewar uncle Nasir yana wani murmushi.
Nan suka ciro ban dir na yan Dubu-dubu guda uku suka a juye a gaban Baba Ɗan Nanne”wannan ban dir ɗaya na kudin gai suwa ne dubu ɗari,daya na saka rana ne, ɗaya kuma sai a tsiya goro, ku yi haƙuri mun manta bamu tsayo ba”
Baba Mudansir ne ke kokarin yin magana, cikin sauri Ɗan Nanne ya tare numfashi shi,dan ba zai bari ya masu salalan tsiya ba,tunda ya ma ya’yansu bakin ciki,yanzun ba zai bari ya masu ciki baƙi ba akan wannan kuɗi,, dan ya san halin ƙanin shi sarai yana iya cewa kudin sun yi yawa a rage, “to Alhamdulillah komai yayi Alhaji, yan zun zuwa yaushe kuke son asa lokacin biki?