WATA TAFIYAR 8

“Alhamdulillah” ta amsa
Dan shiru wurin ya kara ɗauka na wasu yan daki kai,da kyar ya iya amayo waɗansu kalamai,wanda shi kan shi ba ƙaramin jinjina ma kan shi yayi ba.
Shima cikin wani irin salo da ƙwarewa na irin wayayyu maza ya ce “Baby ya jikin ki”
Ta gefen ido ta kalle shi,sabon salo wai Baby,amma fa gay din gaskiya ya haɗu, dan shima fare ne amma ba kar ba, sai dai yafi ta hasken fata, dan in zata tsaya a kusa dashi ana iya kiran ta da baka a kan shi “da sauƙi”
“Baby idan kina buƙatar wani abu ki faɗa min kin ji,kin ga bikin mu sauran wata ɗaya,idan har akwai wani abin da kika shirya sai ki sanar da ni,yanzun zan baki number waya na”
A hankali tace “ba abinda zan yi,kuma ba nada waya”
“Ok ba damuwa” daya daga cikin wayoyin hannu shi ya cire sim din ya ajiye mata a gaban Table din da yake gaban shi,hade da wani kwali, da leda”ga wannan wayar ki fara maneji da ita,sai wannan magani ne in ji uncle dina wai hayaƙi zaki dinga yi da shi safe da yamma ”
“Na gode Allah ya saka da Alhairi”
“Amin Baby, to zan koma amma sai Next week zan dawo”
“To Allah ya kaimu”daganan fita yayi ya wuce, yana mai sauke ajiye zuciya.
Ɗauka wayan da kayan ta yi ta fita a falon,dai dai babban bishiyar tsakar gidan Ɗan Nanne ta tadda iyayen su mata zaune suna shan iska, wanda a zahiri zaman jiran shigowar Asma’u suke yi,dan tuni suka samu labarin zuwan wanda zai Aure ta,har ta da irin motar da yazo da kalan kayan da ke jikin shi duk sun samu labari, dan haka tana isowa kusa da su ta ce “sannun ku Mama”
“Yauwa su Asma’u an dawo kenan daga wurin hiran”
Shiru ta yi ba ta ce komai ba.
Maman Hafiza,matar Baba Sani ne ta ce “to kawo ledar muga me ke ciki”
Ba tare da tunanin komai ba ta tasa hannu ta cire dan karamin kwalin da hayakin ke ciki,, sannan ta mika masu lidan.
Da sauri Inna Larai ta ce”A’a to ya kuma kika cire wannan, kodai shi na musamman ne”
“Inna wannan magani ne a ciki, hayaki ne yaban wai inji kawun shi”
Tana kaiwa nan ta juya ta shige shiyan su,da Inna Saude ta ci karo.
Cikin murmushi ta ce”ba dai har sirikin nawa ya wuce ba?
Itama murmushi ta maida mata,dan a zahiri tana iya ganin irin son da matar ke mata”ya wuce Inna, gama maganin da ya kawo min “ta mika mata kwalin maganin.
Baƙin bishiya kuwa,buɗe ledan suka yi,waya ne a ciki, sai kayan maku lashe,nan inna Larai ta kwashe ta raba masu da ya’yan su” Kowa yaci, dan dole mu rage zafi, dan wannan abin da aka mana ba ƙaramin cin fuska ba ne ”
“Humm ku dai ku kwantar da hankalin ku,wai ku a tunanin ku wannan auren yuwa zai yi ne?
Gaba ɗaya juyowa suka yi suka kallon inna Balki, matar Baba Mudansir, ” Me kike nufi Balki”
A ƙofar gida kuwa, tun bayan Wucewar Haris unguwa ya ɗauka ai Haris Zamir shi zai Aure Asma’u harma ansa biki nan da wata daya,wani ɗan saurayi da ke zaune a gefe ne yace”wai nikam waye Haris Zamir dinnan ne?
Wani ne mai suna Mu’azu ya ce “kai kana garin nan amma bakasan Zamir family ba”
Na suka dasu ne ya ce “to ai Mu’azu ba abin mamaki bane idan ka yi la’akari da yanayin family ɗin”
Wanda ya fara tambayar ne yace”ni dalla ku faɗa min abu,naga sai wani kwana kwana kuke min”
Mai suna Mu’azu ne ya ce “su ba wasu sanannun masu kudi ba ne kamar sauran shahararrun masu kuɗi,idan kaji ana kiran musulmin kuɗi to ya ƙare a Zamir family,domin su tun azaliyan su sun gaji dukiya wurin kakannin su,Allah ya musu dukiya wanda su karan kansu basu isa su ƙarar da shiba,sai dai kuma su basa buƙatar wani daukaka ko nuna su shahararrune ta fanni komai,shi yasa ba kowa ya san su ba,kuma ba ƙaramin taimako suke yi ba,sai dai komai nasu sukan gudanar da komai ne kan tsari,”
“Aiya gaskiya sun burge ni,hala wannan ne kaɗai ɗan su?
” A’a ba shi kaɗai ba ne,dan yana da ƙani mai suna Zabihullah Zamir,wanda shi ne asalin wanda ya gado hannun Arzikin iyayen su,in kanajin ana fadin yaro da kudi abokin tafiyar manya, to shi ne,domin sam bai damu da tarin dukiyar da Allah ya azurta family su dashi ba,dan shi mutum ne mai harkoki da yawa,kuɗi gare she na tsiya,domin dukiyar da Zabihullah Zamir ke da shi duk kudin family su to bayan shi sake,domin shi bai ma cika gudanar da harkokin shi cikin ƙasar nan ba,a takaice yakan ɗauki shekaru bai ko leko Nijeriya ba”
“To yanzun yana ina?
Gaba dayan su shiru suka yi,Mu’azu ne ya fara leke leke, saida ya tabbatar da ba wanda za iya jin abinda zai faɗa sai su, sannan cikin ƙasa da murya ya ce “wasu sun ce wai shekara uku data wuce ya mutu a haɗarin mota, yayinda wasu ke cewa Kasheshi aka yi,wasu kuma na ganin har yanzun yana raye, to dai ba wanda ya san gaskiyar magana har yanzun”
Bude baki suka yi gaba ɗaya suna mai kallon mamaki”to matar shi fa da yaran shi ”
“Kai dai ka iya tambayar banza, nace maka ƙanin Haris ne,yaro ne ƙarami, kwata kwata bai wuce shekara shirin da shida, a lokacin da abun ya faru ba, na dai samu labarin zai auri wata yar uncle ɗinsu, to bansan yanda abin yake ba kawai sai labarin mutuwar shi da muka samu”
Ajiyar zuciya dukkan su suka sauke, jin an kira sallah Magrib.
[ad_2]