WATA TAFIYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA TAFIYAR 9

 

????WATA TAFIYAR????       Story & Written

                By

         Jiddarh Umar

????????????????????????????????

*????✨MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????✨*

https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

 *“`We are the moonlight writers we shine all over the world.“????`* ✍️✍️

بِسم الله الرحمن الرحيم

~~~~~~~????????~~~~~~~

PAID BOOK

      Last Free Page    

               09

Ga mai buƙata zai turo 200 ɗari biyu ta wannan Asusun 2284905309,Hauwa Umar Zenith Bank, 

Sai ki turo shaidar biya ta 08141644865.

Ko Katin Waya.

 “Me kike nufe Bilki? 

Dariya ta yi sosai”ai ban ce komai ba,kawai mu jira lokaci mu ga yanda Tafiyar za ta kasance,shin zata yu kuwa,ko kuwa Tafiyar wacce za a dawo baya ne, mu dai muna nan muna jiran muga yanda WATA TAFIYAR zata kasance” Tana kaiwa nan ta tashi ta shige shiyanta.

Baki buɗe suka bita  da kallo,Inna Larai ne ta ce “me take nufi”

“Ina zamu sani, sai dai kawai nu jira lokaci kamar yanda ta ce,sai muga yanda wannan Tafiya zata kasance” daganan wannan taron ya tashi.

Alhamdulillah yanzun jikin Asma’u da sauƙi sosai dan ta daina wannan haukan bige-bigen da take da kuma ihu,saidai kuma ba wai abin ya sake ta ba ne,dan har yanzun kanta na rawa,dan idan ka kalle ta ko yanayin ta kawai yanda suka mayar da ita ya isa ya shaida maka ba ita kaɗai ɓace,wani lokaci kuma in ƴan rashin kunyar suka taso kuma ta kan yi,kuma ba ko wane lokaci ba ne suke buge ta. 

A hankali lokaci ke tafiya wanda gashi yanzun har an wayi gari a gobe ɗaurin aure. 

Zaune suke su huɗu a wani babban falo wanda ya ji kayan more rayuwa,wata budurwa ce ta fito daga wani daki wacce aƙalla zata kai shekara ishirin da shida,fara ce sosai amma kuma da ka kalle ta kasan farin bana Allah bane kaɗai har na mai,kai tsaye tana zuwa zama tayi saman cinyar Haris,yayin da ta ɗaura hannun ta daya saman Kafadar shi,Kiss ta manna mai a kumatu,”Anya Haris zan iya jure wata mace ta amsa sunan ka kuwa”

Abdullah ne ya ce “to ai dole kiyi haƙuri dan na san sai ta kwanta a inda baki so”

“To wallahi kuwa dana kashe ta,dan banga wacce ta isa ta taɓa ma kwancinaba,wallahi ko wacece sai naga bayan ta,” Cikin bala’i ta juyo ta kalli shi “Haris ban yarda a ɗaura wannan auren ba,wallahi idan aka ɗaura sai na kashe yarinyar nan”

Sultan ne yace”to aka faɗa maki shima son ta yake, mahaukaciya ce fa,ban ci gaki me zai yi da wannan ƙazamar yarinyar,ƴar  matsiyata”

“Farisa ki kwantar da hankalin ki,dan ni ba shashasha ba ne,kuma wannan abin da kika ga duk tsarin Dadyn ki ne uncle Ahmad,shi ya tsara komai,in bancin haka me zan yi da wannan abun,kuma kinsan ni ba zan taɓa cin amanar ki ba saboda irin abubuwan da kika min a rayuwata,ba zan taɓa mantawa ba kin sadaukar da abubuwa da yawa domin mu,ciki kuwa har da wanda ban yi zata ba, ko wannan auren da za a yi a gobe ki jira kawai ki ga yanda abubuwa zasu kasance,kuma na miki alkawarin ko kallon ta ba zan yi ba a matsayin mata, kuma da zaran ta kammala mana aikin mu,za musan yanda za mu yi da ita”yana kaiwa nan ya shiga sauke mata tagwayen kiss a baki,ba tare da kunyar ko shakkar wadanda ke zaune a wurin ba,suma kuma ci gaba da hirar su suke kamar ba su ga ko mai ba,ganin abun nasu na niman yin nisa ne yasa Sultan jan ƙaramin tsaki”daɗi na daku wani bi ƴan iska ne,shi yasa ban cika son zama in da kuke ba,dan ba wuya sai ku ta da ma mutum da feeling din shi,har balle irin mai ƙaramin mara”dariya Abdullah ya yi “ai kaima idan ka samu wuri haka kake”

     Gidan Ɗan Nanne

Inna Saude ce ta kira wata mai lallin gargajiya wance ta ƙware a unguwar ta fanni iya tsara salatif ta jera shi tamkar dizay ita ta kira ta tsara ma Asma’u,sosai kuwa abin ya kama ƙafar ta da hannun ta yayi ƙyau. 

A ranar kuma wasu mata suka kawo kayan auren Asma’u wanda ya girgiza ahalin gidan dana mutane, domin kaya ne wanda ko a auren ta na farko bata samu ko da kwotan su ba,Akwatuna ne guda takwas,duk wani abu da ƴar gatan Amarya ke buƙata to an zuba acikin akwatin,dan ƙaramin akwatin ba abin da ke ciki illa manyan abin wuya da dan kunne abin hannu agogo duka na ɗanyen zinari da azurfa masu azaban tsada,ganin irin wannan dukiyar da aka narka ma Asma’u ba ƙaramin ɗaga hankalin wasu yayi ba,yayin da wasu ke tayata murna. 

   Washegari,ranar ɗaurin Aure. 

Kasancewar a dakin Nanne take kwana yanzun yasa yau tun da ta tashi sallah Asuba bata koma ta kwanta ba,kuma ba wani zikiri ta ke ba, kawai dai ita tana zaune ne kamar wata wacce ta tafi duniyar tunani, zama Nanne ta yi kusa da ita”Fettel tunanin me kike yi? 

“Nanne nima bansan tunanin da na keyi ba”

“To ki tashi ki shiga wanka, kuma ki daina zama haka kina irin wannan tunanin da bakisan me kike tunawa ba,dan baida anfani” Ƙoƙari tashi take,da sauri ta riko mata hannu, jiyuwa tayi ta kalle ta,ganin yanda hawaye ya cika mata ido ne yasa Nanne komawa ta zauna”Fettel akwai abin da kike son ki fadamin ne? 

Da sauri ta share hawayen da ya zubo mata”Nanne dan Allah ki yafe min,haka kawai na ƙasa samun natsuwa,ji nake kamar zan yi wani irin tafiya mai nisan gaske,wanda ba zan dinga ganin ki ba ko  su Baba,Nanne ina jin wani iri,ina mai rokon ki koda zan yi irin wannan tafiya ki yafi min ki kuma yi min addu’a domin Allah kaɗai yasan yanda na keji a raina”

“ki dai na faɗar haka Fettel,insha Allah ba abinda zai faru dake, kuma ba inda zaki tunda  naji sunce anan zaki zauna,kar ki ƙara faɗan haka dan idan wani abin ya same ki ni kuma ya zan yi da rayuwa ta, tashi ki shiga wanka” Haka dai ta tashi ta shiga wanka. 

Ba wani taron azo a gani aka yi ba,kasancewar matan gidan ba wacce tayi gaiyata tunda ba auren yarta ba ce,

Bayan an sauko sallar Juma’a ƙofar gidan Ɗan Nanne cike yake da ɗinbin jama’a,duk zauna suke ana jiran ɗaurin aure su uncle Ahmad da su Haris sune gaba gaba, duk sun sha manyan kaya,makar yanda Addini ya koyar haka aka shiga gabatar da daure Aure,wani abu wanda ya girgiza alahirin al’umar da ke wurin shine jin da suka yi limami na shaida an daura Auren ZABIHULLAH ZAMIR da ASMA’U EL- HABIB akan sadaki dubu ɗari,gabaɗaya ji kayi wurin yayi tsit kamar ba mutane a wurin,sai kuma can lokaci guda kamar an dawo da kowa cikin haiyacinshi nan wuri ya dauki hayaniya,Baba Mudansir ne cikin tashin hankali ya samu liman”Malam ya aka yi hakan ta faru”

“Wallahi nima yanzun yanzun yan gidan yaro suka sanar da ni wai an canza ɗaurin aure ya koma kan yayan shi,wai dama dashi za a yi”

“Innalillahi wainnailaihi rajiun” Shine kawai abinda Baba Mudansir ke maimaitawa, juyawa  yayi ya samu su uncle Ahmad dake ta washe haƙora suna hamdala,yayinda Haris dasu Sultan suke tsaye a gefe suna hiransu cikin tsananin farin ciki da annashewa, 

“Ranka ya daɗe wai me ke faruwa ne? 

” Oh karka damu da ma wurin fadan sunan ZABIHULLAH  ne nayi kuskuren kiran sunan Haris, kuma da ZABIHULLAH  da Haris ai duk abu ɗaya ne yayi su”

“Wannan ai rainin hankali ne,ta yaya zaka Aura ma mutacce rayayye, bayan mun samu labarin mutuwar yaron shikara uku da suka wuce”

“Waye yace maka Zabihullah ya mutu, to bai mutu ba,yana nan raye, dan haka ka kwantar da hankalin ka,,dan mu yanzun zamu wace da Amarya”

“Ai kuwa ba zan taɓa ba da ƴa ku wuce da ita ba, har sai naga Zabihullah da ido na” yana kaiwa nan ya juya ran shi aba ce, wannan wani irin renin hankali ne wannan,wallahi ba zai yarda ba, yau sai dai ai wacce za ayi. 

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button