WAYAFI SONTA 11

P11
…Wani mugun juyawa cikin hjy yyi ! Tadafe k’irji cikeda tashin hankali” tana furta Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un! Akid’ime ta fito dg toilet d’in, ta kunna wutar d’akin had’e da dafe Kai tace nashiga ukku na! ace yarinya ta fansheni ,ita tazab’i tabisu?” Koni na haifi zainab iyakar abinda zatamun kenan! Wannan yarinya ta Saida ranta,to insuka dubafa sukaga yarinyace itafa? Bama wannan ba mezancewa su sule(baffanta) insun tambayi Ina zainab?”yah ALLAH ka kamana mafita hjy ta fad’a hawaye na zuba a idonta! Taja
numfashi tace bazan tab’a nadamar aikin y’ay’ana ba sbd akan gsky suke ,Kuma insha ALLAH bazasu tab’e ba!tunda anan abincinsu yake,Kuma komai zai faru damu to ALLAH ya rubuta…. knocking hjy taji! Bbu wani tsoro ,tace waye…nine hjy taji muryar baba Mai gadi! Hijab tajawo tasaka ta bud’e k’ofar tasamesa tsaye acikin parlour!kallo d’aya yamata yasan tana cikin tashin hankali,sbd ganin kukama take abinda baitab’a ganiba…hjy akwai matsala wlh! Babbama cewar hjy tana nufar k’ofa tace muje waiting parlour….tun dg sadda yagansu da dirawarsa d’akin zainab dajin furucinsu akan billiya duka yasanarma hjy…cike da tsantsar tashin hankali hjy tace billiyafa kace?” Eh wlh hjy k’ilama shine yasanar musu cewar y’allab’ai baya gari sukazo! Cewar baba Mai gadi!
Hjy tace yanxun muje waje naga security d’in!baba Mai gd dake tsaye kusada k’ofar fita waje ,yace ah ah hjy kada jininki yahau ki barshi kawai…nakira office d’in su y’allab’ai cewa bbu lfy agdnsu DSP ALIYU haidar!sunce suna zuwa bayan fitar Yan garkuwa da mutane nafad’a musu haka… Cikin kuka hjy kesanar masa cewar da zainab sukatafi! Baba Mai gadi yazaro Ido ,had’e da cewa inna lillahi wa inna ilaihir raju’un!sadda Ina lab’e naga sunshiga ciki ,sainaje da wayata na dauki lambar motar!nakoma d’aki,suka fita…hjy na hawaye tace munshiga ukku!….k’arar jiniya ita tasaka hjy yin shiru ta d’ago Kai! baba Mai gadi yyi saurin fita!
A compound d’in gdn yasami police sunkai kusan 20 da wani abu…sunfara dube dube…. had’e da d’aukar gawa 3 sai wad’an da akama rauni mutum5 , yyinda bbu mutum 2 sbd police 10 ne haidar yasaka sukula da gdn! nan akayi asibiti dasu, yyinda wasu police suka nufi waiting parlourn gdn danyin bincike,akan jagorancin baba Mai gadi…akuma lokacin anfara Kiran farko na asubah!
Hjy da byn fitar baba Mai gadi ta nufi dakinsu zainab ta d’akko elham ta fito da ita!bed room nata ta koma had’e da d’akko wayarta…tafito waiting parlour taduba taga miss call na haidar da faruq sunfi a k’irga! wani Kiran yakoma shigowa cikin wayar….kafin ta d’aga su baba Mai gadi sun shigo da sauran police d’in,suna Yan dube dube had’e da Mata tambayoyi….wayar guda tayi Kara yad’aga,kafin yace to ogah…kallon hjy yyi yace mama ga DSP nan zaikira kuyi video call! Kafin hjy tayi mgn wani Kiran yashigo! d’agawa yyi had’e da mik’a wa hjy,yadubi saura Police d’in yace muje…nan suka fice…Arikice haidar dake kallon hjy yace alhmdllh danaganki lfy hjy tah…ALIYU! hjy takira sunansa! da sauri haidar ya dubeta acikin wayar jin takira sunansa na asali…faruq yace hjy kuka kikeyi meyafaru??kowani abu sukamiki?”suntafi da ZAINAB! tafad’a hawaye na zuba afuskarta….Sunyi kiddnaping d’inta ,azatansu nice, zainab ta kwanta kan gadona tayi basaja dani, sunwatsa Mata powder suka fice da ita akan idona Ina bayi! danasan hakan zainab zatayi dabanbi umarnin taba na nashigar dani bayi datayi wlh….. what?” Faruq da haidar suka fad’a arikice had’e da furta la’ ilaha illah antassiba hanaka inni kuntti Minal zalimin?
Mezancewa su mamana insun tambayi zainab? Hjy ta fad’a tana hawaye… gaba d’aya haidar ya jik’e da gumi!cikin dakiya yace hjy gamunan zuwa tajirgi zuwa 8am Muna Abuja insha ALLAH… jirgin karfe 6 zamu hau! A office suka kirani akan cewar gdnmu bbu lfy shine nakira Baki dagaba! Duk faruq yadamu…Dole yadamu…kudawo ayi mgn kada sucutar da y’ar mutane batajiba Bata ganiba!faruq yace hjy Ina elham? elham na bed room d’ina,yyi ajiyar zuciya yace babbar matsalar zainab bata mgn! Haidar yace hjy kada kisanar da su mariyar komai kibari muzo…bejira amsartaba yadatse Kiran….
Hjy kuwa alh takira tana kuka tasanar Masa….yace Mata shima Dole yabar abinda yakeyi yazo!kafin tayi sallar asuba tana addua tana kuka!kukan elham ta ji dake kan bed tana bacci!sai Kiran sunan anty zainab takeyi” hjy ta rungume ta tana kuka ! Tace elham anty batanan amma zata dawo… gaba d’aya elham ta rik’i ce sai ihu takeyi!hjy kuwa har idanunta sun kumbura sbd kuka…..
B’angaren su haidar kuwa , number baba Mai gadi yanema ,kafin yakirasa yatambayesa?” akan meyasani gameda zuwan kidnapers din”? Yasanar Masa abinda yasani,yakuma sanar Masa yadauki number! Shiru kawai haidar yyi! Sbd bega amfanin daukar number ba! Meyasa bekira ba ,lokacin dayaji Harbin bindiga…a office?” Kira yyi a office nasu yasaka amasa binkice akan billiya Kuma akamashi ko inyazo shi yadamk’esa!
gaba d’aya faruq bashida kuzari ,tunanin halin da zainab kawai take ciki yakeyi…har suka nufi airport suka hau jirgi,sukabar Lagos…Ahankali ta bud’e Idanunta tana k’arewa d’akin kallo! Inna lillahi wa inna ilaihir raju’un “ta furta azuciyarta sbd tuna abinda yafaru”dakuma ganinta ad’aure kanta bbu d’ankwali dg ita sai doguwar rigar baccinta me dogon hannu da kad’an ta wuce gwiwa! azuciyarta ta furta lallai wad’an nan mutane basuda Imani sbd ganinta datayi k’asa ,cikin wani d’aki sai wari (d’oyi) yakeyi…k’uuuuuuu! Cikinta yyi! alamar tanajin yunwa” gaba d’aya kuka takeson Yi,amma yak’i zuwa, tambayar kanta take marfarkine take kokuwa?” Tashin hankalinta shine ,tana on( period)bama wannan ba ,shin meyasa mutanen dasuka d’aukota sukeson ace hjy suka d’akko?? gabanta yafad’i sbd jin motsin annufo d’akin!rufe Ido tayi tana addu’o in neman tsari azuciyarta…
Su 3 ne suka shigo fuskokinsu arufe….yo ai bata tashiba ko?” Eh Amma cikin irin wannan lokacin zata tashi Dan ubanta tagamana ita wacece data b’ata Mana aiki! Munso ace tsohuwar suce muka d’akko…cewar wani k’ato ,cikin muryarsu ta k’atti! Yo ai ogah damuka sanar Masa yace k’ila k’anwarsu DSP ce !….inbacin addua bbu abinda zainab keyi azuciyarta! Kafin ta Fara motsi had’e da bud’e Ido…suka Mata k’uri da Ido…guda Kai Amma gsky bayan komi yalafa Dole na huta da yarinyar nan sbd tanada Kira… zainab ta zaro Ido cike da tsoro…tsaki d’aya yyi yace Kuna Bata Mana lokaci wlh Kama Yi shiru Kar ogah yajikah!
Keeee! Babban cikin su yafad’a ,Yana zare Ido had’e da matsawa kusada zainab,,yace kifada Mana kewacece agurinsuDSP?” da har muka dauko ki,amatsayin uwarsu ce muka d’akko ,bacin antabbatar Mana da cewa nan ne d’akin baccinta! zainab tamkar tayi amai sbd irin d’oyin dasuke,yacikamata hanci”sai kallonsu take tana zare Ido…ke Dan uwarki bazaki yimana mgn ba?” ah ah kabarta inmuka Mata fyad’e muduka tamana bayani….hawaye suka zobo Mata afuska,tana girgiza Kai…ta musu alamar bata mgn suyi hakuri….wani wawan mari guda yad’auketa dashi ,atake hancinta da bakinta suka Fara zubar jini…awahalce ta dafe Gurin da hannunta dake ad’aure had’e da sulalewa ta sume…????????
Tunda suka hau jirgi DSP ALIYU haidar ke faman voice call da video call har suka iso Abuja,yyinda faruq har Rama yyi,idanunsa sunyi jajir mgn inba doleba bayyi,shikansa DSP yadamu sosai sbd yasan da yarinyar batayi hakaba , mahaifiyar su ce zaa d’auka,Dole kuwa yaje ya k’watota Koda hakan zaiyi sanadin rasa ransa!
Suna fitowa dg jirgi, DSP yadafa kafad’ar haidar yace ,kada kasausari abokan aikinka(Yan jarida) sbd ganin sun nufosu Dan labari har yafara yad’uwa!kowane fuska atamke suka nufi mota…ko parking baa gamaba faruq yafito da sauri yyi waiting parlourn gdn….hjy na zaune da elham kan cinyarta tana bata shayi….kallo guda zaka Mata kasan tana cikin tashin hankali! gefe guda Kuma anty mariya ce keta kuka tamkar k’aramar yarinya…sbd da dare sunji k’arar harbin bindiga,hakan yasa byn angama sallar asuba baffa sule yatambayi Mai gadi lfy?” Shine yasanar Masa….
Arikice faruq yashigo bbu ko sallama! Hjy ta dubesa…kafin tayi mgn haidar ya shigo….kallonsu yyi kafin ya matsa kusada hjy yakama hannun ta!cikin taushin murya yace hjy Dan ALLAH kiyi hkri insha ALLAH indai Ina numfashi to zainab zata dawo lfy” duk abinda yakamata zanyi ! Bazasu tab’a Zama lfy ba ,sunyi sanadin xubar hawayen mahaifiyata… Hjy na hawaye tace insha ALLAH saikayi nassara ALIYU!; zainab Kuma ALLAH ze tsaremana ita…faruq tamkar karamin yaro yafad’a jikin hjy yanata surutai…Koda haidar yaga haka,sai yadubi anty mariya ,yyi gyaran murya had’e da cewa amm anty Dan ALLAH karki sanar da kowa na zainab ! but muyita addua banaso hankalin kowa yatashi ko amuku zaton Baku rik’e ta da gsky ba”…..anty mariya ta share hawaye tace to shikenan Y’allab’ai nima nayi wannan tunanin shiyasa nacewa baffanta yyi shiru muga abinda ALLAH zaiyi…tashi tsaye DSP yyi yace eh kutaya mu da addua….yadubi hjy yace zanshiga ciki ,yanzun zanfito pls kidena kukan haka addua zamuyi…Dole nayi kuka zainab tagamamun komai arayuwata tunda tasaida ranta sbd ni! Koni na haifi zainab iyakar abinda zatamun kenan! Faruq yatashi yabi bayan haidar…
Yunifoam yake sakawa,wayarsa tayi ringing…yaduba yaga private number… faduwar gaba yaji….amma saiya dake”
d’agawa yyi
beyi mgn ba! yyi shiru….to sarkin izzah da d’aga Kai !bazakayi mgn ba saikayi shiru! hhhhhhhh???????? Dole kayi shiru! To bari kaji nasan kaji dad’i daba mahaifiyar ka muka d’akko ba ko?kaiiiiiiiii!wake mgn ?DSP yafada, cikin dakakkiyar muryarsa me saka maraji natsuwa!bamu saniba ,aikafi sani , k’anwar kurma ce?” Taki mgn tana hannunmu,munfara koya Mata hankali…kashiga what’s app d’inka zakaga pic nata… sannan munason ka kamana ko ka aiko Mana da miliyan20…shine fansan ranta ,in aka wuce gobe baa kawoba zamuyi Mata fyad’e….. sannan ka gaggauta sakin Alh buba ko mu kashe yarin…. kaiiiiiiiii!wawah shout up ! Kundad’e bakuyi abinda kuka fad’a dinba,but saina baku mamaki….dit yakashe wayar…kafin yatsaida recording din muryar k’aton da yyi…..tayi seving ,kafin yakira amintaccen yaronsa ,yusuf dake Masa traking d’in numbers ko location…da sauransu…yace yazo nan gd yasameshi…yyi recodings din muryarne sbd kamar yatab’a jinta awani guri…
What’s app yashiga,nanma yaga b’oyayyar number…ta turo sako…da sauri yabud’e….zaro ido yyi ganin photon..zainab kwance k’asa ad’aure , dg itah sai doguwar riga,Kai bbu d’ankwali ga uban tulin gashinta nan !bakinta da hancinta suna jini…da alama ma suma tayi…
[9/27, 5:55 PM] Mmn fareesa: Wannan littafin na kud’ine! dan girman ALLAH inkingani karki karanta ,kar ki turawa kowa..duk Maison siya yakaranta…yaturo Airtel na300 ko MTN na 300 ta wannan number 08100084251…bamasan transfer d’in Kati,kiyi pic ki turo…ko Kuma kitura kudin 300 ta account number kamar haka..0089110527 suwaiba Hussaini zakirai access bank!saikiyi creen shot ki turo shaidar kin biya….