Uncategorized

WAYAFI SONTA 13–14


 P13

….Shigowa matan d’azun sukayi suna duba jikin matar ! yyinda k’irjin zainab ke dukan ???? ???? ta juya Kai tadena kallonsu…

Jitayi guda tace wlh da waya muka ajiyeta Ashe ?”d’ayar tace Kai gara damuka dawo dai ,inda ta farka taganta Aida matsala wlh….nan suka dauki wayar suka fice… zainab ta yi ajiyar zuciya,fatanta ALLAH ya Toni asirin wad’an nan mugayen mutane…,,,,

 

   Zaune take tana lazimi bayan tagama shafa’i da wutiri! taga wayarta tayi haske alamar shigowar sak’o!da Kamar ta share,sbd azatonta ko MTN ne! saikuma ta duba taga new number…atake tamik’e tsaye  tana zare Ido Akid’ime sbd karantawa datayi!bbu Bata lokaci da gudu tamkar yarinya ta nufi part d’insu hjy…adede lokacin Kuma DSP driver d’in sa,yyi parking DSP yafito fuska bbu walwala sbd abinda yafaru astation d’azun…part d’in su yanufa cikin sa’a sukayi clash da anty mariya!

Da sauri anty mariya jiki na kirma  tace DSP gashi kaduba zainab ce ta turomun shi yanzun…kallon anty mariya yyi yakarbi wayar yakaranta….yasaki ajiyar zuciya yace alhmdllh afili Yana murmushi had’e da matsawa dg bakin k’ofar shiga waiting parlour….yacewa anty mariya matso muyi mgn!.

Babu musu sukayi d’an matsa baya  ,yace abinda  nikeso dake pls! Karki gayawa kowa sakon da zainab ta turo sbd Kinga hjy hankalinta zai tashi tace bazanje nid’aya ba ,Dole Saida wasu…hakan zaisa maganar ta fita waje har wasu suji asami matsala…yasanar Mata abinda yafaru astation d’azun akan kisan biliya…kafin yace Kinga hanyar ALLAH Mai yawa inbacin 9:pm tawuce da yanzun zamuje…ajiyar zuciya anty mariya tayi had’e da cewa insha ALLAH bazan gayawa kowa ba,bara na goge sakon ,naje nayita shaidawa ALLAH ! ALLAH ya baka saa…yace ameen had’e da wucewa ciki…

Bbu kowa a parlourn hakan yasa ya nufi part d’in abbansu sbd shima yadawo d’azun da safe akan maganar zainab…

 

Kwana anty mariya da DSP sukayi suna shaida wa ALLAH akan samun nassara ,bbu Wanda yyi bacci acikinsu! Koda yagama sallar asuba da azkhar yashirya cikin suit baka k’e yadauko hular kwano ,yafito da ita da bindigogi yaje  yasaka  aboot din motarsa kafin yakira , commissioner yace yashirya Masa police guda 30 ,zasuje wani binkice,susamesa aget din shiga anguwarsu…ciki yakoma bayan yagama wayar ,yaje yagaishe da iyayensa….kafin yafito…

 

Acikin mota yasaka hular kwanon byn sun dauki hanya,kasancewar motar da DSP yake itace gaba sauran binsa suke abaya suna mamakin Ina zasuje..

    Sunyi kusan tafiyar awa2 tukum DSP yasaka Yusuf yyi tracking number d’in da zainab ta turo sak’o…..atake sukaga alama anan wuraren wayar take…Yusuf dake zaune a front sit  yadubi DSP dake driving yace y’allab’ai anan Gurin gsky wayar take sannan Kuma ba rufe takeba akunne take… DSP yagangara yyi parking !sauran motocin suyi parking abayansu…yadubi wata gada tsohuwa wacce dg ita sai ruwa shine k’arshen gari…Jan Yusuf yyi  suka nufi Gurin gadar….Yusuf yafara searching…kallon DSP yyi yace anan Gurin akwai mutane dasuke rayuwa samada mutum 20 a nan Gurin..DSP yace ba shakka anan suke!abinda za’ayi bara na Fara shiga dg baya saiku biyoni ,kaje kasanarwa sauran ka gane?”eh y’allab’ai! Okay bara naje kasa narmusu yadda zasu fahimta….kokuma dakunga flashing nawa kushigo… Cewar dsp …..da addu’o in samun nassara DSP yatsugunna dg wani Rami ya lek’o cikin gadar kafin yyi bissimillah  yashiga wajen da bindiga guda ahannunsa d’aya cikin jikinsa yab’oye!

    Koda yashiga yaga irin datti da k’ura hardasu ledoji na shara bbu Wanda zai dubi Gurin yace mutane zasu iya shiga k’asan gadar….kasancewar akwai k’asa agurin sai yarik’a takawa sosai sbd insauran sunshigo suga takun sawunshi…can k’arshen filin Gurin yaga wata hanya hakan yasa yabi hanyar cikin k’warin gwiwa…by surprise Yana shiga hanyar yaga k’oface kad’an yalek’a yahango wasu arnan katti ,majiya k’arfi da makamansu a hannu suna Roman about a filin Gurin, da alama filin kamar tsakar gd yake…tunda ga k’ofofin d’akuna nan acikin filin… flashing yyiwa Yusuf…kafin DSP ya lek’a sosai cikin dubara..yasaita daidai gwiwar wani k’ato ya harbesa….jikake tush! arud’e k’attin suka juyo suna kallon inda akayi Harbin…Basu ankaraba sukaga ansake  harbin mutum2…tuni suka Fara guduwa sbd bbu bindiga agurunsu… adedenan Kuma Police d’in suka iso suka Fara Harbin mutanan dake Gurin”

Zainab!tunda taji anyi harbi ,tasan tabbas DSP yabaiyana ta lek’o ta  taga ,dukda yasaka hular kwano Saida ranta yabata shine…

   Gaba d’aya Gurin yahargitse , wad’an da akayi kiddnaping d’in su wasu sun fito suna son guduwa hakan yasa mugayen suka Fara sajewa dasu…

Zainab da matar da aka kawo jiya suna kokarin fita! Wani mugun k’ato yashak’o wuyan zainab Yana cewa kasheki zamuyi sbd sanadinki asirinmu zai tonu.keba k’anwar DSP ko?”…d gudu matar da aka kawo jiya tafita dg d’akin…tana fitowa Kuma taga DSP da bindiga ahannunsa yafito dg wani d’aki…kallo d’aya ta Masa taganesa sbd ansansa adaline dukda baa ganin fuskarsa…kaje yace zai kashe k’anwar ka! arikice DSP yace inane?” Tanuna Masa d’akin da hannu…da gudu yashiga… d’akin yasami k’aton ,suna tsaye shida zainab ,Yana bayanta ,tana gabansa  ya azawa mata wuk’a ga wuya…koka aje bindigarka ,kacire hular kwanan nan ko na yanke Mata Kai… inna lillahi wa inna ilaihir raju’un!DSP ya fad’a Yana aje bindigarsa, yyinda zainab ke hawaye ,tayi bak’i ta rame acikin kwana2″kallonta yyi yaga bbu ko d’ankwali akanta sai rigar baccinta da kad’an ta wuce gwiwa….kallonsa DSP yyi yace karka Mata komai na rok’eka! Yafad’a Yana maida hannunsa guda ta baya ya zaro bindiga a aljihunsa…dariya k’atan yakece da ita! yace ikon ALLAH kaida kanka ka ke rok’on wani akan karyyi kisa ,bacin yanzun ka kashe abokan aikinmu sann…kudakata Yusuf kar…da sauri k’aton yakalli inda DSP ke kallo Yana mgn….da sauri DSP ya zaro bindiga ya harbe kan k”aton….zaro Ido zainab tayi had’e da wurga wukar k’aton dayasaki k’asa Gurin DSP! Da sauri DSP ya juya yaga wani k’ato ne zai sareshi da wuk’a zainab ta gani…ta wurga wukar k’aton daya mutu,wukar wancan tafadi,shima yafad’i sakamakon wasu police dasuka harbesa suna shigowa d’akin… k’uri da Ido DSP yyi Yana mamakin jarimtar yarinyar da basirarta…da gudu zainab tazo tafad’a jikinsa tana hawaye….sauran police d’in suka had’a baki gurin cewa alhmdllh!shiru DSP yyi Yana shafa kan zainab,dake kuka…wani iri yaji sbd wannan karanne na farko da mace da rungumesa arayuwarsa…janyeta yyi dg jikinsa batare da yakalletaba yacire suit din jikinsa yakama hannun ta yasaka Mata…kafin yadubi sauran police d’in yace kuje afitar da matacci da masu rauni..akuma duba sauran d’akunan Koda akwai mutanen dasuka Kama…cike da girmamawa suka amsa suna ficewa…kallon zainab yyi yaga tasaka suit d’in… handcheef yafito dashi Mai girma yadubeta suka had’a ido….tajanye idonta,batare da yyi mgn ba yamika tattausan hannunsa yagoge mata hawayenta had’e da yafa Mata handcheef d’in bisa Kai yarufe Mata gashi! Dukda baduka yarufe ba..yakama hannun ta suka fito dg d’akin…

 

Sadda suka fito anata fita da masu rauni da matacci” DSP ya dubi Yusuf yace Zan wuce gd sbd suganta hankalinsu ya kwanta…kuyi duk abinda yadace…okay Sir! Cewar Yusuf cike da girmama!

Zainab kuwa biye take dashi tana mgn cikin zuciyar ta Ashe DSP Yana da mutunci haka?”sannan Kuma tanajin haushin kanta akan rungumesan datayi,saidai wani b’angaren zuciyarta na shaida Mata ai sbd jin dad’in sun kubuta ne ta rungumesa….wayar DSP tayi ringing ! Dubawa yyi had’e da dagawa yace abokina saukar yaushe?”eh wlh kabari kawai harkun Sami labari!Wai da gske kake ?”to Ni bbu Dan jaridar dazan saurara… DSP ya fad’a cikin muryarsa me dad’in sauraro….Ida fitowa sukayi…suka Sami Gurin mak’il da jamaa ,da Yan jarida!

Fuska atamke had’e da had’e girar sama da ta k’asa, DSP ya ke ratsa mutanan Yana rik’e d hannun zainab ,suka nufi Gurin mota”

Yana bud’e motar da nufin zainab ta shiga “shigewa tayi zata rufe marfin sukayi Ido hud’u da faruq daketa kallonsu…..

 

Kuyi hakuri da kad’an Gurin 10 what app d’ina zeyi update shiyasa ! Sai zuwa gobe insha ALLAH innacanza wani…

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button