WAYAFI SONTA 16

Page 16
*India*
Tun acikin jirgi zainab ta Kama kanta” duk abinda aka bata bataci…yyinda Dr Kamal da faruq ke lura da ita!
Koda suka sauka ak’asar , straight hospital suka nufa , kasancewar Dr Kamal yasani sbd anan yake aiki ,byn wasu watanni yaje gd…hutu yadawo….. zainab dai sai kalle kallen ta takeyi ,tana mamakin Wai yau itace a India…tabbas tayi k’auyanci “Amma àzuciyar ta!d’aki 2 akabasu! Zainab 1 sai su2 guda..Cikin ikon ALLAH byn anbinciki zainab aka azata kan magani!
Yyinda faruq Yana waya da mutanen Abuja suna jin labarin komai har zuwa yau ,da ake Shirin shiga da zainab d’akin aikin…
Tsaye zainab take da rigar da ake sawa in za’a shiga aikin..Dr Kamal na gefenta , kasancewar hardashi za’a Mata aikin…faruq kuwa Yana zaune yanata kallonta ganin yadda dukta damu ,idanunta cike da k’wallah! Kiyi hakuri zainab insha ALLAH za’a samu nassara kidaina jin tsoro”kinji?” Cewar faruq Yana kallonta!
Kamal yadubesa yace Ashe kaima kalura da tana cikin damuwa?” Eh wlh Yaya Kamal!
Zainab dai na saurarensu har suka gama surutunsu ,sukajira sauran doctors d’in aka shiga da zainab cikin theater room d’in…
Alhmdllh Masha ALLAH! anyi aiki cikin nassara dukda zainab dai Bata mgn amma doctors sunce ,bada anyi aikinba zata Fara mgn”. sun azata kan magani, yyinda zainab jikinta yyi sanyi azatonta ko dai bazata sake mgn ba!
Shikansa faruq yarasa me zaicewa su hjy da anty mariya da ke kiransa danjin Yaya da nassara
Ko Babu?”sai dai yace musu ai zainab d’in nagun doctors tukum su saurara….
Ayau yakama su zainab zasu tafi gd Nigeria” yyinda zainab jikinta yake asanyaye “har yawo faruq yace Mata suje” waidan taga gari ,tarage damuwa da kad’aici…amma fafur tak’iya”
Suna zaune acikin jirgi! Wayar Kamal tayi ringing yad’aga! Naji yace Muna hanya ai! Eh wlh har yanxun” pls karka damu komai zaizama normal insha ALLAH… Dg faruq har zainab kallon Kamal kawai sukeyi” yyinda suke mamakin to dawa yake waya Wai?”
Saidai tambayar sa b ahuruminsu bane musammun zainab ma…
Koda suka sauka driver d’in DSP ne yazo yad’aukesu !
Dg faruq har zainab kowa gabansa faduwa yakeyi”akan rashin nasarar aikinta…da wannan tunanin sukazo gd….jiki asanyaye zainab ta fito dg mota tabi bayan faruq suka shige waiting parlourn gdn…da gudu elham tazo ta rungume zainab tana dariya had’e da cewa I miss you so much anty zainab?”granny tace bakinki ya warke ko?”girgiza Kai zainab tayi hawaye na zuba afuskarta…da sauri faruq yajanye elham hjy ta taso takama hannun zainab suka zauna gefen kujera “
Ahankali hjy tace Masha ALLAH zainab karki karaya duk Mai nema gun ALLAH baya karaya”nassara nazuwa tunda likitoci sun tabbatar insha ALLAH zakiyi mgn to damuwar me zakiyi?” D’azun munyi mgn da mamanki ,nama nuna Mata kunacan India sai sati nasama zaku dawo! Nasan uwa da k’ulafucin d’anta “nasan ta k’agara ,sanar Mata yanzun hankalinta zai tashi zainab!
D’aga Mata Kai zainab tayi…kafin hjy tayi mgn anty mariya tashigo” tazauna gefen kujera tanama zainab sannu da zuwa had’e da nasiha… k’amshin turaren sa taji yadaki hancin ta!da sauri zainab ta d’ago”sanye yake da farar shadda riga da wando” rigar batakai gwiwa ba,kansa bbu hula yasha gyara sai salki yake”fuska atamke kamar kullum”da sallama suk shigo shida amininsa Dr Kamal!
Had’a ido sukayi shida zainab” tanamamakin ganinsa da manyan kaya”atake zainab ta had’e Rai had’e da wurgomasa harara! Sbd tunawar datayi dan maganganin daya yab’a Mata aranar dazasu tafi..dukda k’udirinta nan na barin gdn in ankwana2..
Cike da mamakin yarinyar DSP yazaro Ido had’e da nuna Mata kansa” alamar shita harara?” Bbu kunya zainab ta d’aga Kai”
Hakan Kuma yafaru akan idon kamal dake rusunawa suna gaisawa da hjy” yyinda dsp yak’i Zama parlourn sbd jin haushin zainab” dukda yyiniyar Zama….part nasu ya wuce…bayani sosai Dr Kamal yyiwa hjy gameda matsalar zainab yakuma kwantar Mata da hankali….kafin yatashi yabi DSP…
Zaune yasamesa kan kujera ya’aza k’afafun sa kan center table” Yana girgiza su idonsa arufe”Zama Dr Kamal yyi agefensa,yyi gyaran murya had’e da cewa my man how fer?”
Guntun tsaki yaja had’e da cewa bbu komai kasan sha’anin aiki!…dariyar rainin hankali Dr Kamal yyi had’e da cewa ranar nike jira yau gashi tazo wlh!
Harararsa dsp yyi “yace mekake nufi da zancenka?”
Eh abinda Nike nufi kanason zainab yarinyar nan” koka yarda ko karka yarda Amma wlh kana mugun SONTA! Inbason ta kakeba ,minene abin kabiya Mata kud’i amata aiki Amma ka b”oye kace Alh ne yabiya dukda nasan halinka inkayi taimako bakasan asani”sannan meye dalilin ka nayawan kirana gameda jin lafiyarta,dakuma nuna tsantsar damuwa akan ba’ayi nassara ba ???”sannan yanzun aparlour Ina lura daku Kuna tsokanan juna!
Kagama labarin k’aryan?” Cewar DSP Yana yatsina fuska..murmushi Dr Kamal yyi yace nasan zakace abinda yafi hakama,tunda baka tab’a son wata mace ba ,saidai Kai asoka! Da alama itama tana sonka…dallah malam in wannan surutun banzar yasaka kabiyoni kayi gaba”baka Kuma canka daidai ba,ni banasonta,kawai dai na tausaya Mata akan kiddnaping d’in ta da akayi sbd ta tseratar da mahaifiyata da duk duniya nafi so da k’auna…bacin hakan bansan komai ba,zankuma yimata hukuncin hararata datayi… yafad’a Yana tashi tsaye yashige bedroom dinsa…
Murmushi Dr Kamal yyi sbd yafi kowa sanin halin DSP ! Hakan yasa dg shi dai saif suka d’aine abokansa na k’ud da k’ud suma suna hakuri dashine….tashi tsaye Dr Kamal yyi yace ALLAH yakyauta….yanufi k’ofa da sauri faruq yyi baya jikinsa asanyaye sbd yaji duk maganar da yayansa da amininsa sukayi…Koda Kamal yahansa bekawo komaiba yyi Masa sallama yawuce…
***************
Yau kimanin kwana 3 da ,dawowar zainab dg India!Zaune suke itada anty mariya” suna fira dukda zainab nacan duniyar tunanin labarin da anty mariya ta bata Wai DSP ne yabiya Mata kud’i aka fiddata waje….gaba d’aya jikin zainab yyi sanyi” sai yanzun take Dana sani da nadama akan abinda tamasa rannan, sannan bata mance lokacin da yatarbe kunu yak’ onasa sbd ita! Gsky bata kyauta” Dole taje tasamesa tabashi hakuri kawai….hawaye taji sunxubo Mata afuska…da mamaki anty mariya tace ke lfy kike kuka?”
Wai zainab bazaki k’ara hakuri ba! Kinsan me ALLAH ya tanadar Miki?
Girgiza Kai zainab tayi! kafin tawuce d’aki Jim kad’an ta dawo da paper ahannunta ta mikawa anty mariya….karb’a tayi had’e da karantawa” Baki kyautaba zainab meye dalilin ki na hararar babban mutum kamarsa ?” DSP ba yaro bane wlh inda auren wuri aka Masa yahaifeki ,” dudu shekaranki20 shikuwa 40 years garesa! Zaro Ido zainab tayi”azuciyarta tace nadauka be wuce 34 years haka…kije kibasa hakuri nagaya Miki ,inkuma kinason yamiki kallon marar kunya da tarbiyya to! Tashi zainab tayi tama anty mariya sallama ta koma part d’in su hjy….
B’angaren faruq kuwa tunda yaji firan Dr Kamal da DSP ,yyi dogon nazari da hangen nesa”wato Ashe shine ke yawan Kiran Kamal yaji ya jikin zainab, sannan ya lura inyaganshi tare da zainab yake d’aure fuska! Yatuna lokacin da yadakko zainab sadda aka yi kiddnaping d’in ta” Yana rik’e d hannun,,Kuma suit nasa ajikinta! Tabbas yayansa nason zainab” Dole yahak’ura ya yakice zainab dg ransa,Amma harga ALLAH ya na SONTA da k’aunarta!Amma bazaiso macen da yayansa kesoba,sbd yalura shi har yanzun DSP be yarda son zainab yakeyiba”saidai k’arshe irin wannan soyayyar tafi zafi da wuyar rabuwa ,dakuma illah…inkuma suka had’a kansu to zasu buga love! Dole yahak’ura da ita kawai! Yana k’aunar d’an uwansa dabeda kamarsa aduniya” dg yanxun zaikoyi mgn da ita bbu murmushi ko wata mgn dake nuna Yana SONTA!saidai kawai agaisa…
Wanke wanke takeyi tana atsaye a kitchen!tana cikin wanke wuk’a cike da tsautsayi ta yanke…. innalillahi! Ta furta afili” waininayi mgn?” Cewar zainab Akid’ime tana zare Ido Dan son tabbatar wa! Alhmdllh Alhmdllh!! ALLAH nagode maka….Nike mgn da bakina ni zainab?
SaiKace nafarki” tafad’a tana d’aure yatsanta da wani k’yalle….aje kayan wanke wanken tayi ta fito dg kicin d’in tana murmushi…. adedenan Kuma DSP ya shigo waiting parlourn gdn….suna had’a ido da ita!ya k’ara tamke fuska ,yabi tagabanta ya wuce….YAH HAIDAR! tafad’a cikin siririyar muryanta….da sauri DSP ya juyo Yana kallonta cike da mamaki saidai bai nuna afuskaba sbd tsabar miskilanci”saikuma yatunada Kamal yace zatayi mgn insha ALLAH to yaushe tafara maganan?”
Juyawa yyi yayi tafiyar sa….waigawa tayi taga bbu kowa da sauri tabi bayan sa….
Murd’a k’ofar tayi ta shiga baya parlourn” knocking d’in k’ofar bed room d’in tayi sau 2″afusace ya bud’e sbd bemayi zaton itaceba,azatonsa wanine cikin security d’in dake bakin get! Dg shi sai farar vest da wandon yunifoam, kasancewar Yana cire rigar tayi knocking…Koda yaga itace sai ya k’ara had’e Rai yace lfy malama?”
Kallo d’aya tamasa tadauke Kai…. ahankali tace Yaya haidar kayi hakuri Dan ALLAH bazan koma ba”kayafemun…yamutsa fuska yyi yace akanme zanyi hakuri?”kinmun wani abune?” Inma kinyimun to fad’a mun naji”zainab azuciyarta tace gsky mutumin nan akwai son yarfa mutane….Kai duk’e tace na harareka ranar da muka dawo dg India! Murmushin gefen Baki yyi kafin yace meye dalilin ki na hararata ?” Ni sa’ankine?”ah ah pls kayi hakuri…bazan komaba!
Kinason nahakura ne?” Da sauri tace eh”
Sai kin fad’a mun abinda namiki har yasaka kika harareni tukum ,Zan