Uncategorized

WAYAFI SONTA 18

 


Page 18

 “””d’aga Masa Kai tayi alamar eh sunb’ata d’in”Yaya muje ko ! Cewar faruq Yana yin gaba “biyosa DSP yyi,gab dazasu fita yajuyo”ya yafito zainab da hannu akan Wai tazo… d’age kafad’a tayi alamar bazatazo ba”kansa yanuna Mata Wai shidaiko?”eh tamasa alama…tana juyowa sukayi Ido 4 da hjy” cike da jin kunya zainab tayi k’asa da kanta! Hjy tayi murmushi had’e da jawo musu wata firar sbd zainab d’in tasake tasanta da kunya…

     Tsaye take a kitchen gaban gas cooker tana soya manya ” bayan ta tsane farar taliya y’ar hausa!gaba d’aya tunanin haidar ne da maganar yarinyar da akace zatazo gobe aranta…. zainab dama kina anan?”sanyayyar muryasa ta katsemata tunani! ahankali tace eh   Mana !shine katsoratani ko?”uhum kin cika tsoro wlh”meye kike girkawa?”

    Taliya da manja da yaji! lallai badaniba! Bazakaci bane?” Eh sbd akwai yaji”kanada ulcer ne?”ah ah “

To nidai gsky saikaci! tafad’a cike da shagwaba abinda bata tab’a yimasa ba”ya lumshe Ido ahankali yace banfa tab’a cin taliyar da yajiba dadai girmana bansan ko abaya ba”

Shine nace saika Fara dg yau ,Kuma yanzun ko?”uhum ni ruwan zafi tafashashshe nazo kibani zansha..

 

    Wata tukunya ta dauraye a sink ta aza kan gas d’in “Yana tsaye ta rufe ,kafin tazuba manja kan taliyar ,tajawo wani bowl dake gefenta ta bud’e”latuce ne da tumatar da tingande”ta zuba akai”ta aza spoon,kafin ta dubesa taga ita yake kallo”

   Ahankali tace to yanzun yagani tayi?”bbu laifi saiki faraci ko?”

Batayi mgn ba,tajawo flux ta juye ruwan zafin takashe gas d’in” batare data kallesaba ta mik’a Masa flux d’in….bazan karb’a ba sai kin kalleni”fuska bbu walwala tadubesa had’e saurin janye idonnunta akansa..

     Miye abin fushi anan pls?”cikin murmushin yak’e tace fushinme Kuma?uhum zainab kenan”akandai taliyane ko to naji zanci shikenan kindena fushin?”turo baki tayi had’e da cewa” nima d’azun bakayi fushi daniba”yauwa kin tunamun ,Kinga sainayi  purnishing naki ko?”yafad’a Yana Jan kujerar dake cikin kitchen d’in yajawo plate d’in taliyar ya aza kan table yadube ta zo muci!zaro Ido tayi had’e da cewa bazan iya ba “gadai yaji kaci Kai d’aya”tafad’a tana ajiye Masa yajin kusada plate d’in”

Ok to shikenan tunda bakyason naci taliyar ko kuwa inada wani aibu dabazaki iya cin abinci daniba?”

Nidai wlh ba haka bane “inwani yashigo yaganmu fa?” Za’a iya yimana wata fassarar” bece komaiba yatashi tsaye yadauki flux d’in ruwan zafin yyi waje….be juyoba yanajin Kiran da zainab kemasa da magiya….taliyar da zainab kenan bataci ba! d’akin su Takoma tayita kuka har aka Kira isha’i…tayi Sallah!

Tunani takeyi tabbas soyayyar haidar nashirin kutsawa azuciyarta ,tana Kuma zaton shibaya sonta,inhar yanasonta miye abin fushi Dan tace bazaci abinci dashiba!Wani kuka yakubce Mata sbd tuna Yaya Umar tasan shibaya fushi da ita”afili tace nayi rishi babba”

    ALLAH ya jikanka yah uwar”Dole natakawa zuciya ta burki gameda Yaya haidar…..motsin shogowar elham yasakata yin shiru tayi saurin goge fuskarta…amma Ina elham tagani”da sauri tace lahh anty zainab kuka kikeyi?”waya dakeki ne?”

Ba kuka nakeba ,bana lfy kaina ke ciwo…to bara na anso Miki magani….batajira cewar zainab d’in ba tafice da gudu duk da zainab ta so tsayar da ita..Da gudu elham ta nufi bed room d’in hjy!

Wacce suke sallama da haidar yazo yimata Saida safe”granny,!! anty zainab kuka take yi sbd kanta na Mata ciwo….dg hjy har haidar sukabi elham da kallo”hjy tace subahanallahi! To bara naje na kai Mata magani! tafad’a tana jawo bed side drower ta fito da Panadol tafice….

Haidar kuwa ! Mamaki yakeyi meyasa zainab take kuka?” Koda gaske ciwon kqnne?”to kawai saita Kama kuka sbd kanta na ciwo!

    abinda yafaru d’azun yatina koshiyasa take kuka….tsaki yaja daya tuna zainab batada waya dasai yakira yaji meke faruwa ne?”

Kuma shi bazai iya zuwa d’akin suba kodan sbd parrot elham”

Fitowa yyi yanufi part d’in su” byn yyikomai ya kwanta had’e da Kiran Yusuf(amintaccen yaronsa)yasanar Masa yanzun yaje yasiyi sabuwar waya tochscreem da sabon sim card da safe yakawo Masa!kafin yakwanta da tunanin abinda ke damunta har bacci yyi awon gaba dashi…..

 

 

    Washe gari zainab bata fitoba sbd jiya batayi baccin kirkiba sai asuba tayi bacci”hakan yasa Bata fito Taya hjy aikiba” yyinda hjy bata damuba Dan tasan zainab bata lfy!sai tadamu tanaso Inta Gama abinda take taje taji Yaya jin nata…

    Zainab kuwa sai 9:30 ta farka ,ahanxarce tashiga toilet tayi Wanka ta shirya cikin doguwar riga gwont maroon colour” kwalli da powder tashafa da turare,! Takalli kanta a mirrow taga fuskarta tayi fiyau da ita ,tayi haske ,Amma idanunta harsun kumbura sbd kuka…..rolling d’in kanta tayi” kafin ta fito waiting parlour” anan tahad’u d hjy suka gaisa ta Mata yajiki, had’e da cewa taje tayi break fast nata…

Tea ne kad’ai Tasha ta koma d’akinsu..

     DSP kuwa tun 8:30 am Yusuf yaka Masa wayar zainab spark 5 ” sannan yaje yashirya cikin parsonal dressing yaja laptop” Yana aiki amma gaba d’aya hankalinsa yatafi Gurin zainab”time yaduba yaga har 10 ta wuce ko break beyiba….tashi yyi sbd yanada wani case astation d’insu dukda week end ne amma Dole yaje!

Jiyayi baya bukatar cin komai yau!

Fitowa yyi a parking space yasaka driver d’in sa yagoge Masa mota” Yana tsaye saiga faruq da elham sun shigo gdn da alama wani guri sukaje….faruq yace badai fita zakayiba Yaya?” Fita zanyi wlh! Taf nikuwa baccima zanje nayi wlh” inmutum be huta a week end ba saiya huta yaushe?” Ni wlh aikin nan naka yafara isata bbu hutu kwata kwata… murmushi kawai DSP yyi Yana kallon elham yace my baby zokiji! ahankali yarad’awa elham akunne kije gun anty ki zainab kice nace tazo taji inanan bakin get ” Amma ita kawai Zaki fad’a mawa….da gudu elham ta tafi tana dariya” yyinda faruq yyi murmushi yawuce abinsa…

Zainab kuwa tana d’aki tana karatun alk’ur’ani me girma”elham ta shigo da gudu tasanar Mata aiken DSP….Saida takai aya tukum tarufe alk’ur’anin “jitake tamkar kartaje Amma zuciyar ta tahanata hakan!

     Tashi tayi tana cewa elham suje”elham tace ah ah yace karna biyoki” zainab shiru tayi ,saikuma ta fito kawai bbu kowama awaiting parlourn…

 

 

Tundaga nesa yake ta k’are Mata kallo,Yana jingine jikin mota!Saida takusa isowa yalura da fuskarta , idanunta sun kumbura…yah rabbi ! Yafurta Yana kallonta.

Nesa dashi ta tsaya…cikin dashashshiyar murya tamasa sallama had’e da cewa Ina kwana?”arikice yake dubarta dukda be nuna hakan afuskaba, cikin wani yanayi batare da ya amsa gaisuwar taba  yace zainab meke faruwa ne?”idanunki sunkumbura sbd kuka,Mesa kika kwana kina kukane?”

Girgiza Kai tayi wasu hawayen nazuba a fuskarta! Kinga shigo naji meke damunki pls! Yafad’a Yana bud’e gdn baya yashiga! K’in shiga tayi,Kuma batada alamar shigar!

Zainab ! Yakira sunanta,kinaso mu b’ata dakene?” Girgiza Kai tayi” ok to kishigo Kona shigo dake ciki.. ahankali ta shigo ta zauna gefensa ad’od’ane”matsawa yyi sosai yace ki shigo kizauna awale Mana!

Matsowa tayi kad’an ,kafin yace oya inajinki pls tell me ! Kanta aduk’e tayi shiru”

Wanene yasaka ki kuka ko Baki lfy ne?” Girgiza Kai tayi alamar ah ah,keda hjy ne ko elham?” nanma ta girgiza Kai!

Nine?” da sauri ta d”aga Masa Kai! Subahanallahi”yaushe nayi laifi bansani ba”har nasaka y’ar lelen hjy kuka?”yanxun kiyi hakuri kigamun Mena Miki….turo Baki tayi cike da shagwaba tace bakai bane jiya kayi tafiyarka k’aki saurarata kayi fushi Dani” tafad’a tana hawaye! Ya isah kinji ,share hawayenki , yafad’a Yana mik’o mata handcheef d’insa metashin k’amshi” bbu musu ta goge hawayenta….cikin wata muryar dabata sanshi da itaba ,yace I’m really very sorry kinji?”

nima banji dad’in abunba dg baya Kuma sainaga hakan dakikayi shine daidai da fatan kin hak’ura komai ya wuce?”nibe wuceba ! Murmushi yyi yace to saikiyimun hukunci ko?”yafad’a Yana mik’a hannunsa kan kujerar gaba yad’akko kwalin wayarta ya aza Mata akan cinyarta! Yace ga toshiyar Baki…da sauri ta dubi wayar takuma kallesa”alamar?”d’aga Mata Kai yyi had’e da cewa wayarkice,karkice bakyaso kokik’i karb’a,kinsan bbu kyau maida hannun kyauta! Amma Kuma in anty mariya ta tambayeni nace Mata me?”kice ni friend dinki nabaki !”hjy fa?”tasan da wayar ai”

   Nagode sosai ALLAH ya bi…ya isa banison yawan godiya”akwai Sim card aciki sai zuwa gobe zai Fara aiki” to Yaya ” dawane chat dawane chat zakiyi?”yafad’a Yana tsareta da Ido…face book! banison yawan chat ,kamar mutum beda abinyi..banyarba! Gsky kicanxa wani dukafa kowa da kowa Zaki iya gani,inama laifi kice ko what’s app!

     Zanyi what’s app d’in!yauwa kokefa ,amma kada naga number in wani k’ato Kinajina?” Cike da mamaki zainab ke saurarensa”tana zargin to ko Yana sontane?”eh zankiyaye “yauwa kokefa”Dan ALLAH kidena yawan kuka kinji?” To tace tana kokarin fita” zainab! Kingaji da mgn danine?” Ah ah Yaya haidar,shine Kuma kikeson kitafi” bahaka bane ,nima banason murabu(tayi sub’utar baki)kada hjy ta nemeni!saikuma ta rufe fuskarta sbd kunyar kalaminta!

Natafi dake office kina zuwa?”eh !

Wayarsa yalatsa yakira hjy yasaka handsfree” hjy tayi sallama DSP yace dama hjy zamujene da y’arki tamun rakkiya ,bazamu dad’eba! Dan Jim hjy tayi saikuma tace to shikenan ka kula da ita Dan ALLAH Amana nabaka !insha ALLAH hjy zankiyaye… yafad’a Yana kashe wayar ,kafin yazuge glass yakira driver d’insa…

 

Wlh banijin dad’i pls kusani a adduarku

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button