Al-Ajab

Yadda matar da bata taba saduwa da namiji ba ta haifi zankaɗeɗen jariri

Wata mata mai suna Aba ta bayyana cewa ta samu ciki kuma ta haihu amma a saninta babu namijin da ya taba saduwa da ita, Wonder9ja.com ta ruwaito.

 

Yayin tattaunawa da Barima Kaakyire Agyemang a Step1 TV, matar ta ce shekaru hudu kenan da ta san cewa babu namijin da ya taba ko rike hannunta balle su kai ga saduwa.

 

A cewarta ko da taji ciwon cikin ta yi tunanin fibroid ne ba juna-biyu ba. Yayin da ta isa asibiti, ta ce an bukaci yi mata aiki don cire abinda ke cikinta.

 

Ta kara da cewa ta yi iyakar kokarinta na turo fibroid din saboda tsoron kada ayi mata aikin amma ga mamakinta sai santalelen jariri ya fito.

 

Matar wacce ke siyar da ruwa a bakin-titi ta cigaba da shaida cewa ba ta da kudin kulawa da jariri a halin yanzu.

 

Saidai akwai matar wani fasto da take ta kulawa da yaron tun sanda aka haife shi har yanzu tana iyakar kokarinta.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button