Al-Ajab

Yadda na haifi yara biyar tare da mahaifina bayan kwashe shekaru yana yi min fyade -Wata mata

Wata mata ta bayyana yadda mahaifinta ya kwashe shekaru yana yi mata fyade ita da kannenta mata.

 

Matar mai suna Aziza Kabibi tace mahaifinta ya fara yi mata fyade da bugunta lokacin da take da shekara 12 a duniya, inda tace tayi fatan dama ba ta zo duniyar nan ba. Shafin LIB ya rahoto.

 

Mahaifiyarta ba tayi komai ba a kai

Ta bayyana cewa mahaifiyarta tana sane da abinda mahafin nata yake mata amma ba tayi komai ba akai.

 

Ta bayyana cewa mahaifiyarta tana sane da abinda mahafin nata yake mata amma ba tayi komai ba akai.

 

An hana ta zuwa makaranta sannan an ware ta daga cikin ‘yan’uwan ta don kada ta gayawa kowa abinda ake yi mata.

 

Matar ta kuma bayyana cewa mahaifin nata ya gaya mata cewa lalatar da yake da ita “umurnin ubangiji ne”

 

Tace ta so ta gudu ta bar gida a wani lokaci amma sai ‘yan’uwanta maza da mata suka hana ta.

 

Ta bayyana cewa ta fahimci idan ta bar gida, mahaifinta zai fara lalata da kannenta mata don haka sai ta tsaya. Mahaifinta yayi mata alkawarin cewa idan ta daina korafi, ba zai taba kannenta ba, don haka sai tayi shiru.

 

Sai dai, daga baya ta gano cewa mahaifin nata yana yiwa kannenta mata fyade.

 

Ta haifi yara biyar tare da mahaifinta

Tana shekara 15 a duniya, da samu cikin farko da dan mahaifinta.

 

 

Ta samu juna biyu tare da mahaifinta sau biyar sannan dukkanin yaran, wadanda su ma suke a matsayin kannenta, a gida mahaifinta ya amshi haihuwar su.

 

 

 

 

Gabadaya, mahaifinta ya haifi yara shida tare da ‘yayan sa mata.

 

A wata wallafa ta daban ta saka hoton zaman kotun shari’ar mahaifinta bayan asirin sa ya tonu.

Mahaifin matar bakar fata ne dan kasar Amurka mai suna Aswad Ayinde.

 

An yanke masa hukuncin shekara 90 a gidan kaso a shekarar 2013 bisa laifin yiwa ‘yayan sa mata guda biyar fyade.

 

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button