Uncategorized

YAI DA GOBE 23&24

      Su zarah basujima ba da fita “yasakko ahankali Yana tafiya fuskarnan ahad’e tamkar besan meye dariya ba… sumayya dake zaune kan kujera ko kallo be ishetaba… dining room ya wuce yaja gajera yazauna”kafin cikin b’acin rai yace Keeeee!zonan.

Sumayya kuwa ranta yab’aci akan ke d’in dayake kiranta dashi bacin ga sunanta…inharkika Bari nasake kiranki nidake ne!

tashi tayi ta nufi gurinsa”azuciyar ta tana tunanin wacce irin tsanace haka yake nuna Mata?”ahankali tace gani”batare daya kalletaba yace ki had’a mun tea”and last banason surutu da kallo”sbd haka kikiyaye”kinji kobaki jiba?”ahankali tace naji”basket d’in ta jawo…byn ta had’a Masa tea d’in”ta zuba Masa komai a plate”kallonta yyi ido cikin ido Yana yatsina fuska tamkar yaga abin k’yama yace ki fifita mun tea d’in”bazan Shashi da zafi ba..aranta tace bazaka ga gajiya wataba? insha Allah tunda Kaisaikace karamin yarone. komai sai ammaka.bayan tagama yin duk abinda yadace ta dibi abinda takeso ta wuce d’akin ta,tabarshi adining area Yana break fast….


*****************


Hand out ne ahannunta tana dubawa….fisgeshi taji anyi!da sauri cikin fushi ta d’ago kanta… innalillahi!ta furta azuciyar sbd ganin hamsahak’i da yaransa abayansa suna Mata wani kallo”atake Tasha jinin jikinta….cikin muryarsu ta y’an iska yace ke Ina sumayya?”rudewa sameera tayi ,Tama rasa me zatace musu…ko bakya jine?”umm…uhum…tana…tana gida….wata mahaukaciyar dariya suka shek’e da ita ,kafin hamsahak’i yace k’arya kike Muna fuka!tana gidanta ammata aure”inaso kisani nine ajalin mijinta “sannan nasaceta naje na aureta ta k’arfin tsiya” tunda nabita ta arzik’i kan ta amshi soyayya ta…basujira cewartaba sukayi tafiyarsu… ajiyar zuciya sameera tayi”afili tace insha Allah Allah yafika baka isa kamusu komaiba”Allah yashiga tsakaninsu dakai”tafad’a takuma guduri niyar bazata sanarwa sumayya ba ,gudun kada hankalinta yatashi…gaba d’aya taji skul d’in ma ta isheta”nafef ta Tara tafad’a Masa yakaita anguwar nassarawa…wato gdn sumayya.



Bangaren sumayya kuwa sadda ta idar da break fast”parlourn ta zauna sbd ganin Mai gdn baya nan…bata jimaba saiga anty zainab da Inna mariya. sun kawo Mata sauran kayanta dasu gara..sai dangin mahaifinta sukazo Mata sallama..hannu bibbiyu ta karb’i kowa”kunsan amarya da farin jini”acanma dg gdn ummi “wasu nata zuwa”zarah narakosu .duk Wanda yazo sai sumayya ta cikasa da abin arzik’i”kayan irinsu chinchin, dubulan ,alkaki, nakiya da sauransu…sameera bata iso gdn basai kusan 1:30 pm “suka rungume junada sumayya”bayan sun gaisa sannan sumayya tasamu tayi wanka sbd Bata samu yin wankan ranaba,wannan yazo yatafi wannan yazo…bayan ta shirya,ta kawowa sameera kayan motsa Baki. saiga zarah tazo ta kamusu lunch…


Gurin karfe4:30 bayan sun idar da Sallar la’asar”sameera da sumayya suna kitchen suna gyara komai a muhallinsa…sukaji anyi knocking” sumayya tasaka hijab taje ta duba” musty ne da wani”d’auke da kayan amfani na gd”nik’i nik’i ahannusu…bayan sun gaisa yace dama anty yayane yace mukawo”akwai saura amota bara mu’aje  sai akwaso sauran…sannu ta musu ,kafin ta Basu hanya suka shigo parlourn suka ajiye… sameera ta Kira suka Fara kwashe kayan tare…cefane ,dankali, indomie,kwai,Maggi,nama dadai sauransu…komai suka ajiyeshi inda yadace”kafin su kunna gas cooker kasancewar anhad’ata dama”tuwan shinkafa miyar egushi dataji naman kaji da man shanu sukayi sai zoba drinks…gaba d’aya gdn yakacame da k’amshin girkin…sai gan da magrib sameera tace k’awata wucewa gd zanyi,kinsan baba bayaso Muna magrib waje…inkin goge kitchen d’in saiki shiga wanka ko…Bata fuska sumayya tayi had’e da cewa haba Mana?kibari sai kinci abinci Dan ALLAH”hararar ta sameera tayi had’e da cewa sbd ni bak’uwa ce ko?”karki damu zan rik’a lek’oki kafin ki koma skul..  sannan Dan ALLAH,karki bari inkunyi Baki su fahimci irin zaman da kukeyi…kiyita mishi biyayya insha Allah YAU DA GOBE saikin dara agdn nan… murmushi kawai sumayya tayi sbd intanajin suna cewa haka ,gani takeyi tamkar tatsuniya ce…rakiya sumayya tayi Mata bayan tacikata da kayan motsa Baki akan taje gd dasu…kafin suyi sallama”tasakawa k’ofar key”in wannan sarkin izzar yadawo yabude da kansa”ta fad’a tana wucewa d’akin sbd befi10 minit ba akira magrib…



Cikin takunsa na k’asaita cike da nutsuwa” ya iso Baki k’ofar yasaka key ya bud’e k’ofar.wani k’amshi na abinci yadaki hancinsa….yamutsa fuska yyi , had’e da shafa cikinsa ,yatuna rabonsa da abinci tun breakfast ai tuni tsohuwar yunwarsa ta motsa… d’akinsa ya wuce bayan ya rufe k’ofar”agaggauce yyi alwalla yawuce masjeed….

Be shigo gdn ba sai bayan isha’i”parlour yazauna amma be gantaba,yanajin girman kan yakirata”gashi beda  number d’in ta balle yakirata ta kamishi abinci ta had’a mishi ruwan wanka…yafi minti15 a zaune”yaji k’arar rufe k’ofa”amma be motsaba tamkar baya a parlourn”sumayya kuwa kitchen taje ta d’anko jug na sob’o da cups da ruwa swan”tanufi Gurin dining table ta ajiye” kafin ta juya,sbd taso yimishi sannu da zuwa,amma data tuna d’azun da safe ta gaidashi be amsaba saita sharesa kawai….cikin Isa yace ke kamun dinner d’in anan.batace komai ba”tafara kwaso kaomi ta ajiye agabansa kan center table…ta juya abinta da zunbulelen hijab d’inta na Sallah dake jinkinta… tab’e baki yyi had’e da Jan tsaki”Yana wani basarwa ,irin shi adole zaici jagwalgwalo…saidaifa Yana Kai spoon guda abakinsa” yaji girkin is very nice”saidai ko a fuska be nunaba…kunnansa be tsinkeba  Saida yasha sob’on nan..nikaina yabiya Raina… lolx

Koda yagama”nan yatsallake kayan yabarsu”yaje yyimata knocking”tazo ta bud’e sai wani cin magani yakeyi”kafin yadubeta , fuska atamke yace ki gyara girkin ki sbd beyi dad’i ba”nikuma bazan yi asarar kudina na siyi abun buk’atar komai,kekuma Brain naki bayaja” sbd wannan girkin beyi wani dad’i ba..baniso abinci yakwana shiyasa kawai na tura”bbu yadda na iya..inkin gadama kije ki had’amun ruwan wanka” uffan sumayya batace Masa ba,har yagama maganganun sa yajuya.rufe k’ofar tayi had’e da bin bayansa”aranta tana mamakin wacce iriyar zuciya ce dashine?”


Muddin Baku gyaraba saidai kuji shiru…marasa yin comment sunfi kowa jaje inbaayi post ba..bana buk’atar steakers ko godiya… comments kawai inhar kunji shiru karma kuyi jaje…



Share


By mmn fareesa ????️

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button