Y'AN UWANTAKA

Y’AN UWANTAKA NE KO SOYAYYA 1&2

BISSIMILAHIR RAHAMANIR RAHIM

🆓 🅿️1&2

zaune take akan dan damali na step d’in dazaka hau kanufi k’ofar shiga main parlour na gidan”matsaikacin gidane me d’auke da sashe biyu”compound d’in be cika girma da yawaba”sashe na farko shine Inda wata kyakykyawar budurwar da shekarunta zasuyi 26yrs ke zaune tana wanki”azahiri idan kika kalleta zaki d’auka bata wuce 19-20 yrs ba”sbd yanayin yadda takeda kyan jiki”tana wanke jallabiyoyi da wondon jeans da t shirt “kala 3 sai mayan kaya kala 2″tana wankin cikin nishad’i tana wak’arta”gefenta botikine da roba “Inda idan ta sab’e kayan acikin roba saita saka acikin bucket”nesa da ita kuma tap ne”

   kamar dg sama taci wata sanyayyar murya me taushiin gaske dg bayanta ance kamota nan"

Atsorace ta waigo suka had'a ido da wani tsadaddan saurayi kyakykyawan gske"fari dogo"masha Allah"

harara ta wurgomasa tana murgud’a baki tace”.shine zaka tsoratani broth?”

Sorry uk’utinah! kawai yau inaso naganki acikin yanayin tsorone”yafad’a cikin cool voice d’in sa me tafiya da imanin y’an mata”yana kafeta da manyan idanuwansa”

Kayi daidai ai my friend”tafad’a tana maida hankalinta ga aikinta”

sannu da aiki uk’utinah!bara natayaki ko?”yafad’a yana tsugunnawa gabanta”k’amshin turarensa yacika wajen”saida nace d’azun kafin nafita” kibarshi zan mana wanki anjima kikak’i ko?”meyasa yanzun bakyajin mgn ta?”

nidai babu zancen banajin magarka”

tunda dai nasaba nike mana wanki kai kayi mana guga bashike nan ba”tunda mun raba”kabarshi zan Ida da kaina”

be saurareta ba ya nad’e hannun rigarsa yana k’okarin yafara tayata” sukayi muryar wata dattijuwar mata tana cewa”sannu baiwarsa !

narasa wace irin masiface wannan?an rabani dake banacin amfanin ki sai wasu can kike bautamawa”

zaki fidda hannunki kibar masa tsiyarsa ya Ida ko kuwa??ta fad’a atsawace tana kallon budurwar”da fuskarta ke nuna rashin jin dad’in kalaman matar”yayinda saurayin yayi k’asa da kansa beyi mgn ba…..

 Mitsss!dan ubanki bazakizo mujeba?kokuwa kina jiran sai ubanki YUSUF yace kibini"Ahankali maryam tace".umma kiyi hak'uri kije ganinan zuwa dan Allah"bazan jeba d'in"

Idan Kinga nabar nan sai tare dake”Ahankali yad’ago kansa yana shafa tattausan sumar kansa ta fulanin uzuli”da ido yusuf yayiwa maryam alamar tabi umma”

Hannunta ta cire dg cikin kayan wankin ta mik’e tsaye”umma taja tsaki ta wuce tana mita”maryam tabi bayan ta”.

Yusuf yasaki ajiyar zuciya yana girgiza kansa”kafin yaduk’a ya Ida d’auraye kayan”kasancewar ta gama wankin”

Acan bayan windows na sashensu yanufa yafara shanya kayan”

mama dake cikin parlourn tana jiyo komai”ta girgiza kanta aranta tana nemawa matar k’anin mijin nata shiriya”

maryam da umma na isowa sashen umman ta hauta da masifa”

Itadai batace komaiba kanta ak’asa zuciyarta namata zafi”tarasa meye yusuf da iyayensa suka kashema mahaifiyarta aduniya?”

Duk yadda mama da yusuf da abba ke kyautata mata da kulawa da ita.ai yakamata kodan hakan ta k’aunace su…inkin gama tunanin kije kigyaramun ward rope d’in kayana”sannan dole saikin dawo anan da zama wlh”bari ubanki yadawo zan ja dashi awannan karon”

Dan Allah umma kiyi hak’uri kibarni acan tunda broth….rufemun baki wawiya da batasan ciwon kantaba”ba broth buroro”gaba d’aya shida uwarsa sunshanyeki”

Shekaru 26 kintilke agida da zumar saikin gama karatu amiki aure”gashi kingama amma bakya kula samari”kuma badan kinrasa masobaya”gasunan rututu suna suntiri”

Kasa cewa komai maryam tayi”sbd ita kanta tana son kula samarin amma duk idan ta kulasu sai sunyi fad’a da broth d’in ta”tarasa meyasa idan yaganta da wani ransa ke b’aci?”

da wannan tunanin ta wuce bed room d’in ummanta tafara gyara mata kayan…..

****************

yusuf na idar da shanyar ya wuce sashensa”kasancewar yau monday yana azumin nafila”

Bacci yyi sai kusan la’asar yafarka”bayan yagama sallar la’asar ya wuto cikin gidan”

mama na zaune a main parlou yashigo yazauna agefenta”

mama ina my friend?”yafad’a yana kallon k’ofar kitchen dayaketa jin k’amshin girki”

tana kitchen tana had'a maka abin bud'a baki ko?"okay bara nakirata ta had'amun ruwan wanka"

Mama tayi saurin dakatar dashi gun cewa”sannu ubanta kaji?”

kai ruwanma bazaka had’a da kanka ba?dole itace zata had’a maka”bayan aiki take yi”gaba d’aya yarinyar nan batada wani aiki sainaka”idan aka mata aure sainaga yadda zakuyi kaida ita”

Dama inaso namaka mgn “karage wasu abubuwa akan y’ar uwarka sbd asami zaman lafiya”banason fitina yusuf”

Uffan beceba idanuwansa alumshe”itama mama shirun tayi”sbd tasan halin sa indai qnason ganin maganarsa da fara’arsa to saida maryam “

broth!maryam data fito dg kitchen ta kira sunansa anutse”

bud’e idanuwansa dake lumshe yayi ya kalleta yana langab’e mata kai”sbd yadda yaga kayan jikin ta sun amsheta tayi kyau”

Ahankali tace”.
tun d’azun naga bangankaba ko bacci kayine?”tunda nasan awannan time d’in baka zuwa shago”

Umm banjima da tashiba”wanka zanyi yanzun uk’utinah pls”to shikenan bara naje na had’a maka ruwan”sannu ya azumin?”

To Alhamdllh aini kibari nayi ke bakiyi ba ko?”alhamis ai zanyi ko?”banyardaba”

sai kallonsu kawai mama keyi dama Inda sabo tasaba ganinsu haka ko fin hakanma”

Juyawa tayi ta fice dg parlourn yabita da kallo harta b’acewa ganinsa”

Lip d’insa na k’asa yatsotsa yana yiwa mama kallon gefen ido”

Kawai yazaro wayarsa dg aljihun jeans d’in jikinsa ya kanga akunne yana cewa hellow banaji sosai fa”

   yafad'a yana tashi tsaye yabar parlourn"yana fitowa yamayar da wayar aljihu"sbd yasan muddin yace" zai tashi yabiyota sai mama tace yabari tadawo sannan yatafi"

Anutse ta had’a masa ruwan wanka tana fitowa dg toilet d’in tasamesa tsaye yasaka jallabiya milk ajikinsa”sai yayi tamkar balarabe….loxl”sunkuyar da kanta k’asa tayi sbd ganin irin yadda yatsareta da ido”kuma irin wannan kallon dayake mata saita dingajin fad’uwar gaba”

Uk’utinah gobe zaki rakani shago?”mezai hana broth?”tafad’a tana murmushi”

Matsowa yyi dab da ita yana cewa” ga wayata kisamun caji”saiki fitomun da kayan sawa”kuma ni ban yardaba kitafi kibarni ba” kijirani pls”

Amsar wayar tayi tana cewa “lallai ma yaron nan sai kace wata matarka da zan jiraka?”tafad’a tana dariya k’asa k’asa har wishiryarta ta bayyanah”

    Sbd tasan yusuf tashak'a dan yatsani ace masa yaro"finciko hannunta yayi har jikinsu na gugar juna yace".meye kikace?"harara ta galla masa tace".abinda kunnanka yaji"hancinta yaja yace". bara nafito zakisan kincemun yaro wlh"to aidai wata 3 nabaka ni yayarka ce"nadai baki wata 3"

Broth kaifa azumi kakeyi”kaine zaka wahala tunda ni banayi”

kema ai sbd kinyi bak’o ne shiyasa bakyayi ai”yafad’a murya can k’asa”sosai kunya ta kamata”ta janye hannunta daya rik’e”

yana kasaitaccen murmushi yace”.sarkin kunya”kiduba saman mirror pads na nan danasiyo miki”

banza tamasa ta juya”shikuma ya wuce bathroom d’in”

Bayan ta fito masa da kayansa”ta d’auki pads d’in tabar d’akin….

Asalin labarin✍️

Karki bari ayi babuke atafiyar y’ar uwa😊

Azuba zafafan sharhi yanzun aka Fara wasan

wannan book d’in nakudine

Leave a Reply

Back to top button