YANCIN KI Page 1 to 10

“you.. you must be crazy woman ya katseta a fusace yana watsa mata wani irin mugun kallon dayasa hantar cikinta kad’awa da sauri ..”you are going insane ,” imagine the rubbish that’s comin out of your mouth…. “bule.. bule kamata yayi tun lokacin da kika fara wad’an banzayen kalaman naki nasoma d’aukeki da gigitaccen marin dazai sa ki dawo cikin natsuwarki daya gudu yabar gangar jikinki .
“wallahi azim me’ad dakace ni irin namijin dake dukan mace ne, da yau na miki dukan mutuwa, dukan mutuwar bazaki iya tashi ba… you are stupid ni kike son meidawa useless husband da bai san ciwon kansa ba over my dead body …
sororo tayi tare bud’e bakinta tana dubansa a tsorace sannan tace “me kake nufi da wad’an maganganun naka?
“bansani ba.. “oh my God wlh me’ad ban ta’ba tunanin haukan son aikinki ya zarta hk ba “ni kike expect na zauna gida na zama me kula da diyarmu alhalin gaki ” Bari na gayamiki dolenki ki ajiye wannan banzar aikin naki ki zauna gida kibawa diyarki kulawar data dace da kanki amman bazai ta’ba yiwu ba kice ni…
atsawace tace “kamin shiru ,what do you mean by it can’t happen ?
“dakata fu’ad bafa nason abinda kake min banson rainin irin wannan hankalin fa.
“dolenki dai ki zauna gida, ko kina so ko ba kya so “you must take care of your bby by yourself not me, dakikiya kawai dabasan yancin kanta dana diyar cikinta ba..
“kai ma ai ubanta ne
meyasa bazaka zauna ka ajiye aikinka kayi taking care dinta ba ?
“wani excuse kake son nabayar agurin aiki da kake wannan banzar maganartaka ?
“ok ni ne ma nake miki maganar banza ko?”
to kisan dasanin matukar ni nake aurenki ba kece kike aurena ba dole kibar dan iskan aikin nan da kike takama da gadara dashi ,idan company ta tmbyeki dalili rashin zuwanki kece mijinki ne yace ki zauna agida ki kula da diyarki sai muji me zasu ce.
cike da ihu da hargagi tace “wallahi baka isa ba, sam hkn ma ba me yiwu bane fu’ad sai dai kasan yadda za’a yi ,domin kasan taimakon da albashina yakeyi a gidan sabanin naka da bai taka kara ya karya ba .
“ji stupid ..ji abinda kike fad’a ,gaya min “what does your money do in this house?
a matukar tsawace ya sake furta “stupid amfanin me kudinki yake acikin gidan tare da d’auketa da wasu maruka guda biyu ajere…. taja baya da sauri dafe da kuncinta jin marin da fu’ad ya d’auketa dashi wani irin dummmmm taji yana mata kuwa acikin kunneta yayinda jiri yasoma kokarin d’aukarta ,kofar datake jingine daita ne ya taimaka ya riketa ta tsaya bisa kafafunta “shashan cin banza shasha cin wofi ..
“kad’an kikagani sannan yanzu zan fito miki da nawa true colour din, zaki san baki da wayo, zan koyar dake hankalin da iyayenki suka gagara baki yakarasa mgnr tare da cewa dan Malam matsa daga hanya na wuce shasha kawai dabatasan ciwon kanta ba, kin d’auka tsoronki ake ji ne ko me ?
ganin ta kyame guri daya taki bashi hanya yasa hannusa daya ya fixgota da karfi ya makata kan kujera, a guje ta mike tayo kansa gadan gadan ta shige jikinsa “ka mareni fu’ad ?
“an mareki me zakiyi?
” idan akwai abinda zakiyi kije kiyi, idan kuma ke kike ciyar dani daga yau ki daina stupid kawai .
“ko ban ciyar dakai ba but at least kasan akwai abinda kudina yakeyi acikin gidan nan.
“sannu hjy mariya.. ..dan Allah leave the road for me.
ta sake motsoshi tana fuskantatshi har suna shakar numfashin junansu “bazan matsa ba ,kai yanzu har ka isa kace kudina baya amfani acikin gidan saboda kai din butulu ne, daman ku maza halinku ne butulci, ko me za’a muku arayuwa wata rana sai kunce ba’ayi muku komai ba
“ki matsa na wuce ina da abin yi ,kinsa ba tun yau nake warning dinkin akan maganar abinda kudinki yake acikin gidan nan ba, amman bakijin magana ko, ni fu’ad bansaki yin abu dole acikin gidan nan ba , duk abinda nagadama na kawo kiyi hkrn amfani dashi ,idan kin siya wani abu cikin salary dinki wannan matsalarki ce dan ban saki ba .
“kai kasani butulu kawai wanda bai san mutunci ba ,kuma wallahi dole ka ajiye useless work dinka, ka zauna ka kula da yari…. motsin bud’e kofar parlour’n yasa ta katse maganarta tare da juyowa ahankali ..
mmn sudais ce
????????????????????????
‘YAN CINKI
????????????????
????????????????????????
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
page 31 to 35
………diraving kawai yake cike da matsanancin tashin hankali ,yayinda gefe guda na zuciyarsa ke wani irin harbawa, saboda jin bugun zuciyarsa yake tun daga tsakiyar ‘kirjinsa har ilahiri sansan jikinsa. wanda hakan ya haddasawa gefen kansa sarawa da ‘karfi, gaba d’aya ji yayi jikinsa ya mutu, tu’kin ma na neman gagararsa.
A hankali ya gangara gefen titi yayi parking tare da dai-daita tsayuwar motarsa ya rungume sitiyarin motar had’e da d’aura kansa bisa hannuwansa yana fitar da numfashi me tattare da hucin zafi.
tun daga nesa Sajida wace daga gidan me’ad gidan misna ta wuce, ta hango motar fu’ad parke a gefen titi cike da matsanancin mamaki ta soma rage gudun motarta har sanda ta iso daf da inda motarsa take .
tayi parking ta fito da hanzarinta daga cikin motarta ,hankalinta a matu’kar tashe ta doshi inda yake, tana kare fuskarta da tafin hannuta saboda hasken ranar daya dallare mata idanu , jiki a sanyaye ta ‘karasa jinkin motar ta tsaya tare da kai hannuta ta k’wank’wasa glass d’in motar, wanda hakan yasa fu’ad ‘ko’karin d’ago idanunsa domin ganin kowaye.
A hankali ya sauke kyawawan idanunsa a kan fuskarta dake cike da mamakin ganinsa a gurin , runtse idanunsa yayi sosai yana jin wani irin d’aci a ransa mara misaltuwa ….
da hannunta tayi masa alama yayi warning glass din motarsa, sai da ya furzar da iska me zafi ta bakinsa sannan yayi ‘kasa da glass din, kana ya mai da kansa kan sitiyari kamar yadda yayi da farko , shi kad’ai yasan irin rad’ad’in da zuciyarsa take ciki a kan wannan matsalar dake shirin kunno kai cikin rayuwarsa da al’amuran gidansa.
sautin muryarta yaji ta doki dodon kunneshi “lafiya Abban NASREEN kayi parking a gefen titi haka?
“idan ma wani abu ne ke damunka, kamata yayi ka samu ka qarasa gida first, domin samun natsuwar zuciya saboda tsayuwarka a nan is very very risking.. ta ‘karasa mgnr tana zagayo wa d’ayan gefen tana me k’wank’wasawa alamun ya bud’e mata .
da ‘kyar ya samu ya danna wani abu a cikin motar domin bata damar shigowa ba tare da yace mata komai ba saboda kansa dake cigaba da sarawa.
ta bud’e murfin motar jikinta na rawa tare da janye jakar briefcase d’insa dake kujera me zaman kanta, ta zauna tana masa fari da ido muryarta a sanyaye tace ” sannu Abban NASREEN na san duk damuwar nan taka ,baza ta rasa nasaba da matsalar kawata ba?
,”amman ka yiwa Allah kayi hakuri Insha Allahu komai zai zo da sau’ki, me’ad ce bata d’aukar shawara na rasa abinda ke rud’arta….
A hankali ya d’ago idanunsa tare da waigowa gefen da take zaune ,idanuwansu suka tsarke cikin juna, suna had’a ido kowanensu ya kafe d’anuwansa da kallo zuciyoyinsu na ayyana musu abubuwa da yawa .
kallon cikin kwayar idanunsa ta cigaba da yi tana jin wani abu na yawo a jikinta ,had’e da hango wani irin tashin hankali kwance a cikinsu , a hankali ya soma kokarin motsa bakinsa ” kika ce kin rasa abinda ke rud’ar ta ?