Uncategorized

MATAR UBA 14

????????????????????????????????????????????????????????????????????????????             *MATAR UBA* 

????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

       _(A True Life Story_ )

            *Short story* 

 “`Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)“` 

Follow me on Wattpad @milhaat

Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0

???? *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* ????????️

 _(‘Kungiya d’aya tamkar da dubu)_ _____________________________

*MATAR UBA*  Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.

Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK*  much Love.

 *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

“`NOT EDITED

CHAPTER 14“`

“A a nagode” ta juya tayi tafiyar ta, tana ji Yana Kiran sunan ta tayi burus dashi, tab’e Baki yayi ya d’aga kafad’ar sa ya d’aura da fad’in “chan Miki” ya shige cikin gida.

????????????????????????????????

………. Rai ‘bace ta bar gidan, bata nufi ko Ina ba sai gida, tana Shiga compound na gidan ta hangi Asiyah da shamsiyya a zaune suna Hira, ta gaban su ta wuce bata kula su ba kitchen ta nufa ta d’ebo ruwa cikin bucket tayi waje dashi, ba tayi wata wata ba ta watsa musu ruwan, a razane duk su biyun suka Tashi.

Kama Baki tayi Tace “Oh my God ban San da akwai mutane anan ba” ta had’a da tsaki ta juya da niyar komawa d’aki shamsiyya Tace “Me dakata mu sa’annun ki ne?  By waye ba ki iya bada hakuri Baki?” 

Tsaki ta jaa ta juya ta tafi, ganin shamsiyya ta yo kanta tasa ihu ta Ruga a d’ari.

Huci sosai shamsiyya take, Asiyah sai hakuri take ta bata , shamsiyya Tace “Asiyah Dan Allah ki barni na koya Mata hankali, baki ga abinda tayi Mana bane?”

” Na gani, na gani Mana kiyi hakuri Kar ki kulata , neman maganace kawai”

“ai kuwa da ta Kashi na jaki, taci Albarkacinki if not da sai ja karya ta”

” Nagode nagode Muje na raka ki”

WASHE GARI

A hanyar ta ta dawo wa daga talla ta tarar Yana jiran ta, bayan sun gaisa ta nemi ya rage Mata hanya Taki, ya lura motar ne Bata son Shiga, hakan yasa ya kulle motar ya dauka Mata roban suna tafiya suna Hira anan ne ya mata tambayoyi game da Rayuwar ta sannan mene ne matsayin Safiyya a gunta, Bata ‘boye Masa ba ta Sanar Masa da ita d’in kanwartace Amma ba Uwa d’aya ba, isar su ke da wuya ta hango motar Baraka sai da Taki kamar ta arce da gudu, Amma sai ta rike kanta Kar tayi abin kunya, Baraka parking tayi kana ta fito tana mishi kallon sama da kasa , cikin girmamawa ya gaida ta, hannu ta d’aga Masa had’e da daga Masa tsawa “Dakata who are you?”

Murmushi yayi yace “Sunana Hashim Ni Abokin tane”

” Aboki wannan wani sabon iskanci ne haka da zakace min Kai a Abokin tane, don rashin kunya shine harda rike Mata roba” 

Ta Maida kallonta ga Asiyah Tace “ke don uwarki ki wuce cikin gida”

Kuka ta Shiga yi tana fad’in “Dan  Allah mummy kiyi hakuri”

“Okay baza ki wuce ba kenan?”

Jiki a Sanyaye ta shige Ciki, Baraka ta fizgi roban da ke hannun sa , Tace “Kayi saurin barin Nan ko nasa a Canza maka kamanni”

Barin wurin yayi ba tare da ya ji me zatace ba, duk hankalin sa ya Tashi, ya koma gida, mahaifiyar sa na ganin sa ta bi bayan shi ganin yanda d’an nata ya sauya lokaci guda bayan ba a Haka ya bar gida ba, “son me ke damin ka ne?”

Kallon ta yayi da idanun sa da suka canza kala daga Fari suka koma jaa, murmushin takaici yayi ya hura iska Mai zafi kana yace “Ba komai kawai dai kaina ne ke ciwo”

“Kan ka na ciwo baza kasha magani ba sai kace wani yaro”

“Ai yaron ne Amma fa gunki”

Murmushi tayi Tace ” Allah ya shirya min Kai son, dama akwai maganar da nake so muyi da Kai”

” To mummy ina sauraron ki”

” Son kasan kawata Nana? Mahaifiyar Yesmin”

” Eh na Santa”

Murmushi tayi Tace Good so nake kaje gun Yesmin ki fahimci juna mun zauna munyi shawara da mahaifiyar ta ya ta muka duba muka gani mu Kara dankon zumuncin mu, kaga idan kunyi aure ba abinda zai raba mu”

” Mummy kiyi hakuri akwai Wacce nake so”

Shiru tayi Sam Bata ji dadin maganar na sa ba, dai daita kanta tayi Kan Tace ” Wace ce ita? Kar dai Yarinyar da tazo neman ka ranar?”

Murmushin gefen baki yayi yace ” A a wannan Safiya ce Yar uwar Asiya uban su ne d’aya”

Tab’e Baki tayi Tace ” Toh Shikenan Allah ya tabbatar da alhairi” ya amsa da ameen.

 *BAYAN SALLAH ISHA* 

hankalin Asiya ya kasa kwanciya, ta rasa dalilin da yasa duk sanda ta ganshi sai taji hankalin ta ya kwanta, Bata tab’a Jin haushi Baraka ba irin na yau Sam Hashim Bai chan chanci haka ba, a zabure ta Tashi ta sa hijab a jikinta ta fice daga gidan tayi sa’a Mai gadi Yana ban d’aki duk da tasan ba zai Hana ta fita ba,Kai tsaye gidan su Hashim ta nufa ta dad’e a tsaye a bakin gate kwasam sai ga motar da ,tun daga nesa yake hango mutum dake akwai street light a gun sosai, sai da ya karaso gate d’in ya gane ta,Yana ganinta ya kashe motar ya fito da saurin gaske had’e da gudu, ya karasa inda take Yana fad’in “Asiyah kece?”

Murmushi tayi ta amsa da “Eh nice”

“Kina lafiya? Me Kika Zo yi anan?”

“Nazone  na baka hakuri akan abinda aka maka” 

Murmushi yayi yace ” No need ai Asiyah,Zo mu Shiga cikin mota,ba musu tabi bayan sa da kansa ya bud’e Mata marfin motar bayan ta shige ya Maida ya rufe ya zaga Shima ya zauna.

Murmushi yayi yace “Asiyah na tambaye ki Mana please”

“Ina sauraron ka”

“Matar Nan ta ‘dazu wace ce?”

“Matar Uba na Ce”

” Kai Amma bata da kirki, but kiyi hakuri fa na aibata mummyn ki”

Murmushi tayi Tace ” bakomai”

Gyara Zama yayi yace “Asiyah akwai abinda na dad’e ina son fad’a miki Amma ban San ya Zaki d’auki zancen nawa ba”

” Mene Ne ina sauraron ka”

“Asiyah ina kaunar ki Soyayyar da ban tab’a yiwa wata a duniya ba”

Murmushi kawai tayi, yace ” kin yi shiru?”

Rufe fuskarta tayi da hannayen ta, Tace “Nima ina kaunar ka Yaya Hashim”

Wani huci yayi na samu nasara Kan ya matso da kanshi kusa da nata, yace “Dan Allah dagaske kike?”

Kai kawaii ta d’aga Masa alamun “Eh” 

“Alhamdulillah insha Allah baza kiyi Dana sanin Soyayya Dani ba”

Gani yayi har ta bud’e kofar ta fita da sauri ya Sha gabanta ” ina Kuma Zaki?”

“Zan koma gida kar mummy ta nemi Ni”

“Hakane Muje na yi dropping d’inki”

” A a Kar ka damu yanzun Nan zan Isa”

” Bazanyi wannan gangancin ba kin manta ranar abinda yaso ya same ki da dare Allah ne kawai ya tsare? Kawai ki Zo nayi dropping d’inki” 

Ba musu ta Shiga a dai dai bakin layi su ajiye ta, tana Isa ta shige d’akin ta.

Maman Yesmin charting take sosai da maza kala kala aciki har sukayi sharing contact da mutum uku suna WhatsApp suna Facebook, tafi wata d’aya haka, abban Yesmin ya lura da tana dare a online Kuma bada shi take chat ba, abin Bai dame shi ba ya d’auko Normal abune ganin abin sai gaba gaba yakeyi hakan yasa ya kudiri aniyar gano me takeyi.

Tana gaiyatar samarin ta gida idan Yesmin ta tafi makaranta ko islamiya, ko Kuma sai tayi bacci su shigo, hankalin ta akwance bata da wata damuwa da ta rage.

“Abokina na rasa dalilin da yasa Mata ta take chat har saita raba dare Kuma ba Dani take chat ba,abin Yana damina”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button