YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 1 to 10

ta d’age masa girarta d’aya tana sake masa fari da ido muryarta a sanyaye tace “eh Abban NASREEN ni dai gsky bansani ba, amman idan kasan abinda ke rud’arta ka taimaka ka gaya min ? 

” girgiza kansa kawai yayi ba tare da ya sake cewa daita komai ba, ita kuma ta bishi da mayataccen kallo tana yaba kyawun halittarsa, ganin yadda jikinsa yayi matukar amsar kayan dake sanye ajikinsa ya kara hura wutar soyayyarsa acikin zuciyarta ,ji take tamkar ta shige jikinsa ta rumgume shi sannan ta rarrashsshi a kan tarin damuwarsa . 

A hankali ta sauke nannauyen ajiyar zuciya tana furta” hamson kenan …..yau dai gani ga ka kyakkyawan mutumin da zuciyata ta dad’e da kamuwa da matsanancin sonshi, kyakkyawa son kowa ‘kin wanda ya rasa …” am very sorry da abinda kaji yana fitowa daga cikin bakina , domin na dad’e ,ba tun yau ba nake son amayar maka da abinda ke cikin zuciyata, “a gaskiya fu’ad na dad’e da afkawa cikin duniyar kaunarka ,idan ba zaka damu ba zan so ka bani damar kawo farin ciki cikin rayuwarka.

” fuad ina tsanin sonka tun a ganin farkon dana maka a rayuwata, wasu dalilai ne suka hana ni fahimtar da kai tsantsar ‘kaunarka gareni, amman yanzu ga dama ta samu ,” ka natsu ka saurare ni ,ina son ka aure ni na maye maka gurbin da k’awata ta kasa cikewa a gidanka.

bai san sanda yayi saurin dafe kanshi ba cikin matsanancin 6acin rai sakamakon jin abinda ke fitowa daga cikin bakinta, wani tsaki ya ja da ‘karfi kana yace “kin zo ne ki ‘kara min damuwa a kan wanda nake ciki ko me? 

“calm down my hamson i thoueght you feel of fended that I m disturbing you, wanda ba haka bane, ni nasan abinda nake yi, gaba d’aya nasan halin da kake ciki , nasan kana cikin damuwa fu’ad, dan haka nake neman alfarma da ka bani dama na nuna maka kalar tawa soyayyar plz….

A matu’kar firgice ya sake juyowa ya kalleta “me take nufi da shi da rayuwarsa gaba d’aya?

“lallai duniya abin tsoro, haka mutane cikinta, “me yasa sam wasu matan basu da tunani da hango abinda zai je yazo? 

“ita din fa tamkar yan uwan junane suke da me’ad, tare ya sansu komai nasu tare tun daga kan sutura da komai, amman take furta wad’annan zantuttuka gare shi ,ba tare da wata shakka ba ko tsoro , “kai tur da mata masu irin wannan hali… 

kusan minti goma suna zaune haka tana gaya masa zantuttuka masu sanyi da shiga jiki ba tare da yayi yun’kurin sake cewa da ita komai ba, illa zuciyarsa dake bugawa cike da mamakinta ,duk wata kalmar soyayya da zata fito daga cikin bakinta sai tayi silar bugar masa da zuciya, har zuwa sanda zuciyarsa ta kawo masa mafitar da zata tunzura zuciyar me’ad dinsa akan wulakacinta garesa zaiyi amfani da sajida ko hakan zai kawo cigaba arayuwarsu , take ya amince da shawarar da zuciyarsa ta bashi na ya amince mata kawai ko dan koyar da ita darasin dake cikin duniya .

“sajida ta kira sunansa cikin sanyayiyar muryarta me tsananin dadin sauraro “plz Abban NASREEN kace min wani abu mana, da alamun akwai abinda kake son cewa gareni ….

“zaki iya maida ni gida yanzu i think bazan iya ‘karasawa da kaina ba ?

 yayi mganar muryarsa can ‘kasa, jikinta na rawa tace ” me zai hana bari na kira Hakim direbana yazo ya same ni a nan, domin ya biyo ni da tawa motar .

 kansa kawai ya iya d’aga mata tare da juyar da kansa gefe yana kallon gefen titi , dan kwata-kwata baya son cigaba da dubanta, yana jin idan ya cigaba da kallonta komai zai iya faruwa a tsakanin su ,saboda kyawun surarta, jikinta me matu’kar kyau da hargitsa lissafi ga shi tana cikin irin shigar da yafi son mace ta kasance ciki, doguwar rigar atamfa, java gold me adon flower’s ta yane kanta da ‘karamin mayafi baki ,doguwa ce sosai kamar me’ad dinsa, sai dai ba fara bace sai jikinta irin karuwan jikin nan gareta kirjinta cike yake bammmm da ruwan nono , dan wani lokaci yanayin jikinta na sauyawa musamman idan tana cikin farin ciki, ba dai wani tsagwaron kyau gareta ba amman akwai kyawun halittar jiki, a kallo d’aya mutum zai iya afkawa cikin tafkin ‘kaunarta, katse shirun sa tayi ta hanyar cewa kad’an yi ha’kuri yanzu zai ‘karaso. 

kasa amsawa yayi saboda wani abu da yaji yana yawo a gaba d’aya ilahirin jikinsa me kama da shocking wanda ke haddasawa kirjinsa dokawa, cikin mintunan da basu wuce goma ba sai ga Hakim ya ‘karaso a kan okada ,tana hangosa ta bud’e murfin motar ta fito a dai-dai lokacin da ya ‘karaso gareta yana me rusunawa, ta mi’ka masa key’n motarta bayan tayi nesa kad’an daga jikin motar fu’ad “ka biyo mu a baya, abinda ta iya cewa kenan ta juya wanda a lokacin har fu’ad ya samu damar komawa d’ayan bangaren sannan ta shiga ta zauna mazaunin direba taja motar a guje Hakim ya biyo bayanta kamar yadda tace. 

fu’ad yayi shiru yana sauraron abinda take fad’a masa a kan matsanancin ‘kaunar da take masa, amman ya kasa furta mata dai-dai da kalma d’aya domin maida martanin maganar data ishe shi dashi ,saboda bacin ran da yake ciki dan gaba d’aya haushi tare da mamakinta ne ya addabi zuciyarsa .

  A bakin get din gidan taja ta tsaya tare da yin hon,me gadin ya taso da sauri ya bud’e musu tasanya hancin motarsa ciki harabar gidan , kai tsaye inda aka tanada domin parking din motoci ta nufa tayi parking tana sake yi masa nacin ya taimaka ya amshi tayin soyayyarta ,a tare suka fito daga cikin motar sannan ta kulle ,ta tsaya a gabansa tana fuskantarsa tare da mi’ko masa key , wanda dai-dai wannan lokacin me’ad dake zaune cikin d’akin ta mi’ke tsaye da niyyar zuwa d’akin NASREEN kamar ance ta waigo zuwa harabar gidan, idanunta suka sauka, a kansu tsaye ,sai dai duhun daren da ya soma shigowa ya hanata gane kowace tsaye a gaban mijinta tana mi’ko masa hannu buga da k’ari fadadden kirjinsa ya kareta , ‘kirjinta ne yayi wani irin lugud’en bugawa da ‘karfi har sai da ta kai ga dafe dai-dai saitin zuciyarta da taji yana neman tarwtsewa.

A hankali sajida take masa magana wacce ke sake kashe masa jiki “fu’ad ina sonka, bana tunanin zan iya sakacin da nayi a farkon haduwar mu, ka taimaka ka amincewa aurena plz….. tare da d’aura key’n motar a tafin hanunsa tana me shafar tsakiyar hannunsa wanda hakan yasa yayi saurin janye hannunsa “sajida …….fu’ad ya kira sunanta. 

“na’am fu’ad dina .. 

“zaki iya fita daga cikin gidan nan da rayuwata gbdy tun kafin zantuttukanki su soma tarwatsa min ‘kwa’kwalwa? 

tayi shiru tare da tsura masa ido tana kallonsa , take hawaye ya soma ciccikowa a idanunta “kar ka min haka fu’ad wallahi… “dakata plz just live now ya nuna mata hanyar fita da hannunsa “bazan damu da duk abinda zaka min ba, saboda darajar son da nake maka ,ka sani duk duniya babu wacce tafi can-canta ka aura sama da ni, na ha’kura da kai ne a wancan lokacin saboda lokaci ya ‘kure min ,amman yanzu ina tabbatar maka sai inda ‘karfina ya ‘kare akanka …..

“ni dai na gaya miki ki fita cikin rayuwata, kar ki sake kuskuren furta min kalmar so, saboda ko nakasance mahaukaci bazan ta’ba kuskuren aurenki ba, “me na tsinta a aurena da me’ad ballantana nayi tunanin auren ki? 

“kar kace haka plz, ka jarraba aurena fu’ad … akwai bambamci me yawa atsakanina da me.. 

“shout up there yayi maganar a matu’kar harzu’ke wanda yasa me’ad ‘ko’karin fitowa daga cikin part dinta “me ye bam-bamcin ki da me’ad? 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button