YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 1 to 10

“yadda me’ad take haka kike …..

” kar kace haka fu’ad wallahi akwai bam-banci me tazara a tsakaninmu..tsaki ya ja a fusace ya matse key’n motarsa ya shige cikin ya barta tsaye a gurin tana kallon bayansa babu kowa a parlour’n sai ‘karar TV dake manne jikin bango a parlour’n a hankali dafe da goshinsa ya nufi d’akinsa ya fad’a saman doguwar kujerar three seater guda d’aya da ke ajiye a gefe d’aya yana lumshe idanunsa .

mee’ad ta shigo d’akin cikin sauri tana binsa da kallo bayan taje harabar gidan ba taga matar data kawo mijinta gida ba, muryar ta a fusace ta soma magana “wacece wannan tantiriyar da ta kawo ka gida yanzu ? 

“meye ala’karka da da ita da har take da ‘karfin zuciyar tu’ko min miji har ma da shigo min cikin gida?

 shigowarta da banzaye tambayoyinta gare shi yasa shi mi’kewa tsaye ya nufin hanyar bayi “honey cant to hear what am saying? 

” nace wace ‘yar iska ce ta kawo ka yanzu ? ta biyo bayansa tana sake tambayarsa ,yayi mata banza tamkar ba dashi take mgn ba,ya shige bayi tare da bugo ‘kofar bayin da ‘karfi kad’an ya rage bai bugi fuskarta ba, tayi baya da sauri tana dafe bangon d’akin gaba daya hankalinta da natsuwarta ya soma barin gangar jikinta ,idanu ta tsurawa ‘kofar bayin tana mamakin abinda ya faru wanda bai ta’ba faruwa ba, a tun had’uwarsa dashi ,sam bai kasance ma nemin mata ba, ko shiga shirginsu asali ma duk macen da ya ganta bata birgesa itama sa’a taci . 

 

fu’ad na ‘karasa shiga bayi ya sakarwa kansa da ya ji yana ‘ko’karin rabewa gida biyu ruwa, ya kai tsawon minti talatin yana tsaye ruwa na tsiyaya a jikinsa ba tare da ya cire kayan jikinsa ba, sannan ya cire kayan jikinsa ya soma wanka a tsanake cike da ‘bacin rai “me yasa na auri me’ad? ya jefawa 

zuciyarsa wannan. tambayar .

“me yasa ban yi ha’kuri da tarin soyayyarta gare ni ba ,na tunzura zuciyata gurin aurenta ,ga shi ina cikin tsaka mai wuya da lamarinta ? 

“ta yaya zan auri matar da baxata iya bin umarnina ba tare da sadaukarwa gareni …?” hakika nayi kuskure a rayuwata , tabbas nayi kuskure babba da na aureta a rayuwata ba tare da nayi tunani ba… “a zahirin gasky hakkin NASREEN sai ya kamani domin ban za6a mata uwa ta gari ba abin alfahari ba.

“why why why na aureta?

ya furta tare dunkule hannunsa ya naushi iska , da wannan tunanin ya ‘karasa wankansa ya fito ,tana tsaye tamkar wacce aka dasa ta a gurin ,yazo ya wuceta yana goge jikinsa ya nufi wardrobe dinsa ya ciro jallabiyya black colour ya sanya, ya je ya kunna TV kana ya dawo kan kujera ya zauna ba tare da ya kalli inda take ruku6e ba, ya d’auki remote ya kunna AC . 

me’ad ta ‘karaso in da yake ta zauna kusa da shi sosai , zuciyarta na wani irin tafarfasa ta tsura masa ido tana kallonsa , da ‘kyar ta samu ta tattaro kuzarinta tare da kamo hannunsa d’aya cikinsa sannan ta soma motsa labbanta “Abban NASREEN tambayarka fa nake wacece wannan matar data kawoka plz ?

” i have been talking you since, and i really has to do this before everting could have mess up wit us, kawai just tell me who is she?

  

 hankalina ya saka kwanciya saboda ban ta’ba ganinka tare da wata ba, ballanata har ku kasance acikin motarka tare.. 

“ka fara neman mata ne ban sani ba ko me? 

“plz talk to me now hankalina a matu’kar tashe yake.. 

fixge hannunsa da ke cikin nata yayi a matu’kar fusace sannan ya juyo a hankali yana fuskantarta sosai ” me’ad !!! ya kira sunanta har sau uku da muryarsa a sanyaye sai dai da ji kasan yana cikin damuwa da tashin hankali “you really has carryover in your dity life for this idiot matter .

” me’ad lokacin yana neman ‘kure miki amman rashin common sense dinki ya’ki bari ki hankalta, nadamar ki ta kusa zuwa gareki ba tare da kin shiryawa hakan ba , lokacin kukan ki yayi me’ad…..sannan watan da na saninki ya kusan tsayawa matsawar baki canza wannan hali da ‘kudirinki naki a kaina ba…..wallahi ina me tabbatar miki sai kin yi kuka da idanunki nan gaba saboda ami.. … 

“dakata dakata malam, wani irin baki ne haka kake min ?

 tambayarka kawai fa nayi ba dogon sharhi na nema daga gareka ba, da kake kokarin yi min mugun alkaba’i, idan budurwa kayi ko neman mata ka fad’a ,ai sai kasanar wa mutane bawai kasoma wa mutun mugun baki ba, duk ma abinda zaka yi kaje kayi yayi wannan matsalarka ce ba tawa ba, ni dai yadda gobe zata kasance nafi bukata son sani ba wani surutunka ba. 

“who is going stay at home with our daughter tomorrow simple as that? 

“i don’t know, and if you dare ask me this stupid question again i will deal with you right now, “shasha kawai kina nan kina haukan banza ana miki zagon kasa a kan wannan banza aikin naki wanda nan gaba zai jawo miki nadama mara amfani ,amman muje zuwa ya ‘karasa maganr yana maida idanunsa kan tv.. 

zabura tayi ta mi’ke a fusace” kaine zaka yi nadama domin kuwa ga tarin nadama nan a ‘kwayar idanunka ina hangowa. 

“nadamar aurenki ba ya juyo a matu’kar harzu’ke yana dubanta “nadamar aurenki kawai ke cikin ‘kwayar idanuna da zuciyata ,wallahi mead i regret married you in my life ,a yanxu na tsani kaina da na zabe ki a matsayin abokiyar rayuwata .

” na d’auka aurenki farin ciki ne gareni ashe tarin damuwa da bakin cinki ne, wallahi ban san yadda zaki kasance min kenan ba da ban amincewa aurenki ba, nayi da nasani yafi sau ba adadi a kan aurenki da nayi ya ‘karasa maganar yana me 

jan dogon tsaki da zance zuci 

” ban san me ya shiga cikin tunaninna ba a kanta?

ban san abinda ya kai ni amincewa zucuyarta a kanta ba? 

“a da can baya da mahaifinta ya’ki yarda da aurensu , ya ha’kura da ita amman daga baya ta sake dawo cikin rayuwarsa wanda silar haka komai ya faru da shi ya furzar da iska me dumi ta bakinsa .

 ficewa tayi daga cikin d’akin zuwa nata d’akinta, a hankali ta shiga zagaye d’akin hanunwanta sar’kafe cikin juna gaba daya ta kasa tsaye ta kasa zaune, sai zarya take tana yamutsa gashin kanta tare da ri’ke kungunta tunanin abubuwan da suka faru a baya kafin aurensu take”anya kuwa tayi masa adalci da hallaci a rayuwa…..?

“kasa sukuni tayi har zuwa sanda aka kira sallahr isha’i, gabadaya abubuwa ne suka shiga dawo mata, tun daga kan haduwar da fu’ad har zuwa rayuwar aurensu da rashin lafiyar NASREEN kawowa wannan matsalar dake faruwa dasu. tana kiyo sanda fu’ad ya fita tasan masallaci yaje dan haka jikinta a mace ta fito tashiga d’akin NASREEN taba abinci da magani sannan ta dawo daita parlour’n ta kwantar daita tare da yi mata makarin da pillow ,zata juyo kenan NASREEN ta riko hannunta “momy.. 

“yes dear kina son wani abu ne?

yarinyar ta girgiza kai tana dubanta sannan tace” momy meyasa bazaki zauna agida ki kula dani ba kmr yadda doctor yace? 

“nafi son ki zauna atare dani….. ..

shiru tayi ta tsura mata ido kawai tana kallonta ,NASREEN ba dai fitar da zance ba, idan tayi mgn xaka d’auka shekarunta ya wuce yadda take. 

“karki damu baby your dady will be with you zama agida akwai matsala, kinga babu wanda zai taimaka mana, ki duba nawa nake biya school fees dinki da sauran abubuwa idan nace zan ajiye aiki komai zai iya faruwa,kiyi hakuri dad dinki zai kula dake fiye dani kinji an… 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button