YANCIN KI Page 1 to 10

“yes ma.
ta fuskanci ma’aruf sosai “mr ma’aruf this is ur last warning dakazo min da waya meeting …..
sannan ahankali ta fuskanci gabadayansu tace “akwai millions of people out there looking for jobs.. “basu samu ba ,masu kwalkwaluwa sannan suka san yadda zasu sarrafa tunaninsu da kwalkwaluwarsu acikin kasar nan ba irinku dakikai ba, ku kun samu amman kuke iskanci , abinda yakamata ku godewa Allah dayasa kuka kasance cikin wad’an da ke aiki acikn company nan.
ahankali ta sake juyowa matukar fusace gefen da ma’aruf ke zaune sunkuye da kansa “mr ma’aruf..
ya d’ago da kyar yana amsawa da “yes ma.
“ina gargadinka da wannan iskancin naka ya zama karonka na farko da karshe okay “ina nufin karonka na karshe you dare bring ur stupid phone to my meeting, ” idan hkan takasance bazan koreka daga cikin meeting din ba, sai bayan nasa an tozarta min kai ,sannan nayi ratsaratsa da wannan banzar wayartaka sannan zanyi sack dinka daga aiki alright? takasara maganar a matukar hasale .”amshi banzar wayarka daga hanuna ta miko masa wayar tana me lumshe idanunta cike da ‘bacin rai ,yasa hannunsa ya kar’ba wayar tare da furta “thank you ma a dakile .
bata tsaya sauraresa ba tacigaba da magana cike da matsanancin bacin rai
“yauwa mukoma kan abu me mahimmanci da muke duscusing before..kafin wannan stupid din ya katse mana hanzari ” muna magana ne akan sabbin product dinmu na toothpaste da zasu shiga kasuwa acikin tsakankanin wannan lokacin “atakaice dai duk nasan kusan yadda muke son kasuwancinmu yakasance da yadda contains din fluoride dinmu zasu zo hannunmu ko ba haka ba?
suka had’a baki gurin cewa “haka ne ma.
“there is menthoi in it
“we are hering very good report on that as wel dan haka kowanenku yaje yayi nazari akan tautaunawarmu domin yana da matukar mahimmanci….
can hospital kuwa, gudu gudu sauri sauri teacher chioma take a dogon korido din hospitar , kunnenta mane da waya ,cike da tashin hankali ta cire wayar a kunneta tana dubawa tagani ko kiran ya tsinke , ganin datayi har lokacin Number na tafiya yasa ta sake meida wayar kunnenta biyu biyu ta dinga taka matattakalar benen “wayyo Allah, Allah kasa ta d’auki wayar har ta karasa sauka akan step din kokarin neman layin mahaifiyar NASREEN take …
bangaren me’ad kuwa tana nan tsaye tana cigaba da dogon bayaninta akan yadda take son company’s dinsu zai samu cigaba takowani bangare “dan haka we need to…….. karar sautin waya ne ya sake katseta ,kame ta kyam atsaye tana me runtse idanunta a matukar fusace tace “wayar wani tacencen d’an iskan ne ki ring kuma?
“waye wannan tantiri idiot din?
“waye wannan dolon daya bari wayarsa tayi ringing alhalin nace ko vibrating bana bukatar ji, take gabadayansu suka shiga duduba wayoyinsu, yayinda still wayar ke sake kara .
mr tahir wanda tun soma maganarta ya tsura mata idanunsa kawai yana kallon tare da cizan lip’s dinsa yana ji aranshi dakace yana da iko da tuni ya tashi ya yaryarfa mata maruka tsabar haushinta dayake ji,a duniya babu macen dayake jin ya tsana kamarta ..
“wani jakin mara jin magana da disobey ne yabari tsinanniyar culcuting dinsa ke damun kwalkwaluwar mutane..takarasa mgnr a fusace ?
daya daga cikinsu ne yace “madam ,ai wayarki ce ke kara.
gabanta yabada wani irin rassssssss tayi tsurutsuru da kyakkyawan idanunta tana kallonsu daya bayan daya ,zuciyarta na wani irin hamaukacin beting , yayinda har lokacin idanun tahir ke kanta yana kallonta yana ta’be baki ,wani irin abu taji tun daga tsakiyar kanta yana yawo daita har zuwa sansar jikinta tamkar an mata wanka da ruwan sanyi, kunya ce ko kuma nadama ce ta rufeta alokaci daya ita dai batasani ba cike da matsanancin mamaki ta tsurawa mutumin dayace wayarta ke ringa idanunta d’auke da karin bayani “yes it ur phone ma tahir ya sake maimaita mata ,ta juya bayanta ahankali inda ta’ajiye wayar tana duban screen din wayar jikinta na rawa rawa ,tabbas wayar ce ke cigaba da kara “kina iya d’auka madam watakilla kiran gaugauwa ne inji cewar mataimakinta…
tsawon minti goma tana duban screen din wayar batare da tayi kokarin d’auka ba , ta juyo jikinta a sanyaye tana fuskantarsu gabanta na cigaba da bugawa, tacigaba da mgn”muna magana ne akan fluoride da mentho sai kuma abu na gaba , yadda zamu shigar dasu kasuwa da wasu bangarori acikin kasashen duniya …
takasa cigaba da mgn”am..uhm ..am da kuma wanda daman a kasuwa ta kasa karasa maganar saboda yadda jikinta da bakinta ke rawa …
yayinda teacher chioma tacigaba da kiran wayarta babu kaukautawa har takaroso harabar hospital din tashiga zariya ” wayyo ni kam nashiga ukuna ta cire wayar a kunneta tana sake dealing “ina wannan matar ta ajiye wayar danaketa kira bata d’auka ba?
ta sake cire wayar a kunneta tana dubawa “ki d’auki wayar nan dan Allah ,still wayar ring take amman saboda tsautsauran ra!ayi irin na me’ad taki d’aukar wayar sai ma neman izini datayi agurinsu “one minti .. ta juyo inda wayar take still dai chioma ce take kiranta acikin zuciyarta take adduar Allah yasa wannan kiran ya zama kiran lfy, dan bata ta’ba kiranta irin haka ba .
tahir ne ya gyara zamansa tare shafa kasunbarsa yana kwa’be baki da fuskarsa yace “ranki ya dade ki d’auka mana killa zai zama kiran ne me mahimmanci.. tayi masa banza sai dai gabadaya ilahirin jikinta ya sake d’aukar rawa, ta d’auki wayar tana dubawa sannan ta mikawa daya daga cikinsu “can you take it to my office and just put it there for me? “idan kuma kagama karka dawo akan lokaci har mugaba gabatar da meeting kafin ka dawo, ya karbi wayar ya nufi hanyar fita ita kuma tacigaba da magana har yanzu dai muna magana ne akan flavor.. da kuma am uhmm wasu daga cikin flavor Wanda zamuyi amfani dashi acikin product ..
chioma takalli gabas da yamma tana kuka tare da girgiza kai”bata d’auka ba shikenan tawa tasameni ina cikin tashin hankali ta kwasa da gudu zata sake komawa cikin reception, direban da tun fitowar yake watsa mata harara cike da da jin haushin ‘bata masa lokaci datayi ya biyo bayanta da sauri yana kiranta “ke ke ina kuma zaki?
” dawo nan ina kudina dakike kokarin wucewa?
“ga wawa kinsamu ko, sai wani zariya kike awa jigida “kaga kayi hakuri mlm yarinyar da muka kawo har yanzu batasamu lafiya ba tukun mahaifiyarta naketa kira wayarta tayi ring ring amman bata d’auka ba dan Allah ka kwantar da hankalinka kaji zan baka kudinka.
“oho sai yanxu na fuskance inda kika dosa saboda ni wawa ne , nacigaba da tsayuwa agurin nan akan matsalarki har sanda wannan yarinyar me kama da macijiya zata warke kafin na tafi gidana ko”dan Allah malama ni bani kudina na kama gabana”kasan abinda zai faru yanxu ?
” dan Allah kabari naje nasamu doctor nagaya masa zai biyaka kudinka .
ta juya zata wuce yasa hannuwansa duka ya janyota “na fahimta ..”na fahimce maganarki amman miko wayarki nan “ka kwantar da hankalinka zan sa abiyaka kudinka.
direba yace “ina wallahi bazan yarda ba ni dai miko min wayarki kawai najita a hanuna idan kin koma gurin doctor idan yabaki kudin alabashi sai ki dawo ki karbi wayarki. ya kwace wayar ya koma jikin motar ya jingina jikinsa zaman jira , ita kuma ta juya da sauri tana magana “shikenan naji ai ba laifinka bane kwata kwata baka da laifi ,laifin wancan shashar uwar tatace dataki daukar wayar ..