YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 1 to 10

“yasara wace irin mata yake aure data fi bawa aikinta mahimmanci akan diyar cikinta dashi karon kanshi, a tun sanda ya aureta har zuwa lokacin data haifar masa NASREEN bai da kwamciyar hankali, kasancewar aikinta data fifita akansu ,yayinda su kuma suke matukar bukace da kulawarta ,a matukar fusace ta suri hand bag dinta tayi hanyar waje tabarshi tsaye yana sake duban gadon da NASREEN dinsa ke kwance tana fidda numfashi ahankali hawaye na bin gefen idanunta, ahankali ya karasa bakin gadon yana cigaba da dubanta ya kai hannunsa ya shafa sumar kanta yana me jin wani irin ajikinsa, yana jin ina ma yana da hali,wallahi daya cire ciwon ya meida jikinsa domin shi yafi dacewa da wannan ciwon bakaramar yarinyarsa ba.

” yana matukar son NASREEN arayuwarsa baya son bayason abinda zai ta’ba masa lafiyar jikinta ita kad’ai garesa.. ita kad’ai Allah yabashi a tun tsawon shekara goma dayayi aure ,kusan minti goma ya d’auka tsaye agurin yana kallonta yana Shafa sumar kanta hawaye na gangarowa ta gefen idanunsa ,ya ciro hanky cikin aljihun gaban rigarsa ya goge hawayen sannan ya gyara gashin daya zubo wanda ke kokarin rufe mata fuska sannan ya fito daga cikin d’akin.

” abinda yabashi mamaki ba wuce ganin me’ad tsaye abakin kofar d’akin tana jiran fitowarsa ba, wanda shi a tsamaninsa ta dad’e da isa office din doctor, dogon tsaki yaje a fusace ya wuceta yana Allah wadai da halinta har ma da mata masu irin halinta. 

har suka Isa office din likita tunani yake ta yadda zaiyi da al’amarin me’ad gabadaya zuciyarsa tasoma tsirewa da halaiyenta abubuwa dayawa zuciyarsa ke raya masa akanta…. 

doctor najin motsin shigowarsu ya d’ago yana nuna musu gurin zama sannan ya sake meida kansa kan file din NASREEN dake gabansa, ahankali fu’ad yaja daya daga cikin kujerun dake gaban doctor ya zauna yana ware kafafunsa tare da jijiga kafarsa daya, itama dayar kujerar kusa dashi taja ta zauma tana cicci magani.. 

zaune suke gaban doctor suna jira daga garesa, doctor ya numfasa kana ya sake d’ago idanunsa yana dubansu daga bisani ya mikawa fu’ad hannu suka gaisa .

doctor yace “ammm ..i salute ur courage for all your effort on your child, Allah yabata lfy yasa muci amfanin yaranmu gabadaya.. 

ahankali suka had’a baki gurin amsawa da “ameen kana suka ja bakinsu sukayi shiru suna sauraron doctor. 

doctor yacigaba mgn “amm thank God NASREEN has been responding better to treatment now, better than before but her condition now is some what critical than before. 

me’ad ta zaro idanuwanta waje tare da dafe daidai saitin zuciyarta tana duban doctor “inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ,” wannan wani irin tashin hankali hk ,ya Allah karkasa nashiga uku akan yarinyar nan …. takarasa mgnr jikinta na wani irin rawa, take kuma hawaye yasoma ciccikowa a idanunta .

fu’ad batare da ya kalli inda me’ad take ba yace “doctor ban fahimci zancenka ba .

doctor yace “no, just calm down okay , it’s not as if her condition is that critical but you know she’s a sickle cell patient ,there for, she need a lot of attention.. wanda nake tunani dole daya daga cikinku zai ajiye aikinsa at least for a mouth domin bawa NASREEN kulawar data dace .

atare gabansu yaba wani irin rasssss saboda jin abinda doctor yace… 

“saboda zaman daya daga cikinku yana da matukar mahimmanci domin irin magungunan dazamu bata yana bukatar kaida,domin ana bukatar ta dinga shan maganin akan lokaci zuwa lokaci ,and most importantly, she need ur care, love and attention more than before…

” atakaice dai yarinyarku na bukatar kulawarku da duk wani abinda iyaye yakamata suyi domin kwantarwa ya’yansu da hankali, me’ad tayi tsuru tsuru da idanu tana sauraron doctor daki daki tamkar zata shige cikin tunaninsa, yayinda fu’ad yayi shr kawai a tun sanda doctor yasoma bayani kai kawai yake girgizawa tare da had’e hannuwansa guri daya yasanya tafukan hannunwansa ya rufe fuskarsa dashi, shi kad’ai yasan irin rad’ad’in da zuciyarsa take ciki akan wannan matsalar… 

fu’ad ya cire hannunwasa yana duban doctor da idanunwasa da suka gama canza kala “doctor idan na fahimci zanceka sosai wani daga cikinmu zai natsar da zuciyarsa ya zauna tare daita ? 

doctor yace “haka nake nufi saboda kulawarku is very important agurinta. 

“saboda ina yawon samum masu irin lalurarta amman yadda nayi muku bayani haka nake treated a similar case dinta, before wani lokaci sai kuga yaro yasamu lafiya ,ina tunanin wannan tsarin dana kawo muku ,zai samu kar’buwa domin itama ina son tasamu irin wannan kulawar daga gareku ,ina me tabbatar muku matsawar daya daga cikinku zaiyi kokarin bata gudumuwarsa wallahi zakuyi mamakin yadda yarinyarku zata dinga samun saukin ciwon … 

“dan haka atsakaninku sai ku zartar da wanda zai zauna gida tare daita, ka ko ba dan komai ba dan Allah kod’an saboda ni ku taimaki rayuwar tilon diyarku dan Allah you guy’s should do this. 

murmushin fariciki me’ad tayi tana duban doctor “no no karka damu doctor da wannan matsalar Inshaallahu zamu san abin yi ,ai wannan bazai zama wani abun damuwa ba ,dan tabbas zamuyi yadda kace zamuyi magana da juna idan muje gida..

docto yace” thank you. 

shi kam fu’ad shiru yayi yashiga duniyar tunanin yadda abinda Doctor yace, gabadaya ya kasa magana saboda cajin da kwalkwaluwarsa ke yi, yana jin kmr ya zubda hawaye ne akan NASREEN yana matukar tausayawa rayuwar yarinyar ahankali ya juyo ya dubi me’ad dake zaune a gefenshi ,ganin murmushi kwance akan fuskarta, ya d’an sanyaya masa zuciya ,hannusa me’ad ta riko cikin tafin hannuta tana murzawa, da kyar yasamu ya mike tsaye suka fice daga office din likita zuwa d’akin da NASREEN take kwance , tare da sanyata gaba suna dubanta gabadaya ta sake ramewa , ji suke ina ma ciwon ya dawo kansu ta tsira da lafiyata… 

 

daren ranar sam me’ad da fu’ad basu samu damar runtsawa ba ,hatta bacci barawo wannan karon baiyi nasarar d’aukar daya daga cikin iyayen NASREEN ba, tunani kawai suke ta yadda al’amarin zai kasance, “cikinsu waye zai ajiye aikinsa domin bawa yarinyarsu faricikin da kulawar data dace ? 

“shi ne zai tallafi rayuwar diyarsu ya zauna agida ko me’ad da rayuwarta ce kawai ,bazata iya bawa aikinta ba, saboda mahinmmacisa gareta? fu’ad ya tambayi kansa yana satar kallon inda take . har kusan asuba fu’ad na zaune rike da hannu NASREEN ya tasata gaba yana kallonta still hannunta daya cikin nasa, yayinda me’ad ke tsaye bisa kafafunta tana kaiwa allah kukanta daman ita macece me yawon ibada, kullun daren duniya bata runtsawa batare da tayi ganawa ta musamman da ubangijnta ba, ita din mace me yawon ibada da kamewa tare da tsayuwar dare ,a duk inda ta tsinci kanta zata tabbatar da ta tsaya bisa kafafunta gurin bautawa Allah, illarta daya saurin d’aukar zafi akan abinda bai kai yakawo ba, da kuma d’aukar aikinta da mahimmanci datayi akan bawa yarinyarta kulawar data dace .. 

kwanansu daya aka sallamosu daga hospital suka nufo gida tare da jakar magagunguna ,yinin ranar da suka fito daga hospital me’ad na d’aki tare da NASREEN rungume ajikinta tana shafa sumar kanta tana zance zuci kasancewar week end ce ranar babu aiki “Allah sarki haka hukuncin Allah yake gashi dai daga ita har mahaifinta lafiyarsu kalau basu d’auke da wata lalura sannan su ba ss bane balle as, gabadayansu aa ne , gashi sun haifi sickle cell ..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button