YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 1 to 10

  “ina matukar sonki NASREEN dina ,Allah ka raya min ita,saboda banason rasata arayuwata duk da kasancewarta sickle cell kabarni na rayu daita ,Allah karka jarabeni darashinta ” hakika wannan matsalar yancine gab iyaye mata akan yaransu naganin sun kula dasu sosai fiyye da komai hawaye ne ke gangaro mata daga cikin kwarnin idanunta .

ganin baccin NASREEN yayi nisa sosai yasa ahankali ta lalla’ba ta kwantar daita tare da sanya pillow tayi mata makari dashi had’e dayi yi mata kiss a goshinta sannan ahankali tashiga shafa sumar kanta tana jin wani irin tsantsar tausayin yarinyarta me gauraye da kauna mara iyaka, ta lullu’beta da blanket me taushi , sannan ahankali ta sauko daga kan gadon tasanya takalmanta ta d’auki tire dake ajiye akan bed side Wanda ke d’auke da ruwan databawa NASREEN magani ta sha, bud’e kofar d’akin tayi ta fito, kai tsaye main parlour’n din gidan ta nufa yayinda fu’ad ke zaune akan doguwar kujerar dake zagaye da parlour’n ,sanye cikin jallabiya ash colour kafarsa daya ya lankwasashi karkashin dayar kafarsa, yayinda dayar kafar ke mike system ne agabansa wanda ya d’aurashi akan cinyarsa ,yana dane dane tare da tura sakonnin , tazo ta wuce shi tashige kitchen sanye da wata yar karamar riga iya cinyarta da hula net wanda ya bayyana gashin kanta .

ta ajiye tiren hannunta sannan tasoma 

gyaran kitchen tare da goge koina daga karshe ta isa gurun gas tana gogewa tana tunanin wanda zai ajiye aikinsa acikinsu domin bawa yarinyarsu kulawa ,aiki take sai dai zuciyarta na can ga satar kallon fu’ad dake zaune yana aikinsa, saboda farin glass dake tsakanin kitchen dinta da parlour’nta bai hanasu ganin juna ba, duk wanda ke zaune a parlour’n tabbas zai hango wanda ke cikin kitchen, haka zalika wanda ke cikin kitchen zai hangi na parlour, yayinda har wannan lokacin fu’ad na zaune wanda ya mike kafafunsa yacigaba da aikinsa hankali kwance yajiyo sautin muryarta daga cikin kitchen “honey .

batare daya d’ago kansa daga abinda yake yi ba yace “yes love… 

“should i serve you food now? 

“no just give me 5 minnutes i must finish this project, it’s due on Monday…. 

cak ta saida abinda take yi tare da shiga wani yanayi na bugawar zuciya kana a tsanake ta juyo tana fuskartashi “zakayi sumint dinsa on Monday fa kace? 

yace “eh zanyi sumint dinsa ranar monday saboda mahimmancisa .

 da auri tasoma kokarin fitowa daga cikin kitchen bakinta bud’e sannan cike da matsanancin mamaki tasoma magana jikinta har rawa yake ” honey wace monday kenan kake magana akai? 

“Monday jibi mana ya bata amsa, batare daya d’ago ba yacigaba da danne dannesa. 

“ta dubesa a kaikaice tana sake mamakin jin abinda ya fad’a tayi kusa dashi sosai ta yadda kowanensu zai iya fuskantar d’an uwansa “meyasa zakace zaka gurin aiki ranar monday ?

“ko ka manta abinda Doctor ya fad’a mana ne ?

“me doctor yace mana ? 

yayi mata tambayar yana me dakatar da abinda yake sannan ya d’ago ya fuskanceta .

“haba ya kake kokarin ka manta, akan NASREEN mana. 

“eh doctor yace dole cikin ni dake wani ya ajiye aikinsa ya zauna gida tare daita .

“yauwa a she baka manta ba. 

fu’ad yace “so what are you talking about? 

me’ad ta soma fusata dan haka a zafafe tace “what do you mean by.. that, dole mutun daya zai ajiye aikinsa ya zauna tare daita agida ..

“uhmm wannan kuma ai aikinki ne, ki zauna gida tare daita, ta yaya kike tunanin ni na ajiye aikina na zauna gida? 

“this is common sense now it’s your duty a matsayinki na mace” ni me zan zauna nayi a gida?

 yakarasa mgnr ahankali yana kallon cikin kwayar idanunta, gefe daya kuma wani irin bugawa zuciyarsa keyi da sauri sauri . 

ahankali ya numfasa kana yace ” kiyi tunani sosai me’ad akan wannan lamari kodayake bai zama lallai ki gane, abinda nake nufi ba tunda baki aiki da kwalkwaluwarki ya fad’i hkn yana nuna gefensa kansa.. 

“no no fu’ad banason irin abinda kake min “and you know I don’t like all this can of thing kasan sarai banason kana min magana kana ta’ba kanka domin kokarin meidani mahaukaciya mara tunani.. 

ya sake kai hannusa daidai gefen kansa “wannan ai common sense ne ,kema kuma kinsa da haka ,yakamata amatsayinki na mace tunaninki yagaya miki akan kece zaki zauna agida bani ba .

dakata fu’ad “automatically, its your duty to stay with her .

“for what? 

“me kake nufin akan saboda mai?

“okay tunaninki nabar aikina na zauna agida alhalin ga ki ….

“me kake nufi da bazaka bar aikinka ko me ko me? 

“kai kanka kasan kai yafi dacewa ka zauna agida tare da yarinyarmu kasan wannan. 

“gsky bakida hankali da tunani wallahi ,kwata kwata tunaninki baya gaya miki gasky da har kike expecting ni yakamata na zauna gida tare da NASREEN alhalin gaki mace kina nan baki mutu ba . 

“nasan aikina nane, ba sai ka gaya min ba, ta hanyar meidani tamkar mahaukaciya ,”amman ni aikina yana da matukar amfani ga rayuwarmu gabadaya, dan hk ko kaki ko ka so you will be the one that wel stay at home with our daughter…… 

“wannan ai akinki ne me’ad meyasa kike kokarin meidashi kaina. ?

“i know but my job is mo..re more important you just can’t tell me to what’s my du… 

sautin tarin NASREEN ne yakatse mata hanzari ..tarinta kawai suke jiyowa babu kaukautawa da wani irin sauri fu’ad ya zabura ya mike tsaye jikinsa na kyarma “kingani ko kinga abinda maseefarki zai haifar ko dan.. ..ai kafin yakarasa fadar abinda yake son fad’i tarin ya sake yin karfi ai da wani irin mugun sauri tayi hanyar d’akin NASREEN aguje tana ihu kiran sunanta ….. 

mmn sudais ce

????????????????????????

       ‘YAN CINKI

      ????????????????

????????????????????????

             ~NA~

 *AYSHA A BAGUDO*

~DEDICATED TO~

      MRS ADAM

( YAR MUTAN KAGARA)

page 16 to 20

…….aguje suka karasa shiga cikin d’akin, kowannensu na rige rigen isa inda take zaune dafe da kirjinta tana cigaba da tari tamkar ranta zai bar gangar jikinta, da sauri fu’ad ya haye saman gadon ya janyota zuwa jikinsa ya rungumeta yana kiran “sorry baby!!! 

yayinda gabadaya ilahirin jikin me’ad ya d’auki rawa “tarasa me ma zatayi ,sai sambatu take “me kuma ya sameki baby nah ? 

“some one should help me plz “wa meye hk ne.. ..?

zagayowa tayi dayan gefen ta haye gadon tana maimaita “me yasa meki baby nah ?”dan girman allah ki sausautawa zuciyarmu bazamu iya jure kallonki cikin wannan tashin hankali ba. “ya ubangijin ka taimakeni kabawa yarinyata lafiya tayi rayuwa kmr sauran yara. 

NASREEN tayi tari da karfi tare da cewa “da..dady wa…water.. 

a matukar firgice yace ” watare me’ad give me water plz ….. 

me’ad wace ta sake rikicewa tace uhmmm water ? 

“dan Allah malam kije ki kawo min ruwa yanzu yayi maganar a fusace .. “sorry honey, ta duro daga kan gadon ta tsaya sanya takalmanta .

“a fusace yace run now. 

” i am runing “im runing !!

ta bud’e kofar da karfi ta fice batare da ta tsaya rufo kofar ba. 

“ahankali fu’ad yashiga jijiga NASREEN “sorry my baby ,”Inshaallahu zakiji sauki,yashiga shafa kirjinta yana dubanta. 

da matsiyacin gudu me’ad tashige kitchen, madadin ta bud’e fridge ta d’auko ruwa kmr yadda ta shigo da niyyar yin hk, sai kawai ta hau zariya acikin kitchen din tana zagaye kayayyakin amfani tsabar rud’ewar datayi.. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button