YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 1 to 10

 da kyar Allah ya taimaka tasamu ta bud’e kitchen cabinet ta d’auki cup sannan cikin sauri ta dawo ta bud’e fridge ta d’auki robar ruwa nestly water ta fito da mugun sauri . 

 NASREEN kuwa tarin datake sai gaba yake, gbdy ta kamkame ajikin dad dinta, tana tari babu kaukautawa abun gwanin ban tausayi, jikin fu’ad na rawa yace “kiyi sauri mana kin … bai karasa ba, sai gata ta shigo d’akin da sauri , ta mike masa cup dake cike da ruwa, ya amsa ya kai daidai bakin NASREEN “sorry baby take some water kinji, NASREEN tasoma kur’ban ruwan ahankali ahankali. .

me’ad ta zauna tare da raku’bewa agefen fu’ad tana duban yadda yarinyarta tasoma galabaita .

NASREEN tasha ruwa kad’an tana sake yin tari “sorry my baby “ki d’an kara shan ruwan kiji, inji cewar fu’ad still tana makale ajikinsa .

jiki a sanyaye me’ad” tace sannu baby nah Allah yabaki lfy, sai da fu’ad ya tabbatar data sha ruwan sosai sannan ya tambayata “ruwan ya isheki ?

ta d’aga masa kai ala’mun eh sannan ya mikewa me’ad cup din batare daya kalli inda take ruku’be ajikinsa ba .

ya rungume diyarsa tsam ajikinsa ,yana shafa mata baya yana sake yi mata sannu , itama me’ad kwantowa sosai tayi jikinsa tare da d’aura hannuta a jikin NASREEN tana mata sannu, banda sautin sannun da suke mata baka jin sautin komai a d’akin ,gabadaya hankalinsu da natsuwarsu yabar gangar jikinsu ,ya tattara ne ga tilon diysrsu ,kowanen daga cikinsu ya kasa d’aukar ciwon nata da sauki, ciwon NASREEN a zuciyarsu yake , sai dai dukkaninsu sun kasa aiwatar da abinda likita ya fad’a musu akan nuna wa yarinyar soyayya da kulawa har ma da bata natsuwar zuciya shine zai sa tasamun cikakkiyar lafiyarta . 

tsawon minti talatin suna tare daita , suna aikin yi mata sannu ,ahankali muryar yarinyar ta fito “mummy come and sleep here with me, takarasa mgnr tana nunawa uwar gefenta da hannunta daya. 

jikin me’ad na kyarma tace “you mean there ta nuna inda NASREEN ta nuna da yatsan hannuta .

NASREEN tace “yes mumy , take me’ad ta yunkura tabar jikin fu’ad ta zagayo gefen inda NASREEN ta nuna mata tana furta kalmar “okay my baby. 

fu’ad ya kwantar da NASREEN yana shirin mikewa tsaye domin barin d’akin, yaji NASREEN ta riko tafin hannunsa cikin nata “dady sleep here too. 

“na kwanta anan kikace? 

“yes both of you are sleeping here with me . 

me’ad ta kwanta gefenta na dama, haka shima fu’ad ya kwanta gefenta na hagu ,suka sanyata tsakiyarsu tare da lullu’be ta da bargo ,sannan suka tsura mata idanunsu suna kallonta cike da matsanancin kauna.

ahankali NASREEN ta matso jikin dad dinta ta kwanta ajikinsa tana sauke numfashi, dan kusan tafi son babanta sau dubu akan mamanta, domin dad dinta yafi bata kulawa ba tun yanzu ba ,sabanin mahaifiyarta datake nuna tafi son aikinta akanta ….

shiru fa’ad yayi yayinda hannusa ke saman kafad’ar NASREEN yana shafawa ,ahankali yake tunanin abubuwan da suka faru awanin 20 da suka gabata tsakaninsa da rikitacciyar matarsa, sannan ya d’ago kansa cike da jin haushinta, suka had’a ido da me’ad, bai tsaya wata wata ba ya zabga mata harara me tattare da tsantsar danasanin aurenta dayayi arayuwarsa. 

itama batare da ‘bata lokaci ba ta rama tana kwa’be masa baki,har NASREEN tayi bacci suna kwance agefenta suna aikawa junansu harara. 

daga bisa ta sauko daga kan gadon ta zagayo tana kokarin bud’e kofar d’akin, zaraf taji fu’ad ya riko laulausar tafin hannuta cikin nasa yana massaging ahankali ahankali yana cigaba da dubanta tare da jin wani sauyi ajikinsa gbdy taji jikinta yayi wani irin laushi ,amman ta dakewa zuciyarta ta sanya dayan hannuta ta zare hannunta cikin nasa, takarasa ta bud’e kofar ta fita .

shima ya mikewa yayi tsam yabiyo bayanta bayan ya gyarawa NASREEN kwanciyarta tare da lullube mata rabin jikinta, atare suka shiga d’akin nata, tana karasa shiga tayi bayi ta barshi tsaye jikin kofar dakin yana aika mata da wani irin kallo dake kashe mata gabobin jiki. 

batayi cikakken minti biyar a bathroom ba ta fito d’aure da farin towel iya cinyarta wanda ya bayyana santala santalar cinyoyinta dake fitar da wani sheki da hasken kyau kmr wace take amfani da madara ko yougot, yayinda zuwa wannan lokacin fu’ad yayiwa kansa mazaunin a gefen gadonta tare da jingina rabin jikinsa da pillow ya mugun tsurawa kofar bayin ido. 

kallo daya tayi masa tasan abinda yake nufi da wannan biyota din dayayi, tasan bawai wuce jarabarsa ce taciyosa ba ,ita kuma duk abinda zaiyi sai dai amman bazata bashi had’in kai ba, ta gabansa taxo ta wuce tana goge sansar jikinta da wani karamin towel , ta isa gaban mirrow tana jujjuya jikinta da mazauninta Wanda yasa joystic din fu’ad harbawa da sauri,take ya matse joystick dinsa da kafafunsa tare da runtse idanunsa, yana jin dama bai kawo kansa ba,dan gabadaya yanayinta yagama nuna masa irin rashin mutuncin dake tattare daita. 

ahankali me’ad ta d’auki body lotion dinta na so white tasoma shafawa sansar jikinta .

“me’ad idan kingama kizo ina bukatarki …… , tayi masa banza tacigaba da abinda take, sai data gama murazawa jikinta , lotion sannan ta d’auki turarenta na oud moon ta feshe jikinta dashi sannan tasoma kokarin karasowa inda pray mate yake, ta daidaita tsayuwarta da niyyar zata fara sallah taji sautin muryarsa ya doki cikin dodon kunneta me’ad ! me’ad!.! ya ambaci sunanta a karo na biyu cikin d’aga murya da yanayi na fushi da kosawa… 

lokacin daya fahimci bata da niyyar amsawa saboda har ta tayar da sallah ya d’aga murya cikin zafin rai ya buga mata tsawa mai firgitarwa, yace “ke me’ad ba dake nake magana ba ne kika tada sallar da babu lada acikinta sai tarin zunubi ? 

“ina matsayin mijinki ace ina miki magana tun kafin ki tayar da sallah amman bazaki amsa min ba, kiyi sallar amman ki tabbartawa kanki baki da lada ko kwaya daya kasancewar kinsa abinda ke tafe dani gareki.. 

wannan karon har ta kai raka biyu na nafila har ta sallame amman ko d’aga kai me’ad batayi ba ballanatana ta amsa masa har ma yasan ko tasan da zamansa agurin , al’amarin daya sake daga masa hankali kenan da firgitarwa, domin duk lokacin da wani abu zai gindaya tsakaninsu, sai tayi yunkurin tauye masa hakinsa wanda yasara dalilin hk, wani lokacin ko zata bashi had’in kai sai yayi sha wahala da karfinsa koda kuwa hkn bazai wa zuciyarta da gangar jikinta dadi ba.  

zuciyarsa kamar zata fashe ganin ta sake mikewa ta tayar da wata sallar, muryarsa da jikinsa rawa suke yace “wallahi wallahi me’ad kina cikin halakakkiyar rayuwa matukar baki saurari uxirina ba, har abada bazan yafe miki hakina da kike dannewa ba . ya mike tsaye da kyar yana layi tmkr wani mashayi gbdy yanayin idanunsa sun sauya haka ma gangar jikinsa ya sauya .

yasoma kokarin barin d’akin.. me’ad ta gaugauta sallamewa ta mike tsaye tasha gabansa tana dubansa a matukar firgice kirjinta na wani irin bugawa, tsoro da matsananci firgici fu’ad ke hangowa cikin idanunta, sake matsowa tayi kusa dashi sosai kmr zata shige cikin jikinsa tare da kamo hannuwansa duka cikin nata still tana kallon kwayar idanunsa ,ya kawar da fuskar gefe saboda a yadda yake jinsa zai iya marinta had’e dukan mutuwa . 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button