YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 11 to 20

ASALIN MAHAIFINKIfu’ad Muhammed argungu d’an asalin karamar hukumar argungu ne dake jahar kebbi, cirani ne yashigo da kakaninsa garin lagos , wato malam musa da mai d’akinsa halima da yaronsu muhammed , inda sukayi masauki a unguwar g’begulori dake karamar hukumar agege, fu’ad bakabe ne daya fito daga cikin kabawan asalin jahar kebbi ,yayinda danginsa gbdy suka kasance talakawa ne tulis .

tunda malam musa ya dira a garin lagos bai ta’ba zama daidai da rana daya da sunan hutu ba, kullun yana fita neman abinda zai ci da iyalisa ,ba wata sana’a malam musa yake ba illa aikin dako cikin kasuwar matuwaf zuwa ketu ,Allah yasanyawa aikin dakonsa albarka domin basu ta’ba neman abinda zasu ci sun rasa ba ,kuma tun daga kan muhammed Allah bai sake basu haihuwa ba ,dan haka suka d’auki soyayyar duniya suka d’aura akan tilon d’ansu da Allah ya basu ,duk da kasancewarsu talakawa amman hkn bai sa sunyi sakaci da tarbiyar yaronsu ba ,suna iyakacin bakin kok’arinsu akan ganin sun inganta rayuwarsu data d’ansu ,domin sunyi kok’arin sanyashi makaranta gwanati dan samun cigaban rayuwarsa .

“haka rayuwarsu tacigaba cikin talauci da babu har yasamu ya kammala secondary school dinsa a ikeja high school daga nan bai cigaba da karatu ba , sai dai ya Kan fita buga bugarsa duk inda yaga aikin karfi zaiyi fassakare ne wanki da guga zaiyi . Muhammed ya taso tare da mahaifansa har zuwa girmansa , kafin Allah ya had’ashi da ramlat, wace suka kasance diyar makotasu ce ,sukayi aurensu bisa amana da soyaya.

fu’ad shi kad’ai iyayensa suka samu ya tsaya a duniya ,dan haihuwarsu biyar yaran suna mutuwa akansa suka samu ya tsaya wanda sanadiyyar haihuwarsa, mahaifiyarsa 

 ta rasu ,a cewar mutane bama tasan abinda ta haifa ba ta cika, sai rikonsa ya dawo gurin kakaninsa, lokacin daya kai shekara bakwai mahaifinsa ya rasu sakamakon ciwon hawan jinin daya kamu dashi a tun mutuwar matarsa ramlat, ba a d’auki wani lokaci me tsawo ba malam musa shima yace ga garinku. gidan ya saura daga halima sai fu’ad.

fu’ad yayi karatunsa na primary har zuwa jami’a ahmadu bello, bisa tallafi na gwanati da taimakon Allah dana kakarsa inda ya karanci business administration.

 ,fu’ad ya sha matukar wahala gurin karatunsa saboda rayuwar babu da suke ciki ,da taimakon scholarship dana abokai da tsohuwar kakarsa halimatu yasamu ya kammala karatunsa da kyar ,bayan kamala karatunsa da bautar kasa yashiga wahalar rayuwa sakamakon rashin samun aiki , kafin had’uwar sa da mom dinki ya kwashe shekaru sama da shida yana zaman banza batare da yasamu aiki ba duk da kyawun da takardunsa sukayi.

” sun had’u da me’ad ne 

A wata safiyar litinin .

 labari ya karad’e koina akan zance batakashin da’akayi a garin lagos duk gidan tv da radio daka kuna a lokacin fuskar ACP Aliyu rano ake nunawa da tawagarsa rike da bindigunsu suna harbi .

  ni da fu’ad ne muka shiga cikin wani d’an madaidacin shago inda muka saba yada zango ,muna shiga na ja na tsaya ina murmushin jin dadi,yayinda fu’ad dake tsaye a bayana yasa hannusa ya buge min keya “banza kawai munafukin Allah ,gulma nacinka ko?

bud’ar bakina sai cewa nayi “abokaina yau fa fu’ad yayi kasuwa da ala’mun shima yau ya fad’a tarko kauna nakarasa mgnr ina kwashewa da dry har da tafa hannu.

“kajika da wani zance iska inji cewar sauran abankanmu, sudais, Abdul da kabeer .

 kabeer yacigaba da magana idanunsa na kan kallon tv “yayi kasuwa fa kace kmr wani kayan marmari.

“allah kuwa yau naga qunjinsa domin ya had’u da yarinyar da bazai iya hakura daita ba.

” dan Allah malam karka damemu zauna ka kalli abinda duniya take ciki.. zaro ido nayi sa sauri lokacin da idanununa ya sauka akan TV “kai kai ai naga wannan mutumi da’ake nuno yanzu , wannan batakashin da kuke kallo agabana fa akayisa ,shi dai fu’ad bai ce komai ba yakarasa kan doguwar kujera ya zauna yana duban abinda ake nunowa a TV wanda agabansu komai ya faru. 

“kana nufin ka ganshi inji cewar kabeer? 

“Kwarai da gaske na ganshi da idanuna, “kai dai wallahi babban makaryaci ne ,yau kuma da karyar daka zo mana kenan?inji cewar abdul ..

 “Na girgiza kai tare da kallon fu’ad ,”fu’ad dan girman allah kayi magana zasu fi yarda da maganarka saboda muna tare da kai lokacin da abu ya faru .

fu’ad na jinsa ya sake mikewa akan doguwar kujera yayi kwanciyarsa tare da lumshe idanunsa duka , ya d’aura hannunsa ya dafe goshinsa dayan hannunsa na saman ruwan cikinsa, kasancewarsa marason hayaniyya.

duk surutun danakeyi banza sukayi dani suka cigaba da sauraron labarin da’ake watsowa suna kur’ba ruwan Lietop.

” kunga wallahi da gaske nake kai dai fu’ad wallahi banza ne ,kana ji ana kokarin meidani makaryacin karfi dayaji amman kayi shiru.

“me ka keson nace fu’ad ya fadi hkn atakaice batare daya bud’e idanunsa ba. 

“ka gani ba dan Allah kayiwa mutane shiru, shi kansa fu’ad din bashi da tabbas da zance dake fitowa daga cikin bakinka duba da yanayin da yayi magana to yaya kake son mu dake zaune agida mu yarda bayan karyar abincin ruhinka ne daka kashigo fa zance yarinya kake yi ,cikin minti biyu kacal kasanyo wani zance daban .

 “eh naji karya abincin ruhina ne, amman wallahi wannan zance ba karya bane ,koda nasaba yi muku karya ,ku matso kuji yadda abun yakasance nakarasa maganar ina me zagayo na zauna akan table ,gabayansu suka zagayeni ” muna jin ka fad’i kuma wallahi kana somawa da karya zan gane ka kuma san karshen abun..inji cewar kabeer. 

“ina zaune wancan dan iskan yace na rakashi inji din ciro kudi ,muna isa aka fara ruwan sama tare da walkiyya.. nakarasa mgnr ina zabgawa kabeer duka ajikinsa “kai dan Allah malam da baki ake bada labari ba da hannu ba “yi hakuri abokina abinda idanuna suke hangomin ne abun birgewa ,tsawon lokaci muna tsaye har ruwan yasoma tsagaitawa mukayi tunanin mu fita saboda hango inuwar mutun tsaye”bude kofarmu ke da wuya sai naga wata kyakkwar yarinya kirar Japanese tsaye cikin doguwar rigar har kasa hannunta rike da lema ,kyakkwa ce yarinyar sosai ,ku tamabayi fu’ad dan lokacin na lura har yafini gigicewa akanta, amman sai naga ya waske ita kuma yarinyar idanunta na kansa ta tsura masa ido tana kallonsa, bud’e bakin yarinya keda wuya tace “sannu amman gsky kunjima da yawa sai wani zarar kudi kuke kmr wad’an da zaku cire kudin bank din duka.

nayi saurin cewa “dan Allah kiyi hakuri ai tuni muka cira , tsayawa mukayi domin fakewa ruwa ,amman bamu aron lemarki sai mun d’an tsaya daga waje ke km sai shigo idan kin cira sai mu dawo mu tsaya ana .

“a tunanina ni zatabawa lemar tunda ni nayi mata magana ta fahimta , amman sai naga ta mik’awa wancan dan isakan lema, ya nuna inda fu’ad ke kwance ,in dai takaice muku ko damuwa da kulawar data nuna masa bai yi ba ,sai ma zagayeta da yayi ya wuce yayi gaba ya tsaya tare da tura hannunwasa duka cikin aljihun wandonsa , ina lura da yadda yanayin yarinyar ya sauya, ba dan taso ba ta miko min lemar wanda kad’an yarage hannunmu bai had’e da juna ba, na matsa mata tashiga, ni kuma na fito na tsaya ina karewa halitar jikinta kallon , ina gaya muku kywaun yarinyar ya had’u sosai.cikin mintunan da basu wuce goma ba ta fito idanunta akan fu’ad ,sosai fa kura masa ido tana takowa zuwa inda yake tsaye. 

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button