TAKUN SAKA 39

*_Chapter Thirty Nine_*………..Duk da ba sanin mitake tattaunawa da zuciyarta yayi ba yaji a ransa yau ƙila har ALLAH ya isa sai tai masa. Tama nutsu ta tabbatar da shiɗin Isma’ill ɗinne ko wanine daban hakan ya gagara saboda rashin man kanta. Komai bai iya yace ba, yasa bargon kawai ya share mata hawayen da har yanzu sun kasa tsayawan. Wayarsa ya sake ɗauka dai-dai shigowar sabon saƙo. Yasan Abdull ne dan haka bai tsaya ɓata lokaci ba ya buɗe saƙon. Duk da dai sai da Abdull ɗin ya gama masa sheri irin nasa ya rubuto masa dukkan abinda ya buƙata baibi takansa ba. Kwantar da kanta yay bisa filo a ransa yanajin
haushin ya akaima baiyi tunanin yin duk hakan ba, duk da dai ba fitowa fili yay wajen gayama Abdull ɗin ba, shegen bin ƙwanƙoninsu ne kawai irin na likitoci zaisa ya fahimta. Toilet ɗin ya sake komawa yay duk yanda ya rubuto masa sannan ya dawo wajen Hibbah. Da ƙyar ya samu ta tashi tana faman masa raki. Nokewar farko da tai saboda babu kaya a jikinta ya sashi ɗaukar rigarsa dake gefe ya saka mata. Koda ya mikar da ita azaba ta sata faɗa masa jiki ta fashe da kuka.
Kansa ya ɗan girgiza da ɗaukarta dukanta kawai dan shi kansa wajen hutawar yake bukata. Ga tausayinta fal ransa dan shi bayason ganin mutum a damuwa dalilin sa. A banɗakin ma ba tsira yayiba. dan harda cizo ya sake sha. Ummi da su Yaya Abubakar kam sunsha kira matuƙa. Da ƙyar ya samu ya taimaka mata tayi yanda Abdull ɗin ya rubuto masa. Koda ya tambayeta batun wanka bata tankaba. Dan dama tunda suka shigo bata yarda tako kalli yatsan hannunsa ba idonta a rufe suke. Sai da yaja mata gargaɗi a kausashe sannan tayi, shi ya sake taimaka mata suka fito. Ya zaunar da ita a gefen gadon yasa karamin towel ya rage mata ruwan kanta. Gudun kar lokacin salla ya cigaba da shigewa ya sashi ɗakko mata wata doguwar rigan a kanyan da batasan a ina ya samoba. Shiya taimaka mata ta saka nan ma. Ya saka mata hijjab ɗin da faɗin, “Tashi kiyi salla”.
Wani irin bugawa ƙirjinta yayi a karo na biyu, saboda jin da muryar da yay magana sak na yaya Isma’il. Sai dai ta dake matuƙa na hana kanta dubansa ta tada sallan cikin layin rashin ƙwarin jiki har yanzu tana hawayen. Sauƙinta ma ta ɗanji daɗin taimakon ruwan zafin da yay mata duk da sai da ya haɗa da mazurai.
Sallar ma dai haka tayita harta kammala tana kuka. Yayinda shi kuma yake kimtsa gadon cikin mamakin abinda ya ci karo da shi. Bai daice komai ba ya naɗe zanin gadon ya hau duba wani a ɗakin kozai samu. Sai dai babu. Dole ya fito zuwa ɗayan ɗakin dake a sashen. Zanin gadon dake ajiye na gadon ɗakin ya dauka ya koma. Da kansa ya shinfiɗa cike da karfin hali. Gamawar tasa tayi dai-dai da kammalawar Hibbah sai dai ta kasa tashi a wajen.
Duk da ya fahimci ta idar baiyi magana ba. sai ma zama da yay a bakin gadon ta gefen ta yana latsa waya. Massege ya turama Habib akan ya kawo masa abinci ya ajiye a falo. Wayar ya ajiye yana maida hankalinsa gareta. “Kin idar?”.
Kanta kawai ta jinjina masa tana share hawayen da suka ziraro mata. Duk da ya fahimci kukan take baice komai ba ya miƙe ya fita a ɗakin. Yasha mamakin iske abincin da yasa Habib ɗin ya kawo harma da wanda baiceba. Dan harda magunguna a leda. Tambarin jikin ledar maganin ne ya sashi shan jinin jikinsa. A fili ya furta “Abdull”. Aljihun wandonsa ya ɗan laluba domin cirar wayar sai ya tuna ya barta a bedroom. Dan haka ya ɗauka abincin kawai ya koma. A inda ya barta anan ya sameta, sai dai yanzu ma ta sake haɗe kai da gwiwa.
Komai baice mata ba har sai da ya haɗa mata abincin, cikin dakewarsa, dan ya fahimci lallaɓawar bazatai masaba, Hibbah bahaguwar mutumce kuma zuma ce sai da wuta. yace, “Tashi kici abinci”.
Ɗagowa tai, dan muryarsa kawai razanata takeyi a halin yanzun. batare da ta yarda ta kallesa ba cikin rawar muryar kuka tace, “Na ƙoshi, dan ALLAH ka kaini wajen Ummi na, inason na ganta”.
Maimakon ya amsa mata sai ya miƙa mata kofin tea kawai. Ganin taƙi amsa, tamaƙi ɗagowa ta dubesa ya kamo hannunta ya ɗaura kan kofin. “Baki gaji ba kenan mu koma a ƙara”.
Da dauri ta amshi kifin jin abinda yace, yay gajeren murmushi yana ɗauke kansa daga kallonta. Uziri ke garesa na fita, gashi babu dama baima san yanda zaiyi da ita ba. Tsoro da yunwar da takeji ga zazzaɓi yasata shanye tea ɗin akan lokaci ta ajiye kofin, komai baiceba anan ma ya ɗauka ledar maganin ya duba. Ƴar takardar da yaci karo da ita a cikin maganin ya warware ya fara karantawa. Yanda duk za’a sha maganin ne a ciki, sai ƴar tsokanar da yay masa a ƙasa wadda ta sashi sake tabbatar da zarginsa akan Abdull ɗin yana kusa da shi. Ajiyewa yay ya ciri maganin ya bama Hibbah. Babu musu ta amsa ta sha.
“Wai nikam baza’a kalleni ba?”.
Yay maganar yana ƙoƙarin ɗago haɓarta ganin taƙi yarda koda kuskure ta dubesa. Idanunta ta rumtse hawaye suka ziraro. “Kuka dai, kuka dai babu hutu?. Bakisan yanzu ke kin girma ba ne? Kin tashi da ga autar Ummi, shalelen su yaya Muhammad. Nanda ƙanƙanin lokaci za’a fara kiranki Mamy insha ALLAH ”.
Sake fashewa tai da kukan tana ture masa hannu da juya kanta gefe, sai hakan ya bashi dariya. Amma yay ƙoƙarin gimtsewa da faɗin. “ALLAH ya baki haƙuri tashi muje ki kwanta”. Yay maganar Yana miƙar da ita. Koda ya kwantar da ita a saman gadon shima sai ya kwanta a gefenta tare da ɗan ranƙwafowa yay mata runfa da jikinsa. Hannu yasa yana share hawayen da take zirarwa har yanzun. “Bana son kukan nan Muhibbat, kinga yana ƙara miki zazzaɓi da ciwon kai, yaya Isma’il yayi laifi. amma a yafe masa shalelen Yaya Ammar….”
Cikin dasashshiyar muryarta ta katsesa da faɗin, “ALLAH ya kiyaye, kai ba Yaya Isma’il bane. Gara ma ka daina wannan ɓoye-ɓoyen fuskar da yaudarar mutane kana jefa rayuwarsu a haɗari kai kazo ka kwana lafiya”.
Murmushi kawai yayi batare da ya amsata ba da sumbatar laɓɓanta ya rungumeta a jikinsa dan kansa ciwo yake masa. Tun tana jan ajiyar zuciyar kukan da take har barci ɓarawo ya saceta. Shima dai barcin ke son ɗibarsa saboda maganin da yasha. Cikin ƙanƙanin lokaci duk suka tafi duniyar barcin.
Barci sukai sosai har magrib ma ta ɗan gota. kiran wayarsa da akai ne ya farkar da shi harda ma Hibbah, sai dai ita tayi luf bata nuna ta tashin ba harya janyeta a jikinsa ya ɗauka wayar. “Barka da yamma sir”.
Ya faɗa cikin muryar barci lokacin da yake kai wayar saman kunnensa. Jin abinda wanda ya kira sir ɗin ya faɗa da ga can ya sashi miƙewa da sauri yana kallon agogon ɗakin. Kansa ya ɗan dafe ganin yanda lokacin yaja sosai harma anyi magrib. “I’m sorry sir kaina ke ciwo na ɗan kwanta ne bansan lokaci yaja ba haka”.
Amsar da aka sake bashi da ga can ta ɗan sakashi sakin ɓoyayyen murmushi da faɗin, “No sir insha ALLAH yanzun nan zan iso ɗin ka jirani, dan ina son baka gaba ɗaya bayanan kawai kafin na ida tattara sauran gobe idan ALLAH ya kaimu.”
Idanu Hibbah da maganganun nasa suka bama mamaki ta ɗan buɗe tana kallonsa. Gabanta ya sake faɗuwa dan still dai Yaya Isma’il take gani har yanzu, kamar yanda a murya ma dai ɗin shine. Duk da ta jima tana wasiwasi akan muryar master idan yayi magana dama batun yanzu ba. Sai dai tsakanin ɗazu zuwa yanzun muryar tasa tafi kamanceceniya data Yaya Isma’il ɗin fiye da ko yaushe. Ganin ya juyo ya dubeta bayan ya katse wayarne ya sata saurin maida idanunta ta lumshe zuciyarta na azabar bugu da sake shiga a ruɗani. Ya fahimci ta tashi. dan haka ya miƙe batare da yay magana ba ya shiga toilet a ɗan hanzarce.