Uncategorized

YAU DA GOBE 15-16

   Idan bazaki tsaya muyi mgn ta fahimtaba…you can go! yafad’a murya akausashe…tabe baki tayi had’e da Jan kujera ta zauna tana cika tana batsewa…. laptop yajawo yana latsawa kafin yace byn dawowata dg UK me nace Miki?”bata fuska tayi had’e da cewa amma dace nashirya aurenka bana ce makaba daddy yace sai na Ida service nanda 6 month”Kuma kace to”uhummm naface to!amma ke sbd wa kika ki yarda muyi aure alokacin?”sbd daddy Mana”

Batare daya kalletaba yace ok!to nima sbd abbana k’anin mahaifina”zanyi wannan auren… yafad’a irin ko ajikinsa d’in nan”

Cikin fushi tace oh haka ma zakace?”

Kallonta yyi ido cikin ido kafin yace waye yaja faruwar hakan cikin mu?”

    nidai sweet heart ba wannan ba”miye mafita ko kuwa kanason auren?”

Kinsan bansan surutu da Jan mgn ko?”bacin ke dama Ina kula wata?”

Hakane nima nasani saidai in cusa maka ita akayi”amma gsky ka zab’a koni ko ita sbd bazan iya sharing d’inka ba… murmushi yasaki saidai kiyi hakuri kawai in Kinga anfasa auren nan saidai ko nina mutu ko yarinyar…kibarshi bayan wasu watan ni sai muyi aurenmu “hakan yyimiki?”nibemunba”haba sweet heart!yakake so nayi da Raina ne?”wlh bazai yuyuba ko wacece haduwarmu da ita bazaiyi kyauba”bata isa shigarmun gona ba”kafi kowa sanin yadda nike sonka… tafad’a kuka nacin k’arfin ta…wani tausayi yaji tabashi”ahankali yace sorry kinji?”Kinga bazan iya bijirewa abba naba”kace kika ja komai da yanzun munyi aurenmu”nikaina bakisan yadda nadamu bane”itama yarinyar tanada Wanda takeso kawai matsala aka Samu…cikin kuka tace gsky ni wannan matsalar batamun adalciba”amma insha Allah byn auren zanyi yadda muka rabu…ajiyar zuciya rukky tasaki…yazaro handcheep Yana share Mata hawayenta had’e da rarrashinta cikin taushin murya…ai tuni rukky tasaki jikinta suna fira harda murmushi”da kanshi yyi dropping d’inta zuwa gd”saidai ta cewa driver d’in ta yatafi…



   ************

Abba ne zaune kan kujera”parlourn  agdn su Dr safana”yyinda Dr safana ke zaune kan carpet”Abba yace banason natakuraka shiyasa nazo da kaina”dama   akan yarinyar nan ne my son har yanxun batasan Kaine zata auraba”shine nikeso yau nasanar Mata ko zuwa gobe tunda jumaa sai kaje ku gaisa kaji me yakamata kuyi na biki tunda gashi cikin wata3 har anci sati3… sannan inaso kamun alfarma guda d’aya karka nunawa duniya cewa bakasan sumayya Dan Allah….shirun da Abba yyi yasaka Dr safana cewa to Abba atakaice”azuciyar sa Yana mamakin Wai bata ma saniba “saishi ne aka Fara gaya mawa kenan”wani haushinta yasake jiki ya nunku aransa”Abba ya Mike Yana gyara malun malun d’insa yakalli hjy Aysha dake saukowa dg up stairs yace nina wuce hjy….kafin ummi tayi mgn zarah ta shigo “da sauri ta duk’a ta gaida Abba “ya amsa Yana cewa to Yaya service d’in?”tace alhmdllh!yace to kima shirya dakin kammala sai aure naga yamiki… murmushi kawai tayi tana b’oye fuska…nan sukayi sallama d ummi yafice”zarah ta shagwabe fuska had’e da cewa wlh ummi nagaji ga yunwa”ummi tace yocan makarantar bakici abinciba?”haba ummi wane cin abinci kana fama da koyawa yara wannan yyi nan wannan yyi nan”Kai gsky teachers na k’ok’ari wlh…ummi tace sannunki !kije kitchen ki dafa indomie banyi girkiba kinsan na fita”yanzun laraba tazo muka aza…zarah kuwa musty yafad’o Mata arai”tasan inda adane time d’in dasuke d’asawa dashi wlh duk abinda takeso zai siya Mata”amma gashi benan…Yaya Aliyu ta kalla ganin tamkar bbushi a parlourn tace Yaya pls zanci suya wlh yunwa nakeji… mik’ewa tsaye yyi fuska agimtse yaja gajeran tsaki had’e da ficewa dg parlourn…

Ummi tace kekuma me yakaiki Masa mgn?”turo Baki zarah tayi had’e da cewa wlh ummi cikin kwanikan nan narasa me nayiwa Yaya baya kulawa Dani”sai harara ko tsaki komai kamasa laifine…ki Masa uxuri kinsan ban fad’a mukuba dg ke har auta abbanku zai had’a sa aure da sumayya y’ar amaryar sa”shine yaketa jin haushi da b’acin Rai…zarah tayi ihun murna had’e da cewa wayyo ummi wlh naji dad’i,dama ni bani wanison ya auri rukin nan wlh..ni batamunba…yo ai yace zai aureta itama dg baya.cewar ummi tana Zama”zarah tace tofa!wlh ni sainaga yamafi dacewa da sumayyar tanada kirki da hankali ga sakin fuska agaisa da mutane…ummi tace hakane gsky sai kuyita Masa adduar Allah yasa yasota tunda Yana nuna baya sonta”

Tab’e baki tayi had’e da cewa ai Yaya sai ahankali Insha Allah YAU DA GOBE wata Rana zai sota”ummi tace Allah yasa!zarah tace ameen tana wucewa kitchen….



Da sallama sumayya ta shigo parlourn abba “sbd kiranta da mamanta tace yanayi yanzun”bayan ta Mata gargadin duk umarnin daya bata tabi indai besa b’awa shari’a ba…hakan yasa Sumayyar jin faduwar gaba….jikinta asanyaye ta gaishe da abban kafin ta zauna kan carpet..”ahankali Abba yace sumayya!inaso kibani aron hankalinki kiji abinda Zan fad’a Miki yanzun  insha Allah “inaso kiyiwa maganar kyakykyawar fahimta!cikin faduwar gaba sumayya tace insha Allah abbah….

Yace madallah! sumayya inaso kisani nasaka ranar aurenki sati 3 dasuka wuce da Aliyu”nan da wata 3…nasan kinsanshi tunda kinje asibiti yadubaki.. yayansu Sadiq d’an Yayana marigayi……????????????????‍♀️????‍♀️????‍♀️




Share

By mmn fareesa ????️

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button