YAU DA GOBE 19-20

Tun d’azun Ina jinku abakin k’ofa”inda banzoba dukanta zakuyi kenan?”
Kicin kicin da fuska jidda tayi tana gunguni k’asa k’asa…anty zainab tace kiyi yadda zanji Mana marar kunyar banza da wofi..ai wlh Koda Aliyu yace ke yakeso bazan bada goyan bayan ki aureshiba! sbd baki dace dashiba”kaf halin mahaifiyarku bbu abinda kika bari… Sadiq ne na k’warai a y’ayan hjy jamilah.gsky adena zagar Mana uwa!cewar safeenah tana turo Baki…anty zainab tace zaku fice kubawa mutane guri ko kuwa?”amma kusani dg yau ko ance kusake zuwa part d’in nan kuyi rashin kunya baza kujeba”kaf saina zayyane wa Yaya abinda yafaru…jidda da safeenah suka zaro ido sbd sun San halin abbansu..ji sukayi tamkar subata hakuri “amma girman kai yahana , musammun tunda agaban sumayya ne.. k’ofar suka nufa zasu fice”anty zainab tace sai kuyiwa uwarku albishir “Maryam d’in dabakwaso tahaifi y’an 2 duka maza…duka maza??”jidda da safeenah suka furta atare”suna ficewa..tsaki anty zainab tayi had’e da kallon sumayya dake tsaye tana sauraronsu ,tace muje ciki sumayya dg asibiti nike. nazo daukarwa mamanki kayane dazata canza… murmushi sumayya tayi had’e da cewa to anty Ina wuni?”lfy lau sumayya kiyi hakuri kinji”insha Allah kece da riba ki barsu da halinsu”YAU DA GOBE zatayi aiki akansu indai rayuwace…. y’ar dariya sumayya tayi had’e da cewa lahh bbu komai anty!kafin su shige bed room d’in mama…
Zaune suke a parlourn gdn”mama ce sai anty zainab (kasancewar ana zata zauna har ayi suna sbd tarabu da mijinta sbd bata haihuwa)sai sumayya dake zaune kan carpet tana rik’e da baby guda”yyinda gudan ke hannun anty zainab….hjy jamilah bbu ko sallama ta shigo afusace”sai huci take. tana cewa zainab ! zainab!!Ina kike juya? murmushi anty zainab tayi.sbd dama tasan muddin sai hjy jamilah tazo sbd tasanar wa Abba abinda su jidda sukayi…yakuma hukuntasu .kallon ta tayi had’e da cewa gani ! Mai abun haihuwa ‘to dukda Ina juyar na godewa Allah daya bani ilimi da hankali….ke dakata !rashin kunya zakimun sbd kema anbaki kinsha ?akan agola zakiyiwa y’ayan d’an uwanki sharri “ki had’a d’a da ubah ko?” Sbd ke bakisan zafin haihuwa bako?” To Bari kiji ni warkice daidai k’ugun kowa”bacin kungama kilbibinku na rakata labour room”shine saikin debo jiki kinzo sbd kima yarana sharri”yo Allah natuba saime?”ai bakan wannan alh yafara haihuwa ba”ke Kuma algunguma keda y’arki dani kuke zance” inhar tacika y’ar halak dg yau tadena Zama agdn nanzakusan kunshiga gonata…hjy jamilah ta fad’a tana yiwa k mama mugun kallo! murmushi mama tayi had’e da cewa ni bana fad’a! fad’a sai jahili sbd haka damuwarkice “Ina cikin farin cikin kyautar da Allah yamun…mitss taja tsaki had’e da cewa oh nikike cewa jahila kenan?”shiru sukayi suka k’yaleta harta Gama tujarar ta ta fice…anty zainab tace Allah yakyauta…
????????????????????????
Ahakafa akayita karban barka har ranar suna yazagayo”yara sukaci suna UMAR da DA USMAN (wato sunan mahaifin Dr safana da sunan Abba)ana kiransu da muzaffar da mu’annas…hjy jamilah kuwa zahiri take nuna b’akin cikinta afili”duk wata hidama da akayi bbu ita bbu y’ayanta basu shiga.anty zainab kuwa washe garin suna Takoma gdn hajjah”ummi kuwa tsakaninta da hjy jamilah sai harara”musammun sbd taga harda ummi aka Kai mama asibiti ta haihu..ummi kuwa Bata damuba ,sbd halin hjy jamilah ba bak’onta bane..
Gefe guda Kuma bikin Dr safana da musayya sai k’ara matsowa yakeyi”ayanzun haka saura 3 week bikin…har angama Gina inda zasu zauna… sannan tun zuwan farko da Dr safana yyi besake zuwa Gurin sumayya ba”Dr Nasir yaso suzo sbd suji ko akwai event d’in da za’ayi”amma Dr safana yace baza’ayi bidi ar komai ba.sai inzai auri rukky”wato auren SO…amma dukda haka Dr Nasir yace shizaije yaga Sumayyar da k’awayen ta…itama sumayyar anata b’angaren bata buk’atar ayi wani event”saidai Koda anty zainab taji”cewa tayi dole ayi….
WA’AZI , MOTHER’S EVENT DA KAMU…Kuma dole Dr safana yaje kamu da kanta zata sakashi yazo…itadai sumayya jin anty zainab kawai takeyi batace komaiba”sbd aganinta ai saiyazo sannan yaji dame dame za’a yi”tasan kuwa ba zuwa zeyi gunta”shiyasa Koda Samira tayi Mata magana akan ina Invitation card?”biki saura3 weeks”yaushe har zasuyi inviting din friends d’insu?ai yanzun yakamata biki saura 3 weeks sufara gayya..itadai sumayya shiru kawai tayi”sbd ada ganin abun takeyi kamar wasa”Amma ganin anfara shirye shiryen biki yasakata gasgata abun,dakuma kayan Mata da aketa bata dana gyaran jiki…dukda batason Sha saidai bbu yadda ta iya..
********
Ayau yakama lahadi”biki yarage saura 20 days akuma yau ake kawo lafen sumayya…gaba d’aya shirye shiryen tarban bak’i akeyi”anty zainab da Inna mariya (matar baba Iliya)sai hjy bintu(k’awar mamace anan makwab tansu take) sune keta hidimar abinda za’a tarbi bak’i dashi…yyinda mama ke gefe da twin’s dinta sbd tana Kara da alkunya na d’an fari”saidai kallonsu take tana zaune…hjy jamilah kuwa tunda taji yau ake kawo “tasaka ido tana jiran 4pm tayi suga kayan lefen…dukda zuciyar ta acunkushe take akan abinda Abba yamata na cewa sai ana gobe daurin auren sumayya Sadiq zaizo…bacin tunda yatafi kusan 2 month kenan. saidai suyi waya amma be zo gidaba..sai Abba yanuna mata cewe sbd Aliyu zaizo badan Sumayyar datake k’i ba….
Ummice zaune da zarah da wasu k’awayen ummi sunata duba kayan lefen…wayar ummi tayi ringing… d’agawa tayi tana murmushi had’e da cewa autana kayi wuyar gani!sai yaushe zakazo bikin?”wlh bansaniba ko d’azun zarah tamasa mgn da safe akan me da me za’a yi?”yamata banza..to shikenan…ta fad’a tana yanke wayar”zarah ta tabe baki had’e tashi sbd tayi wanka tunda da ita za’a tafi..ummi ta dubeta had’e da cewa auta yace sai saura kwana3 biki zaizo”Allah yakaimu kawai zarah tace tayi tafiyarta..
Da misalin karfe4:30 pm”bakajin komai sai tashin bud’a a part d’in mama sbd kayan lefen sumayya tuni sun iso”Yan uwansu na Kano da mak’ota da abokan arziki had’e da dangin Abba sunata ganin lefen sumayya akwatina12 da sark’an gold da zobenta….Masha ALLAH! abin sai Wanda yagani komai yaji akwai manyan suturu na alfarma…hjy jamilah tagama gani da k’yar ta daure wa zuciyarta ta nufi part d’in ta…tana shiga tasami yayarta saratu…byn sun gaisa ta dubeta had’e da cewa Ashe y’ar kishiyarki alh zaiyiwa aure?”tab’e baki hjy jamilah tayi had’e da cewa aikuwa abinda yasa bana murna d bikin shiyasa wani nawa be saniba…Yaya saratu tace Wai jamilah har yanzun bakisan annabi yayi wafati yabar duniya?”kiyita abubuwa”yanzun ace ga jidda nan ta kammala NCE d’in ta Amma batayi aureba”badon komaiba sbd duk Wanda zaice Yan sonta saikin kawo wata makusa akansa “kin nuna akwai wani nakasu atare dashi…kwanaki har gdnsu yarinyar nan khadija (first love d’in Sadiq)kika ci Mata mutunci itada iyayen ta akan tarabu da sadi…sbd ke yanzun abin jindadine agunki ace ga y’ayanki ba’a aurar dasuba sai agola?”Kinga Yaya saratu Dan ALLAH kirabu dani naji da abinda ke damuna Dan ALLAH…tashi tsaye Yaya saratu tayi had’e da cewa bbu komai”inkinada rabo kya gane wata Rana”nizan wuce gd”amma sainaje naga lefen na musu Allah yasa alkhairi…tabe Baki hjy jamilah tayi… yyinda Yaya saratu ta fice…