YAU DA GOBE 25&26

????YAU DA GOBE ????
????????????????????????????????????????
Story & writing by mmn fareesa
????️25&26
“””Da kayan daya gama dinner,tayi cin karo dasu aparlourn”cike da mamaki take duba komai”sbd ganin yacinye wayam “Baki ta tab’e had’e da cewa”inhar beyi dad’i ba ai sai mutum yabarmun abuna”ko hasidin iza hassada yaci wannan girkin dole ya yaba.tafad’a tana kwashe kayan takai kitchen…kafin ta nufi bedroom d’in sa”da sallama ta shiga ,yana kwance kan bed yyi matashi da
hannayensa idanunsa a lumshe.kallo d’aya tamasa ta d’auke kanta had’e da shigewa bathroom…byn tafito” yadubeta fuska ayatsine yace zanje office gobe ki tabbata before 9:pm kin gama had’a mun breakfast!amma kiyi wanka kafin kishiga kitchen d’in”banason katsanta”maleji kawai nakeyi kafin my rukky ta shigo gdn nan”Allah ko?bansaniba! murmushi ya subucewa sumayya”ta dubesa ashek’e had’e da cewa ai ko yanzun bata b’aciba ka kirata tazo goben saita had’a maka break fast din kawai… Keeeee! yafad’a atsawace”karki koma yadda Ina mgn kinayi koki mayarmun da murtani”shashasha marar kunya”inbacin dole kin Isa na aureki… shiyasa ko office ban d’auki hutuba sbd “auren da akamun ban d’aukeshi auren jin dad’i da farinciki ba… sumayya kuwa har yakai aya idanunta na kallon saman silin d’in d’akin….get out of my room…batare data tankaba ta fice zuciyar ta na suya…
*Washe gari*
Tana idar da Sallar asuba” ta gyara waiting parlour da bed room d’in ta”kafin ta nufi bedroom d’in Dr safana… murd’a k’ofar tayi sbd taje ta gyara d’akin”Yana kwance kan bed yarufa da blanket…tunda take dashi bata tab’a Zama tayi mishi kallon tsabba sai yau…bbu abinda yafi burgeta afuskarsa illah k’atuwar sallayarsa dake tsakkiyar goshinsa dakuma sajensa… tab’e baki tayi sbd tunawa datayi ita basonsa takeyi ba… toilet taje ta wanke ta had’a mishi ruwan wanka” kafin ta fito”steel Yana bacci, agogon dake jikin bango ta duba taga7:30am.
Jitake kamar tarabu dashi inma yyi lattin zuwa office d’in shiya sani”to amma sbd tanaso ta gyara d’akin yasa “ahankali ta Kai hannunta gefen pillow d’in”tana bubbugawa”tayi hakan kusan sau3 kafin yabude idanunsa dake jajir k’yam akanta…wani kwarjini taji yamata”da sauri ta janye hannunta”jiki na kirma tace katashi kayi wanka Zan gyara d’akin”tsaki yaja had’e da cewa ban fad’a Miki ba banason katsalandan da shishshigi”?”Ina ruwankine?”
Girgiza Kai kawai tayi had’e da cewa laifina ne”insha Allah kozaka kwana kana bacci bazan koma tayar dakai….tsit tayi sbd ganin yatashi azafafe”da sauri tayi baya jikinta na kirma zata fice…kidawo kiyi aikinki pernishment d’inki saina dawo sbd jiya namiki warning kan Ina fad’a kina fad’a ko?”sumayya batace komaiba kanta na k’asa”yajawo towel cikin Ward rope ya wuce toilet”itakuma tacigaba da aikinta agaggauce…tana idarwa ta nufi kitchen…cikin minti35 gdn gaba d’aya yakacame da k’amshin girkin ta….Dr safana kuwa dama beyi Sallar asuba ba”sbd beyi bacci da wuriba”akan matsalar feeling d’in dayakeji tun shekaran jiya da dare.. byn yyi sallar,yaduba bata fito Masa da kayaba…tsaki yaja had’e da fitowa,dg shi sqi jallabiya ajikinsa….Yana isowa waiting parlourn gdn k’amshin yadaki hancinsa”ficewa yyi Yana tab’e baki sbd kwata kwata yarinyar bata burgesa..part d’in su ummi Ya nufa”aparlour yasami ummi da musty suna sallama zai koma KD…Zama yyi suka gaisa da ummi”kafin musty yagaisheshi”zarah dake kitchen ta fito “byn sun gaisa tace Yaya Ina anty sumayya?”wlh kayi dacen Mata duk dangi casukeyi tanada kirki wlh ga kyau…kallon da Dr safana yyi wa zarah yasakata yin shiru…murya akausashe yace kinsan bansan fad’i ba’a tambayeka ba ko?”get out”cike da mamaki zarah da musty ke sauraronsa”ummi kuwa kanzil bata ce mishiba”zarah kitchen ta koma”musty yabita sbd yabata hakuri suyi sallama…”ummi ta juyo ta dubesa rai b’ace kafin tace ,dama Ashe bazaka canzaba?”bazaka iya rik’e amanar marainiyar Allah ba?”dukdan kawai anfad’a maka danginka na yabon matarka kake haka?”to bari kaji wlh kabi ahankali YAU DA GOBE ta wuce wasa”inhar kabari yarinyar nan tabar hannunka wlh bazaka tab’a samun kamarta ba….da sauri yakalli ummi”sbd mamakin firucinta”ahankali yace kiyi hakuri ummi”amma tunda namuku biyayya nima ai sai abarni na auri zab’ina… murmushi ummi tayi had’e da cewa ai namiji mijin mace4 Allah yabaka ikon auro ita taka zab’in…amma kazanca hali kaji naga yamaka”shiru kawai yyi Yana tashi yafice…
Zarah kuwa abin yabata tsoro da haushi..wani tausayin sumayya taji yakamata” tabbas auren Wanda baya sonka matsala ce babba…haba my sweet baby! Kinsan halin Yaya inyau dokin zuciya?” Musty yafad’a Yana kallonta” janye idanunta tayi had’e da cewa bazakayi break fast ba”? zanyi a hanya g driver can Yana jirana”ok Allah yatsare! Iya abinda Zan samu kenan?yanzunfa Inna tafi zanyi kusan3 month kafin nadawo”nasani ai ko” gsky baby kina bani wahala”yakamata ki Dena pritending ki amince kawai…Wai broth saunawa zance maka mudena maganar nan ne Wai?”
Haushi sosai musty yaji akan wannan abun data ke Masa..kanzil bece mataba yafice dg kitchen d’in..zarah sqikuma taga kamar bata kyauta ba. akan abinda ta mishi”sharewa kawai tayi tacigaba da aikinta..
Dr safana Yana fita part nasu yakoma yasami sumayya “najera warmers a dining table”had’e Rai yyi”kafin yace”kije ki fitomun da kayan dazan saka!nafito dasu ai”bayan natuna cewar ban fito maka dasuba..bece komai ba yawuce d’akin sa..itama nara d’akin ta wuce sbd ta shirya”sbd tanaso taje ta gaido ummi “
Ahankali yake tafiya zuwa dining area”sanye yake da suit farare da takalmi sawu ciki sai lapcoat dake saman kayan sai briefcase dinsa dake rataye ahannunsa….kujera yaja ya zauna ya bud’e cup yaga ta had’a mishi tea”sai cheeps da farfesun kaji”ga bread da yaji butter…yyi Bismillah yafara break fast hankali kwance…anutse take tafiya”k’amshin turaren ta,ya ankarar dashi zuwanta”girar sama data k’asa yahad’e”sanye take da doguwar riga ta lace light blue..fuskarta tayi Shar bbu make up..da hijab iatama light blue iya gwiwa ajikinta…ahankali ta aza hannunta kan d’aya dg cikin kujerun table d’in murya a nutse tace Ina kwana?”cup din dake hannunsa ya ajiye “kafin yace dama haka aka Baki tarbiyyar gaida babba?”and last meye abin kizo ki tsaya mun aka?”kayi hakuri dama inaso zanje nagaida ummine….katseta yyi da cewa Ina ruwana ni?”damuwarkice kiyi yadda kikeso”inkuma kika shiga gonata ki gane kuranki”dama Abba yace monday Zaki koma skul ba”na rik’a ajiyeki kafin na wuce office”bazan iya hakanba’ innayi k’ok’ari nabaki kud’in transport…jin yakai aya yasakata juyawa tabar mishi parlourn gaba d’aya… dak’in ta ta koma ta fad’a kan bed tasaki kukan bak’in ciki..gwanin ban tausayi….Saida tayi Mai isarta tukum ta fito tayi break fast…. yyinda Dr safana ya wuce office abinsa batare dayasan halin datake cikiba…
****************
Ummi na kwance kan doguwar kujera”kasancewar zarah ta tafi skul d’in datake d’auka”cikin nutsuwa sumayya tayi sallama cikin sanyayyar muryar ta”ummi ta amsa cike da fara’a”tana Mata sannu da zuwa…cike da kunya sumayya ta duk’a har k’asa ta gaida ummi kafin ta zauna kan carpet!ummi tace ah ah sumayya koma kan kujera Mana”sumayya tace ah ah ummi nan ma yyi..kafin tace Ina anty zarah?”murmushi ummi tayi tace tana skul “shiru yad’an ratsa tsakani”kafin ummi tace ince dai bbu wata matsala daiko?”nasan halin babana inyamiki wani abu kisanarmun kinji karki b’oyan sumayya… kanta aduk’e tace bbu komai ummi Muna lfy…shiru kawai ummi tayi sbd tasan ba haka bane”aranta tace Allah sarki! Allah yabashi matar rufin asiri…ummi Zan koma dama cewa nayi bara nazo nagaidake “amma anjima Zan dawo in anty zarah ta dawo?” Ummi tace to shikenan nagode k’warai sumayya Allah yyimiki albarka”kiyita hakuri kinji”zaman aure d’an hakuri ne…da haka sukayi sallama sbd Sumayyar nason komawa ta aza girkin Rana…