YAU DA GOBE 29&30

????️29&30
Wannan shafin nakine kyauta ummu sultan????????????
…..suna fitowa wayarsa tayi ringing”ta katse wani Kiran yasake shigowa.ajiyeta yyi fuska ahad’e yace Allah yasa kikoma yunk’urin guduwa kigani!wayar yaciro dg aljihun wondonsa.sake bin Kiran yyi sbd ta tsink’e… subahanallahi!; to shikenan gani nan zuwa insha Allah… yafad’a Yana kashe
wayar”kafin yamayar da ita aljihu.yaciro key d’in d’akinsa ya dubi sumayya dake zaman dole kan kujera ya wurga Mata shi”Yana cewa ki gyaran komai very neat”kimun lunch”kinji ko bakijiba?”shiru kawai tayi tana share hawayenta…yaja tsaki yafice da sauri..
Duk abinda yadace Saida tayi komai. tamkar yadda takeyi abaya”
Saidai zuciyar ta acunkushe take”tana tunanin minene makomar aurensu ?”
Duk inta tuna yarabata da martabarvta saitaji tamkar ta had’iyi zuciya ta mutu sbd haushi da takaici… musammun inta tuna da yawan matan dake samun kulawa agun mazajensu adaren farkonsu”amma ita nata Daren farkon ga yadda yazo Mata..
Saida ta idar da girkin ta jere komai a dining table”ta wuce tayi wanka”bayan ta shirya tadanci abinci sama sama”kafin tasaka hijab da nik’eb ta Kira driver awaya, cewar ta shirya yafito da mota gatanan zuwa..
Basu gama loctures ba sai 6:pm”lokacin data iso gd”gab da magrib…yanayin yadda taga parlourn yasa tagane me gdn yadawo..bed room d’in ta kawai ta wuce tayi Sallah”kafin ta fito zuwa kitchen had’a dinner..
Koda ta idar ta kwashe kayan d’azun ta jera na yanzun..hakan yyi daidai da shigowar sa parlourn” ko inda yake bata kallaba.tqna idarwa tayi wucewarta d’aki…gogan kuwa tab’e baki yyi”ya iso dining area d’in….
Washe gari cikin farin ciki ta farka sbd yau zataje taga mama da twin’s datakejin byn mama bbu Wanda takeso sama dasu aduniya….bayan ta Gama had’a musu breakfast ta shirya”sanye take da doguwar rigar lace yellow.tayi kyau Masha Allah”kallo d’aya zaka mata kagane tana cikin farin ciki”Yana zaune Yana break fast hankalinsa kwance.”kujera taja ta zauna”had’e da cewa Ina kwana?”batare daya kalletaba yace kirik’e abarki”yaushe rabon da kigaidani?”cike da mamaki take sauraren sa”tunda tazo gidan wata2 kenan Bata tab’a gaidashi ya amsaba amma Kuma har zaice haka?”
dama in angaidakai kana amsane?”
Bansaniba! shiru kawai tayi tana had’a tea”ganin Yana k’ok’arin tashi tace maganar tafiyar na shirya… ashek’e yakalleta”sbd ganin yanzun dududu befi karfe 9 nasafeba”na lura kwana 2 nan kanki na rawa zan saita mikishi”kokuwa sbd abinda yafaru kike hakan? Toni sai5pm natsara tafiyar…nikuma yanzun na shirya”Dan kayi hakuri naje driver yakaini”da karfe 5din sai kaje…hakan be munba”kina nufin wazai Miki garki da gyaran d’aki na…batace komaiba har yagama yyi tafiyarsa d’akin sa”bayan ta idar da breakfast ta gyara Gurin”da bed room d’in ta ,ta wuce d’akin sa”sbd ganin yafita,ta binciko keys d’inta daya karb’e…takuma Sha alwashin bazata yi girkinba dagyara d’akin saidai yakasheta…chat taitayi”sai bayan taji yunwa Tasha comflax da Madara tayi Sallar azahar ta d’auki Jakarta ta wuce part d’insu ummi sbd yadda ta tsara dg can su wuce gdn mamanta…
Da sallama ta shigo cike da nutsuwa”zarah dake tsakkiyar parlourn azaune ga plate na d’an wake agabanta yaji kayan had’i”ta amsa fuska cike da fara’a”Zama sumayya tayi suka gaisa”kafin tace ummi fa?”yanzun ta shiga wanka “muci abinci anty sumayya… murmushi sumayya tayi had’e da cewa ah ah nako…ai wlh baki isaba!saikin cisa Kona Dena zuwa part d’inki”zarah tayi saurin katse Sumayyar.
Matsawa tayi sbd itama tanason Dan wake mutuminbtane”sunaci suna korawa da siro..gab dazasu cinye sumayya ta zare hannunta tace nagode anty zarah nak’oshi…hakan yayi daidai da isowar ummi cikin parlourn”zarah tace hmmm gsky yakamata kisaki jikinki nanfa gdnkune!ummi data zauna tace ‘yata sannunki da zuwa !kwana 2 kindena lek’owa mu gaisa”sumayya na murmushi tace aikuwa lfylau ummi Muna jarabawa ne shiyasa”Allah sarki Allah yataimaka!cewar ummin…bayan sun gaisa ” ummi tace yaune zakuje gdn Abbanku ko?” Tace eh “mma sai karfe5″ ummi tace ainazata yini zakiyi acan?” Sumayya dai tana murmushi batace komaiba..
Ummi kuwa ta fahimci tabbas Aliyu ne yace sai karfe5″.girgixa Kai kawai tayi tana tunanin sai yaushe Aliyu zai canza?
Sundade suna fira abinsu…dg baya zarah ta kunna kallo kasancewar week end kowa Yana gd…wata k’atuwar mage aka hasko atallar wani firm dasuke kallo sumayya ta rintse idanunta had’e da Wai Allah!zarah tayi dariya had’e da cewa tsoronta kikejine?”
Sumayya tace aini Kinga “mage k’adangare,tsaka Ina mugun tsoronsu wlh…musam… maganar ta mak’ale mata sbd hancinta daya shak’i k’amshin turaren Dr safana!
Maida k’ofar parlourn yyi ya rufe”kafin yyi sallama can cikin mak’oshi!kallo d’aya zaka masa kasan ransa ab’ace yake…sbd dawowarsa kenan dg asibiti!sbd ammishi Kiran gaggawa”yakwaso yunwa da gajiya yazo yasamu dining wayam”gashi bata nan “azatonsa ko gdn abban ta tafi”wata zuciyar tace Masa ko tana part d’in su ummi?”hakan yasa yanufo nan.
Satar kallon sa sumayya tayi aikuwa suka had’a ido yamata wani mugun kallo daya saka hanjin cikinta juyawa…saidai duk ummi na ankare dasu…zarah tace Yaya wani waje kaje bacin yau week end?”banza yyi Mata yadubi sumayya fuskarsa amatukar daure yace ke tashi kiwuce ki koma can…cike da tsoro sumayya jikinta ke rawa sbd tasan yabata umarni batayiba”damma sauk’i ta d’auke keys d’inta”koba kyajine?”yafad’a ad’an tsawace…tashi tsaye tayi! sumayya koma ki zauna! Cewar ummi fuskarta a’daure tana kallonshi”Dr safana sosa Kai yyi” sbd idonsa ya rufe ya manta da ummi na nan” ahankali yace to Amma ummi saitazo nan tayi zaune ga gidanta ! Intayi bak’i fa?”inbakin sunzo sai akirata anan taje ko?”ince ba yau kace zakuje gdn Abbanku ba?”eh ummi yaune.to saikabari dg nan kuje can d’in”in kundawo Takoma sashenkun… shikenan mutum bazaiji kad’aici yamasa yawaba yad’an fito”yaushe rabonta da nan d’in ma saifa yau!nama lura inba makaranta ba Bata zuwa ko Ina..cewar ummin tana kallonsa”sbd ta lura sumayya na mugun jin tsoronsa”bece komai ba yafice.sumayya taja ajiyar zuciya”
Koda yafita abind azaici yanema”kafin yaje masjeed yyi sallar la’asar”kafin yadawo yyi wanka ya shirya cikin riga da wando na ash colour din shadda”da hula sai agogonsa na fata itama ash”sai k’amshi ketaji ajikinsa…yyi kyau naban mamaki ga haske da yyi ,sbd jin dad’i d hutu…afito sak a agonsa..lolx
Tsaki yaja sbd yatuna bayada da number inta”dasai yakirata kawai su wuce”dole ya koma sashen ummin”bbu kowa a parlourn”d’akin zarah ya nufa “acan yasame su itada zarah da alama Sallah sukayi”zarah nataje Mata gashinta tana cewa gsky anty sumayya kinfini gashi Masha Allah…kallo d’aya yamasu yad’auke Kai “Yana mamakin yawan gashinta”shi wlh jiya daya gani azatonsa attachment ne tasaka”bece komai ba yajuya”hakan yasa zarah tayi murmushi had’e da cewa antynmu daura d’an kwali ga sweet heart d’inki najiranki”nasan Yayana da aji”Kinga bazaiyi mgn ba”Dan ALLAH kicanza manashi… murmushi kawai sumayya tayi batace komaiba…ta d’aura dan kwalinta”ta gyara gyalenta had’e da rataya jikkarta akafad’arta…Masha Allah”duk batayi k’iba ba”Amma tayi kyau ta k’ara haske da wayewa”Inka kalleta zaka d’auka budurwace…. Sumayya tadubi zarah tace pls muje kirakamu can d’in…zaro ido zarah tayi had’e da cewa rufan asiri karkijamun gun Yaya Dan ALLAH kije karkiyi laifi…da sauri sumayya ta fice”aparlour tasameshi suna mgn da ummi”da alama fad’a take mishi sbd tayi shiru dataga Sumayyar…cike da girmamawa Sumayyar tace ummi zamu tafi”to sumayya Allah yatsare kugaida mutanan gdn”tana murmushi tace zasuji da kyau…fita yyi..yabar Sumayyar suna mgn da ummi…kafin itama ta biyosa a parking space…Yana hakimce gdn baya”ga driver yashiga mazauninsa.