ZAIN ABEED 11

Page 11…
End of book1
*Gaba ɗaya Littafin sadaukarwa ce ga ADDA RAMLA MAI DAMBUN ZAMANI🥰😂 Allah yabar ƙauna*
Special Thanks to Real Smasher BILLYGALADANCI🥰🥰 Aysha Aliyu Garkuwa, My ƙungiya Elegant Online writers😍😍😍
Ɓata fuska Abeed yyi yana sanya hannunsa tare buge nata, data riƙe masa hannu, ƙasa tayi da kanta idanunta na ɗan cika da hawaye, ganin hakan da tayi ya sanya Abeed ƙara haɗe fuska sosai a ɗan kaushashe yace “Kee…” Shiru tayi taƙi ɗago kanta, tsawa ya daga mata tare da cewa “I’m i your mate?” jikinta na rawa ta kallesa ba tare da tace komai, idanun Sara ya cika da hawaye, ganin hawayen fuskarta yasa Calmy yace “Saaaa..” Sara ta ɗago idanunta ta kallesa kallo ɗaya tayiwa fuskarsa tayi kansa da kanta, Abeed yace “Zo nan Saaaaa” matsawa tayi wajansa domin no matter how scared of him ba zata iya barin wajan ba, shi take kallo a matsayin wanda ta sani kawai, ganin shoulder ɗin su na gogar na juna Abeed ya ɗan ja baya kaɗan yace “Zaki ci?” Gently ta ɗaga masa kanta alamar eh, yace “Ok eat” kasa taɓa komai tayi sai hannunta data miƙa wajan naman, kafin ta ɗauki naman ya buge hannuna yace “ke Mayya ce? Da sai Nana za kici?” Miƙewa tsaye kawai tayi tana ɗan surutai a Zuciyarta, juyawa tayi suka haɗa idanu Abeed, ya ware mata manyan idanunsa da mmkinsa sai yaga ta murguɗa masa baki, with so much surprised ya ware idanunsa, yun ƙurawa yyi kamar zai bita, ta fasa ihu tare da yin part ɗin Amma. Tattausan sajensa ya shafa yana sauke ajjiyar zuciya, felling so much better akan yadda yake ji jiya, fararen ƙafafuwan sa ya miƙe kafin ya ɗauki mug ya haɗa tea ya fara sha a hankali, kaɗan yaci abincin ya miƙe tsaye, walking slowly ya nufi part ɗin su, Sara dake laɓe tana kallon duk abinda yake yana barin wajan ta ƙarasa inda yabar Lunch ɗin ta fara cin naman kamar wani zai ƙwace mata. Abeed na shiga cikin bedroom ɗin su ya samu Zain zaune yana kallon movie, Abeed ya ɗan kallesa sai kuma ya ɗauke kai, ya nufi bathroom, wanka yyi ya fito ya shirya cikin ƙana nan kaya na shan iska, zuwa lokacin Zain ya koma Parlo kai tsaye shima parlon ya koma, Zain ya samu yana waya taɓe baki yyi jin Zain na cewa “Give me some times Du’a, i can’t marry serious idan ba tare mukai da Abeed ba, just relax” Diva dake zaune tana jin zuciyarta sam bbu dɗi tace “we’re all mature, na fara hqr gsky ace aure sai wani yyi zakai?” Idanunsa ya buɗe yace “hold on, wani fa kika ce? Idan akwai wani bai huce ke ba, Abeed ya fi ƙarfin ki kirasa da wani, i don’t force you to love me, dan haka zaki iya neman wani” yana faɗin hakan ya kashe wayar sa, yana jin wani irin haushin Du’a, duk wanda zai taɓa masa Abeed wlh ko waye zai iya karta masa rashin kirki, Abeed idanunsa akan Movien da Zain ke kallon na Sanam teri kasam yace “What noisess” Zain yace “for?” Abeed ya ɗan shafi kansa yace “Bata time ne kallo movie, kalli yarinyar ta mutu fa?” Zain yyi dry tace “And so what dan ta mutu? Have you watching frm the beginning?” Abeed yace “Nop, kawai hauka ne kallo Love movie” ya faɗa yana sauya channel zuwa ta ball, time ɗin ana buga ball Tsakani Madrid da Laliga, Zain yace “Ka gwada soyayya ko bbu yawa, zakai farin ciki koda farin cikin zai zama taƙi ne” Abeed ya gyara zama bayan ya buɗe fridge ya ɗauki chocolate da yawa yace “ba wata Soyayya da take dauwama, nifa da mace Gwamma Chocolate ina respect sunan mace ne kawai” Zain yace “Sure? Zakai bayani one day” Abeed ya lumshe fararan idanunsa yana jin zaƙin chocolate ɗin na ratsa masa ƙwaƙwalwarsa, yana matukar son chocolate, a hankali yace “Bayani, like? How?” Zain yace “Ohhu, lokacin da zaka fara ɗanɗana soyayya da ɗanɗana mace a time ɗin zaka san chocolate ba komai nace, U can live with chocolate, but u can’t live without woman” Abeed yace “wahala dai” ya faɗa yana ƙoƙarin saka wata chocolate ɗin abakinsa da sauri Zain ya kwace, Abeed ya buɗe ido sosai domin abin yazo masa unexpected, yana ɓata fuska yace “Malam zan maka rashin kirki bani” Zain yace “Dan Allah yaya kaji dana kwance chocolate ɗin?” Shiru Abeed yyi baice komai ba, ya jima da sanin Zain bashi da kunya, Zain yace “To duk sanda kasan mace, ba zaka so tayi nisa dkai ba ko na 1mnt ne, Abeg my friend take your time ka Gwada ko kissing na mace ne” tashi Abeed yyi ya zauna yace “God forbid, baki na ana wata” ya faɗa yana nuna bakinsa tare da ya motsa fuska, Zain yace “Eh, idan har kai lafiyayye ne” Komawa Abeed yyi ya kwanta, yana jan tsaki Zain yace “Ni yayyanka kake ma tsaki?” Abeed yace “Allah ya sauwaƙe,kowa ya san nina fara shaƙar iskar duniya” Zain yace “wlh ƙarya ne, kai daka maƙale a ciki” pillow Abeed ya ɗauka tare da cilla wa Zain yana kwaɓe fuska..Kiran sallar Magrib ya sanya suka miƙe a tare, Abeed ya ɗan riƙe cikinsa maganar da yyi duk ya sanya ciwon na masa zafi, a haka sukai Alwala Zain ya shige Masjid Abeed kuma ya zauna a ɗakin bai iya zuwa masjid. Wajan 9 na dare suka fito a tare sanye da ƙana nan kaya, wando 3gauther sai vest mai ɗan kama jiki, Abeed ne kawai ya sanya bandana a saman gashinsa, kai tsaye danning area suka nufa, a nan suka samu Amma da Abba, Zain ya jawa Abeed kujera ya zauna kusa da Abba, shi kuma Zain ya zauna kusa da Amma, Zain yace “Barka da sare our sweet parent’s” Amma tace “me kuke tun ɗazo kun zauna musun da kuka saba” Zain yyi Murmushi yace “A’a kallo muke” shi dai Abeed bai ce komai ba, sai can yace “Abba barka da dare” Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas yace “Ywwa sweetheart, ya jiki” yana ɗan kwantar da kansa a kafaɗa tare da kwaɓe fuska yace “Allhmd, Abba zani Australia” da sauri Amma ta kalli Abeed shima ya kalleta sai ba tace komai ba, Abba yace “meyesa?” Abeed yace “Kawai Abba” Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas yace “To ba zaka ba” a sanyaye Abeed yace “To Abba” Zain dai shiru yyi ya fara cin abincin shi kuma Abeed ya sunƙi da kansa, so yake yaje yaga wani babban likita acan Australia amma ba zai iya faɗa ba, idanunsa ya ɗaga cikin Sa’a kallonsa ya sauka akan Sara wacce take zuwa wajan, ganin babu wanda ya kula da ita ta miƙe da sauri tare da shan gabanta, sai a lokacin Amma tace “Abincin fa” Yana kare Sara wacce take sanye da wani crazy Jen’s ita gwiwa yace “I’m full” kallonsa Amma tayi amma bata hango abinda yake ɓoyewa ba, Abeed ya kalli Sara fuska babu fara’a yace “Muje” maƙale ka faɗa tayi tana murguɗa baki, idan yyi mgn yasan za’a jisa, sai kawai ya kama hannunta tare da shigewa part ɗin data fito, yana zuwa ya kulle ƙofa tare da tura ta da bedroom shi kuma ya jingina da jikin ƙofa, tun daga ƙasa ya fara ƙare mata kallo har zuwa sama, da sauri ya ɗauke idanunsa yace “Ke baki da hankali ko?” Kallonsa tayi ba tace komai ba, juyawa yyi tare da fita ya kulle ƙofar, bayansa tabi da kallo cikin Sanyin murya tace “Abin bauta kabas ka taimake ni” tana nan tsayen taji an buɗe ƙofar ware manyan idanunta tayi ganin ya shigo hannunsa riƙe da bulala, baya ta fara ja tana yarfe hannayenta idanunta ya cika da hawaye, duk inda tayi binta yake baya son raini a rayuwa yaga kuma kamar bata da kunya, har ta ƙarasa jikin bed yana binta, ganin zai kamata ya sanya ta sulale ta gefensa zata gudu yyu saurin kama hannunta, ƙara ta ƙwala, Abeed kam hannun ya riƙe ya dinga tsola mata bulalar tana ihu sai da yyi mata bulala goma, sannan ya zauna gefen bed ɗin tare da daka mata tsawa yace “Shiru, ko nai ball dake” ajjiyar zuciya ta dinga saukewa hannunta tuni yyi ja, sai a lokacin jikinsa yyi sanyi ganin ba wani lafiya gareta ba, ƙilan ma bata san me take masa ba, gently cike da tausayi ya jawota tare da zaunar da ita saman cinyarsa yace “Shiru” kanta ta ɗura a ƙirjinsa tare da cewa “Twin” idanunsa a rufe yace “Saaaaa” ya faɗa yana hura mata iska a hannun wanda yyi jaa sosai, shiru tayi jikinta har lokacin rawa yake, kanta dake ƙirjinsa ta ɗaga idanunta ta sauke a fuskarsa murya na rawa tace “Twin” idanunsa a rufe yana fisgar Numfashinsa dake ƙoƙarin kwacewa yace “Saaaa” ya faɗa yana buɗe ido tare da kallon ta ganin yadda take kallonsa yasa yace “Nine ko?” Fuska ta kwaɓe tare da ɗaga masa kai, yace “Ok ki daina saka wannan kayan” kayan jikinta ta kalla sai ta kallesa, ɓata fuska yyi yace “ɗaga ni” tashi tayi shi kuma ya miƙe tare da nufar wajan deep frizeer bottle of water ya ɗauka, tare da ɓalle wa, a hankali ya manna bakinsa a gorar ruwan yyi bisimillah ya fara karatu, ya jima na karatun kafin ya gama ya rufe ruwan ya jijjiga, juyawa yyi ya ganta tayi rufda ciki, yatsarta a baki tana tsotsa a hankali..ya jima yana kallonta kafin ya ƙarasa wajanta ganin zata faɗo, ajjiye ruwan yyi, tare da sunkuyawa ya ɗauke ta gaba ɗaya ya mayar da ita tsakiyar gadon, zama yyi ya mata addu’a ya shafa mata, kana ya ja mata duvet ya rufe mata jiki baki ɗaya, remote ya ɗauka ya ƙara mata gudun a.cn daga nan ya fita daga part ɗin. Har zai je wajan Naila sai kuma ya shige nasu part ɗin ya sauya kaya zuwa na bacci ya kwanta yana sauke ajjiyar zuciya.