Al-Ajab

Ƴan Sanda sun kama wani matashi da ya kashe babansa yayin gwajin maganin bindiga

Rundunar ƴan sanda a jihar Adamawa ta tabbatar da kama matashin da aka ce ya harbe mahaifin sa a lokacin da ya umarce shi da ya gwada ingancin maganin bindiga a kansa.

Rahotanni sun ce Yusif Adamu ya umarci agolan sa, Suugbomsumen Adamu da ya harbe shi domin gwajin ingancin wasu sabbin haɗe-haɗen sauyoyi da ya samu da nufin kare shi daga harbin bindiga.

 

An jiyo cewa marigayin ya yi kuri ne da cewa sabbin sauyoyin da ya sha suna da karfi kuma za su kare shi daga harbin bindiga; don haka ya umarci wannan agola nasa ya harbe shi, da nufin bindigar ba za ta kama shi ba.

 

Ai kuwa, rahotanni sun bayyana cewa da agolan ya ɗirka wa malam Adamu bindiga, maimakon a ga ya murje, ya girgije, sai gani a kai sharaf ya faɗi a mace.

 

Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadin da ta gabata a kauyen Sankipo da ke karamar hukumar Jada.

 

A cewar ‘yan sandan, har yanzu wanda ya harbe shi yana hannun su.

 

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Suleiman Nguroje ya ce, “An kama wanda ya harbe shi a gidan kaso.

 

“‘Yan sanda za su binciki lamarin sosai tare da tabbatar da cewa an yi adalci, ba tare da la’akari da alakar mamacin da wanda ake zargin ya yi harbin ba.”

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button