Al-Ajab

Ɗalibi ya kashe kansa bayan budurwarsa ta juya masa baya

Wani ɗailibin ajin ƙarshe a kwalejin fasaha ta tarayya ta Oko da ke jihar Anambra ya kashe kansa saboda budurwarsa ta juya masa baya.

Wata majiya ta bayyana wa Jaridar Daily Trust cewa ɗalibin ya ɗauki matakin ne bayan da budurwar da ya ke matuƙar so ta ce masa ya je ya nemi wata budurwar.

Rahotonni sun ce ɗalibin, wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba, na koyon sanin makamar aiki gabanin kammala karatun na sa.

Majiyar ta ce marigayin ɗalibi ne mai ƙwazo da hazaƙa.

 

Allah ya kiyaye my daga aikata aikin dana sani Amin.

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button