NOVELS

GARKUWA PART 3

Cikin yanayin tashin hankali yaci gaba da cewa.
“Me na tsare mata nida matata da ɗan cikin ta me suka tsare miki me jaririn da baima fito duniyan ba yatsare miki? da har kike ikirarin kasheshi”.
Wani irin numfashi mai zafi yafesar kana yamai da kansa kijin kujera yakwantar tare da lumshe idanunsa, kana ya kuma buɗewa a hankali.
Kamar an sikareshi haka ya miƙe da sauri ya fara tarkata ƴan ƙananan kayyakin ai kinsa da suke baje bisa table ɗin yana gamawa. Ya fito tare da jan ƙofar Office ɗin ya rufe.

A can sashin Gimbiya Aminatu kuwa.
Bayan Hajiya mama suka bi da kallo cike da mamaki ganin yan da tafita a firgice,
Gimbiya Saudatu kuwa ido takurawa cikin Shatu da wani irin tsananin mamaki kai tagirgiza kana itama ta jujjuya kai tanufi kofar fita.

Shatu kuwa ko a jikinta saima gyara zamanta tayi suka shigaisawa da Gimbiya Aminatu kana tayi mata ya jiki.
Ummi ma zaman tayi tagai sheta takuma yimata yajikin, daga nan kuma hira suka ɗan farayi.
Wanda gaba ɗayansu ko wacce da abinda ke ranta.
Gimbiya Aminatu da Ummi su shiru kawai sukayi suka ƙi yin wata mgna akan fita da yanayin da Hajia Mama tayi wai dan kada su nuna firgici su yasa hankalin Shatu tashi.

Sun ɗan jima anan sashin nata suna ɗan hira.
Cikin kula Ummi ta kalli Shatu daketa sauke hamma da lumshe ido alamun baccin ya fara cika mata ido.

Dan yanzu baccin rana yazame mata wajibi idan bata yishiba bata jin daɗi jikinta, jin baccin yayi mata nauyi sosai a ido ne yasa tace.
“Ummi mu tafi zanyi bacci”.
Da sauri Ummi tace.
“Toh muje kam gashi kinata hamma”.
nan sukayiwa Gimbiya Aminatu sallama suka koma part ɗin su.

Suna shiga kai tsaye bedroom ɗinta ta wuce.
Tana shiga ta faɗa saman bed ai ko ba jimawa bacci yayi awon gaba da ita.
Itama Ummi nata ɗakin ta wuce.

Yah Sheykh kuwa a hankali ya dai-dai-ta parking kana yafito anitse yake ɗaga kafarsa laɓɓansa na mosawa a lamun tasbihi.

Shiru falon nasu babu kowa ba motsin komai Side ɗin nasu, alamun duk suna bacci.
Cikin sanyi ya juya ya nufi falon Shatu.
Nan ɗinma shiru ba kowa, a hankali ya kutsa kai ya nufi Bedroom ɗin ta.

A hankali ya zauna a bakin gado kusa da ita,
Kwance take rigingine, bacci takeyi mai daɗi sai numfashi take sauƙewa a hankali,
A hankali ya ƙara juyowa ya fuskanceta da kyau,
hannunshi yasa ya ɗan jawo rigarta ya ɗan yi sama dashi.
Ido ya lumshe jin wani sassayan numfashi data fesar.
Alamun baccin nayi mata daɗi.
Ɗaurin zaninta dake bisa ɗan cikin nata ya ɗan murza yayi ƙasa dashi.
Tafin hannunshi na dama ya kife bisa fatar cikin nata.
A tare suka sauƙe numfashi.
A hankali ya ɗan sunkuyo cikin rauni da tarin son abinda ke cikin mata.
Murya can ƙasa yace.
“Ana Uhubbuk ya habibi. Ina sonka ina sonka ina tsoron abinda zai cutar min da kai da Amminka.”.
Shiru Shatu tayi da yanzu ta farka sai dai bata bude idanunta ba.
Cikin sanyi shi kuma ya sunkuyo ya manna bakinshi kan fatar cikin nata yayi kissing nashi, kana a hankali ya fara karanto addu’o’in yana tofawa kan fatar cikin yana murzawa da tafin hannunshi.
Wanda haka yasa wani bacci mai cike da salama ya kwasheta.
Shi kuwa cikin sanyi yake cewa.
“Yah Allah Kaine mai rayawa mai kashewa. Kaine mai badawa mai hanawa. Kaine mai jarabtan bawa da cuta kuma kaine mai bada waraka. Yah Allah dan tsarkin al’ƙur’ani da girman kujerar al’arshi da soyayyarka da Manzon Allah Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama ya Allah ka raya min wannan cikin ka inƙanta minshi ka tsare minshi ka bashi lfy ka fito min dashi duniya lfy ka al’barkaci rayuwar sa ka tsare minshi da tsarewarka shi da mahaifiyarsa”.
Ido ya lumshe kana ya sake mannawa cikin kiss sannan ya gyara mata konciyarta sannan ya fita ya nufi side ɗin sa.

Hajia Mama ce zaune gaban.
Wani mummunan mutun mai mummunan kamanni da shigar sutura, cikin murya mara daɗin amo yace.
“Na gaya miki ki kiyayi cikin wannan yarinyar raba kanki da son cutar da cikin nan domin, komai zai lalace miki muddin kika taɓa cikin nan, tsohon asirin dake binne tsawon shekaru da dama zai tonu, duniya zata gano ainihin kamanninki”.
Cikin masifa tace.
“Kai boka GILMAU ba cewa nayi ka karya min ƙwarin guiwata ba, zuwa nayi gareka dan mu nemi mafita.
Kaida bakinka kace min muddin wannan shegiyar yarinyar ta haihu cikin masarautar Joɗa komai zai lalace min to kuma ta yaya zaka cemin in bar cikin jikinta ta haifeshi. Wlh bazata yiwu ba, dole in zibdashi yabi kororo ko kuma nasa Jahan ya burmamim cikin shegiyar bafullatanar dajin nan da wuƙa ya zazzago da cikin, ko kuma na hayo ƴan daba su zo su kashe min kowa na zuriyar Aisha”.
Wata muguwar dariya boka GILMAU ya kece da ita dariyar da tasa tsaunuka da kwazazzaɓan da wurin da kogon da suke ciki ya amsa da azaban ƙarfi wanda saida Hajia Mama ta firgita.
Ido ta fara zazzarowa ganin wani irin masifeffen hayaƙi mai azabar duhu ya turniƙesu tako ina.
Cikin dakiya da kafurar zuciya tace.
“Yauwa kira muggan al’janunka ka gaya musu buƙatarsa suje su zuƙe min jinin waccar ja’irar yarinyar ya bare, su gaya min duk abinda sukeso zan sama musu”.
Da sauri ta gyara zamanta jin muryar bokar ta sauya cikin ƙarfi yace.
“Kada ki damu Hajia Halima, zaki samu cikar burinki.
Amman sai kin ajiye mana kuɗi kimanin Naira Miliyan ɗaya. Sannan zamuyi miki wannan aikin”.
Da sauri ta jawo jakar kuɗinta ta zuge rafofin kuɗin dake ciki ta juye a gabanshi wanda sunfi one million, da sauri tace.
“Gasu nan ni dai a hallaka min cikin da ita mai cikin.
Sannan a sabauta min Jafar ta yadda bakinsa zai bar karatun nan dan ta nan kaɗai ne zan samu nasarar binne tsohon sirri”.
Dariya yayi kana hayaƙin ya ɓace.
Yana mai cewa.
“Wannan fa faɗa ne tsakanin ƙarya da gsky tsakanin duhu da haske”.
Da sauri tace.
“Su waye ƙaryan da duhu su waye haske?”.
Yana mai gaba tafiya yace.
“Wanda ke riƙe da Allah da Manzonsa sune gsky kuna haske”.
Shiru tai ta zubawa bikin ido.
Shi kuwa Boka cikin alamun canzawar murya yace.
“Ni dai babu ruwana kan aikinki amman tunda baƙin mayen al’janin ya amshi aikinki ku kuka sani ina dai da tabbacin duk wanda ya riƙe ibada ko kunyi nasara a kanshi bazaiyi tasiri ba shekara nawa muna yaƙi kansu har yau mun kasa cikin galabarsu sabida su Allah suka riƙe”.
Da sauri tace.
“Ni na gamsu”.
Daga nan ta miƙa ta fito, ta fara tattaki cikin dajin da ciyawi da ƙayoyi.
Tafiya mai tsawo tayi kana ta fito bakin titin birji inda tabar motarta sai haki takeyi da numfarfashi dan azabar tafiyar da ta sha dan yin zalumci da muguwar zuciya da taɓewa a gajiye ta shiga cikin motar tata taja ta tafi.

A ranar misalin ƙarfe goma na dare.
Hajia Mama tsaye a can bayan side ɗin ta cikin bishiyoyin dake wurin da duhu.
Cikin tarin bayyana ainihin tsana ziryan ta kalli Sheykh dake tsaye gabanta, cikin irin shigar Jalal.
Riga da wondo ne 3 qtr rigar kuma mara hannu.
Kana yasa fuskarshi ta roba wacce mutanen duniya suka sanshi da ita da sunan Jahan.
kallo ɗaya zakayiwa askin kanshi zaka bashi sunan taƙadiri mugu dan yadda akayi fuskar ba annuri.
Cikin tashin hankali tace.
“Jahan na gama samun mafita, baƙin al’janin boka GILMAU wanda mayene ya amshi aikinna zai zuƙe jinin cikin dama ita kanta fitsarerriyar ƙauyen”.
Wani irin sassanyan ajiyan zuciya ya sauƙe a cikin ransa tare da yin mgnar zuci.
“Ɓatacciya mai ɓataccen tunani nafi tsoron kiyi tunanin sawa Shatu guba akan bokayenki.
Wanda na sani in sha, Allah.
Bazasuyi nasara a kaina da ahlinna ba in sha Allah bazaki samu nasaraba dan Allah yana tare damu”.
A zahiri kuwa cikin sauya murya ya juyeta eh zuwa muryar ƴan daba yace.
“Uhum rana dubu ta ɓarawo ko rana ɗaya kuma ta mai kaya”.
Da sauri tace.
“To waye ɓarawon waye mai kayan?”.
Da sauri ya canza akalar zancen da cewa.
“Yoh kece mai kayan mana tunda kece uwar gidan Habibullah, ita waccar balarabiya tazo ta aure miki miji tai ta zazzago ƴaƴa maza harda tagwaye.
Kinga yanzu zamu samu nasarar kauda ahlinta, inma bokayen sunƙi yi mana aiki ko ni zan gama da wannan cikin Hajiyar mugunta”.
Dariyar jin daɗi tayi dan in yace mata Hajiyar mugunta tasan.
Duk duniya shi ɗaya ne yasan asalin ainihin muguntarta sai bokanta.
Takanji ta gamsu da kanta da ta iya sirranta muguntarta a ranta har tasa yardarta a zuƙatansu”.
Ganin yadda tai murmushi ne ya sashi yin ƙasa da kai tare da yin murmushin kana yace.
“Toh ni zan wuce gida babyna tana jirana”.
Cikin gamsuwa da tasan yakan nuna mata yanada mata.
To tace kana yabi can bayan bishi yoyin ita kuma ta dawo cikin Part ɗin nata.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button