Labarai

Fasinjoji 9 sun rasu yayin da motarsu ta fada Dam a Kano

Wasu fasinjoji 9 sun rasu yayin da motarsu ta fada Dam a Kano

Wasu mutane 9 da suka shiga wata motar haya kirar Golf, sun rasa rayukansu a ranar Asabar a karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano bayan da motarsu ta fada cikin dam.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta Kano, Saminu Abdullahi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a jihar Kano.

Saminu, ya ce, “A ranar Asabar, 19 ga watan Nuwamba, 2022, hukumar kashe gobara ta jihar ta samu wani kiran gaggawa daga wani mai suna Ali Faci da misalin karfe 6:45 na yamma inda ya sanar wa hukumar cewa motar ta afka cikin Dam din Fada.

Wadanda hadarin ya rutsa da su sun hada da yara jarirai mata biyu ‘yan kimanin watanni shida da mata hudu ‘yan shekaru 30, 28, 27 da 25, da kuma maza shida ‘yan kimanin shekaru 48, 45, 42, 40, 35 da 28.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button