Noor Albi

NOOR ALBI 3

Har aka gama sallah Bata Gama shanyarba Saida aka sallame tagama ta tattara gurin ta share ta tsaftacesa ta watsa ruwa tayo tata alwalar ta nufi ciki ta wuce dakinta direct tasaka wata baqar jallabiya ta tada sallah.

Bayan tagama sallar dakin Anty Sa’adah taje ta dauka Qur’an ta nufi palon abbansu ta zauna gefensa tafara karatun al qur’an din cikin zuciyarta har akai sallar ishai anan palon tayi sallah bayan tagama taga alamar shima sallar yakeyi Dan Haka Kai tsaye ta nufa abincinsa ta zubo ta tareda zuba Masa ruwa a wani kofin ta daukosu tareda magani tadawo gabansa.

Tana Gama basa komai ta gyara Masa koina abdullahi yazo ya daukesa daga kan kujera ya maidasa Kan gadonsa Tai Masa addua ta fice shima abdullahin tare suka fito taja Masa kofa.
gurin Anty Sa’adah ta nufa Dan karatun dare datake koya Mata na littafan addini.

Acan takai kusan karfe goma na dare suna karatun kafin ta harhadawa anty Sa’adah dakin ta gyara Mata shimfidar gadonta dasuka zauna Baki taje ta dauko Mata ruwan dare datake yawan tashi Sha ta aje Mata kafin ta fito taje ta rufe gidan da koina ta nufi nata dakin tayi Shirin kwanciya tayi addua ta kwanta.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button