‘Surukata Ce Ta Roki In Yi Wa ’Yarta Ciki Kafin Na Aure Ta’
Wani matashi da ake zargi da yi wa budurwarsa ciki ya fada wa wata kotun Ibadan cewa surukarsa ce ta roki ya yi wa ’yarta ciki kafin ya aure ta.
Matashin ya fadi haka ne a lokacin da yake kare kansa a kotun kan zargin da buduwarsa ta yi masa na rashin kula da ita yadda ya kamata, inda ta nemi kotu ta raba tsakaninsu.
Ya ce abin da iyayen matar suka bukata ya aikata, amma daga bisani suka nemi juya masa baya.
“Ban san abin da ya faru ba. Iyayenta sun fada mini cewa ba za su taba yarda ’yarsu ta zauna da ni ba.
“Kuma ta hana ni ganin dan da muka haifa,” inji shi.
Tun farko, budurwar ta shaida wa kotun cewa saurayin nata ba ya kula da ita da danta mai shekara uku.
“….Tun bayan da na haihu, sau biyu saurayin ya ba ni N1,500 sai kuma kayan sawa na yaro, daga nan ya ci gaba da kauce wa nauyin da ya rataya a kansa,” inji ta.
Da take yanke hukunci, Alkalin kotun, Misis S.M. Akintayo ta ce babu wani aure da za a warware tsakanin masoyan tun da asali ba su yi aure ba saboda babu inda aka biya sadaki.
Daga bisani, kotun ta ba da umarnin dan ya ci gaba da zama a hannun mahaifiyarsa, kana Sodiq ya rika ba da kudin ciyarwa N10,000 duk wata.
(NAN)